< Malaki 3 >

1 “Duba, zan aika manzona, wanda zai shirya hanya a gabana. Sa’an nan a farat ɗaya Ubangiji wanda kuke nema zai zo haikalinsa. Manzon alkawari, wanda kuke sa zuciya kuwa zai zo,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
הנני שלח מלאכי ופנה דרך לפני ופתאם יבוא אל היכלו האדון אשר אתם מבקשים ומלאך הברית אשר אתם חפצים הנה בא אמר יהוה צבאות׃
2 Amma wa zai jure wa ranar zuwansa? Wa zai iya tsaya sa’ad da ya bayyana? Gama zai zama kamar wuta mai tace ƙarfe, ko sabulu mai wanki.
ומי מכלכל את יום בואו ומי העמד בהראותו כי הוא כאש מצרף וכברית מכבסים׃
3 Zai zama kamar mai tace azurfa da mai tsarkaketa; zai tsabtacce Lawiyawa, yă kuma tace su kamar zinariya da azurfa. Sa’an nan Ubangiji zai sami mutanen da za su kawo hadayu a cikin adalci.
וישב מצרף ומטהר כסף וטהר את בני לוי וזקק אתם כזהב וככסף והיו ליהוה מגישי מנחה בצדקה׃
4 Hadayun Yahuda da na Urushalima za su zama yardajje ga Ubangiji, za su zama kamar a kwanakin da suka wuce, kamar a shekarun baya.
וערבה ליהוה מנחת יהודה וירושלם כימי עולם וכשנים קדמניות׃
5 “Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
וקרבתי אליכם למשפט והייתי עד ממהר במכשפים ובמנאפים ובנשבעים לשקר ובעשקי שכר שכיר אלמנה ויתום ומטי גר ולא יראוני אמר יהוה צבאות׃
6 “Ni Ubangiji ba na canjawa. Shi ya sa ku zuriyar Yaƙub, ba a hallaka ku ƙaƙaf ba.
כי אני יהוה לא שניתי ואתם בני יעקב לא כליתם׃
7 Tun zamanin kakanninku, kun juye wa ƙa’idodina baya, ba ku kuma kiyaye su ba. Ku komo gare ni, ni kuma zan koma gare ku,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya za mu koma gare ka?’
למימי אבתיכם סרתם מחקי ולא שמרתם שובו אלי ואשובה אליכם אמר יהוה צבאות ואמרתם במה נשוב׃
8 “Mutum zai iya yi wa Allah fashi ne? Duk da haka kun yi mini fashi. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka yi maka fashi?’ “A wajen zakka da hadayu.
היקבע אדם אלהים כי אתם קבעים אתי ואמרתם במה קבענוך המעשר והתרומה׃
9 Kuna ƙarƙashin la’ana, dukan al’ummarku, domin kuna yin mini fashi.
במארה אתם נארים ואתי אתם קבעים הגוי כלו׃
10 Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.
הביאו את כל המעשר אל בית האוצר ויהי טרף בביתי ובחנוני נא בזאת אמר יהוה צבאות אם לא אפתח לכם את ארבות השמים והריקתי לכם ברכה עד בלי די׃
11 Zan hana ƙwari su cinye hatsinku. Kuringar inabi a gonakinku kuma ba za su zubar da’ya’yansu kafin su nuna ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
וגערתי לכם באכל ולא ישחת לכם את פרי האדמה ולא תשכל לכם הגפן בשדה אמר יהוה צבאות׃
12 “Sa’an nan dukan al’ummai za su ce da ku masu albarka, gama ƙasarku za tă yi daɗin zama,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
ואשרו אתכם כל הגוים כי תהיו אתם ארץ חפץ אמר יהוה צבאות׃
13 “Kun faɗi mugayen abubuwa a kaina,” in ji Ubangiji. “Duk da haka kuka ce, ‘Me muka faɗa a kanka?’
חזקו עלי דבריכם אמר יהוה ואמרתם מה נדברנו עליך׃
14 “Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Allah. Wanda amfani muka samu ta wurin kiyaye umarnansa muna yawo kamar masu makoki a gaban Ubangiji Maɗaukaki?
אמרתם שוא עבד אלהים ומה בצע כי שמרנו משמרתו וכי הלכנו קדרנית מפני יהוה צבאות׃
15 A ganinmu, masu girman kai suna jin daɗi. Masu aikata mugunta kuwa ba arziki kaɗai suka yi ba, amma sukan gwada Allah da mugayen ayyukansu, su kuwa zauna lafiya.’”
ועתה אנחנו מאשרים זדים גם נבנו עשי רשעה גם בחנו אלהים וימלטו׃
16 Sa’an nan waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da juna, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya kuma ji. A gabansa aka rubuta a littafin tarihi waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuma girmama sunansa.
אז נדברו יראי יהוה איש את רעהו ויקשב יהוה וישמע ויכתב ספר זכרון לפניו ליראי יהוה ולחשבי שמו׃
17 “A ranar da na shirya ajiyayyen mallakata, za su zama nawa,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan ji kansu kamar yadda mahaifi cikin tausayi yakan ji kan ɗansa wanda yake masa hidima.
והיו לי אמר יהוה צבאות ליום אשר אני עשה סגלה וחמלתי עליהם כאשר יחמל איש על בנו העבד אתו׃
18 Za ku kuma ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, tsakanin waɗanda suke wa Allah hidima da kuma waɗanda ba sa yi.
ושבתם וראיתם בין צדיק לרשע בין עבד אלהים לאשר לא עבדו׃

< Malaki 3 >