< Luka 9 >

1 Bayan da Yesu ya tara Sha Biyun wuri ɗaya, sai ya ba su iko da izini na fitar da dukan aljanu, da na warkar da cututtuka.
Ya kira almajiransa goma sha biyu, ya ba su iko su fitar da kowanne irin aljani, su kuma warkar da cututtuka daga mutane.
2 Ya kuma aike su, su yi wa’azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.
Ya aike su, su yi wa'azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.
3 Ya ce musu, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, wato, ba sanda, ba jaka, ba burodi, ba kuɗi, ba riga na biyu.
Ya ce masu, “Kada ku dauki komi tare da ku domin wannan tafiya. Kada ku dauki sanda, ko jakar matafiyi, ko gurasa, ko kudi - Kada ma ku dauki taguwa biyu.
4 Duk gidan da kuka sauka, ku zauna nan sai kun bar garin.
Dukan gidan da ku ka shiga, ku zauna a gidan har zuwa lokacin da za ku tafi daga wannan yankin.
5 In mutane ba su karɓe ku ba, sa’ad da kun bar garinsu, ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.”
Dukan wadanda ba su marabce ku ba, sa'adda ku ke barin wannan gari, ku karkabe kurar kafufunku a matsayin shaida a kansu.”
6 Sai suka tashi suka shiga ƙauye zuwa ƙauye suna wa’azin bishara, suna warkar da marasa lafiya a ko’ina.
Daga nan sai almajiran suka tafi zuwa cikin kauyuka, suka yi ta shelar bishara, su na warkar da mutane a ko'ina.
7 Yanzu fa, Hiridus mai sarauta ya ji labarin dukan abubuwan da suke faruwa. Sai ya rikice, don waɗansu mutane suna cewa, Yohanna Mai Baftisma ne ya tashi daga matattu,
Ana nan Hirudus, mai mulki, ya ji labarin dukan abubuwan da su ke faruwa. Ya yi mamaki saboda wadansu mutane suna cewa Yahaya mai yin Baftisma ne ya sake dawowa da ransa.
8 waɗansu kuma suna cewa, annabi Iliya ne ya sāke bayyana. Waɗansu kuma har wa yau, suna cewa, ɗaya daga cikin annabawa na dā ne, ya tashi.
Wadansu kuma suna cewa, annabi Iliya ne ya sake bayyana, wadansu kuma suna cewa daya daga cikin annabawa na da can ne ya sake bayyana da rai.
9 Amma Hiridus ya ce, “Yohanna dai na yanke kansa, amma wanne mutum ne nake jin labarin abubuwan nan a kansa?” Sai ya yi ƙoƙari ya ga Yesu.
Hirudus ya ce, “Ba zai yiwu Yahaya ne ba, domin na datse masa kai. To, wanene wannan da ni ke jin wadannan abubuwa a kansa?” Daga nan sai ya cigaba da neman hanyar da zai ga Yesu.
10 Da manzannin suka dawo, sai suka faɗa wa Yesu abin da suka yi. Sai ya ɗauke su, suka keɓe kansu su kaɗai, zuwa wani gari da ake kira Betsaida.
Sa'adda manzannin suka dawo daga tafiyarsu, suka gaya wa Yesu dukan abubuwan da suka yi. Daga nan sai ya dauke su domin su tafi tare da shi zuwa garin Baitsaida.
11 Amma taron mutane suka ji labari, sai suka bi shi. Ya marabce su, kuma ya yi musu magana a kan mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkarwa.
Amma sa'adda taron suka ji inda Yesu ya tafi, sai suka bi shi can. Ya marabce su ya yi masu jawabi a kan mulkin Allah, kuma ya warkar da wadanda su ke bukatar warkarwa.
12 Da rana ta kusa fāɗuwa, sai Sha Biyun suka zo wurinsa, suka ce, “Ka sallami taron domin su shiga ƙauyuka na kewaye, su nemi abin da za su ci, da wurin kwana, don inda muke, ba kowa.”
Da yake yamma ta fara yi, sai almajiransa goma sha biyu suka zo suka ce da shi, “Idan ka yarda ka sallami wannan babban taron mutane dominsu shiga cikin kauyuka, da ke kewaye da gonaki, dominsu sami abinci da wuraren da za su kwana, da yake mu na nan a wurin da ba kowa.”
13 Yesu ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.” Sai suka ce masa, “Muna da burodi biyar da kifi biyu kaɗai. Sai dai, in mun je mu sayi abinci domin dukan wannan taron.”
Amma sai ya ce da su, “Ku ba su abin da za su ci.” Suka amsa masa, “Dukan abin da muke da shi shine, 'Yan dunkulen gurasa biyar da 'yan kifaye guda biyu, ba za mu iya zuwa mu sawo abincin da zai ishi mutanen nan su duka ba.”
14 Maza kaɗai sun kai kusan dubu biyar. Amma ya ce wa almajiransa, “Ku sa su su zauna a ƙungiya hamsin-hamsin.”
Mutanen da suke wurin sun kai kimanin mazaje dubu biyar. Sai Yesu ya ce da almajiran, “Ku ce da mutanen su zauna kungiya-kungiya, mutane hamsin a kowacce kungiya.”
15 Haka almajiran suka yi, kowa kuwa ya zauna.
Sai almajiran suka yi haka, dukan mutanen suka zauna.
16 Sai Yesu ya ɗauki burodin biyar da kifin biyun, ya ɗaga kansa sama, ya yi godiya, ya kuma kakkarya su. Ya ba wa almajiransa, domin su rarraba wa mutanen.
Ya dauki dunkulen gurasan guda biyar, da kifin guda biyu, yana dubawa zuwa sama ya albakarce su, sa'annan ya gutsuttsura, ya ba almajiran domin su rarraba wa mutane.
17 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi. Almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu.
Dukansu suka ci kowa ya koshi. Daga nan almajiran suka tattara sauran abin da ya rage, har kwanduna goma sha biyu suka cika!
18 Wata rana sa’ad da Yesu yana addu’a a ɓoye, almajiransa kuma suna tare da shi, sai ya tambaye, su ya ce, “Wa, taron mutane ke ce da ni?”
Wata rana Yesu yana yin addu'a shi kadai, sai almajiransa suka zo sai ya tambaye su, “Wa mutane suke cewa da ni?”
19 Suka amsa, suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yohanna Mai Baftisma, waɗansu kuma annabi Iliya, har wa yau waɗansu suna cewa, kai ɗaya daga cikin annabawan da ne, da ya tashi da rai.”
Suka amsa, “Wadansu suna cewa, Yahaya mai yin Baftisma, wadansu suna cewa kai annabi Iliya ne, har yanzu wadansu suna cewa kai wani cikin annabawa na da can ne ya dawo da rai.”
20 “Amma ku fa, wa, kuke ce da ni?” Bitrus ya amsa ya ce, “Kiristi na Allah.”
Ya tambaye su, “Ku fa? Wa kuke cewa da ni?” Bitrus ya amsa, “Kai Almasihu ne wanda ya zo daga wurin Allah.”
21 Yesu ya gargaɗe su da ƙarfi, kada su gaya wa kowa wannan magana.
Sai Yesu ya gargade su da karfi, kada su gayawa kowa haka tukuna.
22 Ya sāke cewa, “Dole ne Ɗan mutum ya sha wahaloli da yawa, dattawa, da manyan firistoci, da malaman dokoki kuma su ƙi shi, kuma dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tā da shi da rai.”
Sa'annan ya ce, “Dan Mutum dole ya sha wahalar abubuwa da yawa; dattawa za su ki shi da manyan fristoci da marubuta, sa'annan za a kashe shi. Bayan kwana uku, za a tashe shi da rai.”
23 Sai ya ce wa dukansu, “In wani zai bi ni, dole yă mūsanta kansa, ya ɗauki gicciyensa kowace rana, ya bi ni.
Sai ya ce da su duka, “Dukan wanda ya ke so ya biyo ni, dole ne ya yi musun kansa, ya dauki gicciyen sa kulluyomin, ya biyo ni.
24 Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni zai same shi.
Dukan wanda yake so ya ceci ransa, za ya rasa shi, amma dukan wanda ya ba da ransa domina, za ya cece shi.
25 Ina amfani, in mutum ya ribato duniya duka, amma ya rasa ransa, ko kuma ya yi hasarar ransa.
Wacce riba mutum zai samu idan ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa?
26 Duk wanda yake jin kunyana da na kalmomina, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa sa’ad da zai zo a cikin ɗaukakarsa, da ɗaukakar Uban, da kuma ta tsarkaka mala’ikun.
Dukan wanda yake jin kunya ta da magana ta, Dan Mutum ma zai ji kunyarsa, sa'adda ya dawo cikin darajarsa da darajar Uba da ta mala'iku masu tsarki.
27 “Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su ga mutuwa ba, sai sun ga mulkin Allah.”
Amma ina gaya maku wannan tabbas, wadansu cikinku da ke nan tsaye, ba za su mutu ba sai sun ga mulkin Allah.”
28 Bayan kamar kwana takwas da yin wannan magana, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yohanna, da kuma Yaƙub, suka hau kan dutse tare don yin addu’a.
Kwana takwas bayan Yesu ya fadi wadannan kalmomi, sai ya dauki Bitrus da Yahaya da Yakubu, ya hau kan dutse domin ya yi addu'a a can.
29 Yana cikin addu’a, sai kamannin fuskarsa ta sāke, tufafinsa kuma suka zama da haske kamar hasken walƙiya.
Sa'anda ya ke yin addu'a sai yanayin fuskar sa ya canza sosai, tufafinsa kuma suka yi sheki da haske kamar walkiya.
30 Sai ga mutum biyu, Musa da Iliya, suka bayyana cikin kyakkyawar daraja, suna magana da Yesu.
Nan da nan sai ga mutane biyu suna magana da shi, wato Musa da Iliya.
31 Suka yi zance a kan tashinsa, wanda shi ya kusan ya kawo ga cikarsa a Urushalima.
Suka bayyana da daraja kewaye da su, suka yi magana da Yesu a kan tafiyarsa wadda za ta zo ba da dadewa ba a cikin Urushalima.
32 Barci kuwa ya kama Bitrus da abokan tafiyarsa sosai. Da idanunsu suka warware, sai suka ga ɗaukakarsa da kuma mutum biyun tsaye tare da shi.
Bitrus da almajiran da suke tare da shi barci mai nauyi ya dauke su. Sa'adda suka farka sai su suka ga daukakar Yesu; kuma suka ga mutanen su biyu da ke tsaye tare da shi.
33 Da mutanen na barin Yesu, sai Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, wato, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.” (Bai ma san abin da yake faɗi ba.)
Sa'adda Musa da Iliya suke shirin su bar wurin Yesu, sai Bitrus ya ce, “Ya shugaba, ya yi kyau da muke a nan. Zai yi kyau mu yi runfuna uku, daya dominka, daya domin Musa, daya kuma domin Iliya.” Amma hakika bai san abin da ya ke fadi ba.
34 Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije ya bayyana ya rufe su, sai suka ji tsoro, yayinda suke shiga cikin girgijen.
Sa'adda yake fadin haka sai wani girgije ya zo ya rufe su. Sai suka ji tsoro sa'adda girgijen ya kewaye su.
35 Wata murya ta fito daga cikin girgijen, tana cewa, “Wannan Ɗana ne, zaɓaɓɓena, ku saurare shi.”
Sai ga wata murya daga cikin girgijen tana cewa, “Wannan Dana ne wanda na zaba, ku ji shi.”
36 Da muryar ta gama magana, sai suka tarar Yesu shi kaɗai ne. Almajiran kuwa suka riƙe wannan al’amari a zukatansu. A lokacin nan, ba su gaya wa kowa abin da suka gani ba.
Sa'adda muryar ta gama magana, Yesu yana nan shi kadai. Suka yi shiru ba su iya cewa kome ba a kan abin da suka gani a kwanakin nan.
37 Kashegari, sa’ad da Yesu tare da almajiran nan uku suka sauka daga kan dutsen, sai taro mai yawa ya haɗu da shi.
Washe gari, da suka sauko daga kan dutsen, sai taron mutane da yawa suka zo wurinsa.
38 Sai wani mutum daga cikin taron ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Malam, ina roƙonka, ka dubi ɗan nan nawa, gama shi ne kaɗai nake da shi.
Nan da nan, wani mutum daga cikin taron mutanen ya yi magana da karfi, “Mallam, kayi wani abu dominka taimaki da na, shi kadai ne gare ni.
39 Wani ruhu yakan kama shi, sai ya yi ihu farar ɗaya. Yakan sa shi farfaɗiya, har bakinsa ya yi kumfa. Da ƙyar yake barinsa, yana kuwa kan hallakar da shi.
Mugun ruhu ya kan hau kansa, ya sa shi ya yi ta magowa. Ya kan girjiza shi da karfi ya sa bakinsa ya yi ta kumfa. Da kyar ya ke rabuwa da shi, kuma ya kan ji masa ciwo ba kadan ba bayan da ya bar shi.
40 Na roƙi almajiranka su fitar da shi, amma ba su iya ba.”
Na roki almajiran ka su umurci mugun ruhun ya fita daga cikinsa, amma ba su iya ba!”
41 Yesu ya amsa ya ce, “Ya karkataccen zamani marar bangaskiya, har yaushe ne zan kasance tare da ku, ina kuma haƙuri da ku? Kawo yaronka nan.”
Yesu, ya amsa, ya ce, “Ku karkatattun tsara marasa bangaskiya, har yaushe zan zauna da ku ina jimrewa da ku? “Kawo yaronka anan.”
42 Yaron yana kan zuwa ke nan, sai aljanin ya buga shi ƙasa, cikin farfaɗiya. Amma Yesu ya kwaɓe mugun ruhun, ya warkar da yaron, sai ya miƙa shi ga mahaifinsa.
Sa'adda yaron yake zuwa, sai mugun ruhun ya fyada yaron a kasa, ya jijjiga shi sosai. Amma Yesu ya tsauta wa mugun ruhun, ya warkar da yaron. Sa'annan ya mika yaron wurin mahaifinsa.
43 Duk suka yi mamakin girman Allah. Yayinda kowa yana cikin mamakin dukan abubuwan da Yesu ya yi, sai ya ce wa almajiransa,
Dukansu suka yi mamaki da girman ikon Allah. Amma sa'anda suke ta yin mamaki a kan dukan al'ajiban da ya yi, ya ce da almajiransa,
44 “Ku kasa kunne da kyau ga abin da zan faɗa muku. Za a bashe Ɗan Mutum ga hannun mutane.”
“Ku saurara da kyau a kan abin da zan gaya maku, ba da dadewa ba za a bada Dan Mutum ga mutane.”
45 Amma ba su fahimci abin da yake nufi da wannan magana ba. Ba su gane ba, don an ɓoye musu shi. Su kuwa sun ji tsoro su tambaye shi.
Amma almajiran ba su gane abin da yake nufi da haka ba, an hana su fahimta, domin kada su gane abin da ya ke nufi tukuna, kuma suna jin tsoron su tambaye shi.
46 Wata gardama ta tashi a tsakanin almajiran, a kan ko wane ne a cikinsu zai zama mafi girma
Wani lokaci, almajiran suka fara gardama a tsakaninsu game da wanene za ya zama mafi girma a cikinsu.
47 Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa ya tsaya kusa da shi.
Amma Yesu ya san abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya kawo dan karamin yaro ya tsaya a kusa da shi,
48 Sai ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi wannan ƙaramin yaron a cikin sunana, ni ya karɓa, kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. Gama mafi ƙanƙanta duka a cikinku, shi ne kuma mafi girma.”
sai ya ce da su, “Idan wani ya karbi dan karamin yaro kamar wannan saboda ni, dai dai yake da ya karbe ni. Idan kuma wani ya karbe ni, ya karbi wanda ya aiko ni kenan. Wanda yake mafi kankanta a cikinku, shi ne mafi mahimmanci.”
49 Sai Yohanna ya ce, “Ubangiji, mun ga wani mutum yana fitar da aljanu a cikin sunanka, muka yi ƙoƙarin hana shi, don shi ba ɗaya ba ne daga cikinmu.”
Yahaya ya amsa yace, “Ya shugaba, mun ga wani mutum yana ba miyagun ruhohi umarni su fita daga cikin mutane da sunanka. Sai muka ce da shi ya dena yin haka saboda baya tare da mu.”
50 Yesu ya ce, “Kada ku hana shi, gama duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.”
Amma Yesu ya ce, “Kada ku hana shi yin haka, domin dukan wanda ba ya gaba da ku, yana tare da ku.”
51 Da lokaci ya yi kusa da za a ɗauki Yesu zuwa sama, sai ya ɗaura niyyar tafiya Urushalima.
Sa'adda rana ta kusato da zai hawo zuwa sama, ya kudurta sosai zai tafi Urushalima.
52 Sai ya aiki’yan saƙo, su yi gaba. Su kuwa, suka shiga cikin wani ƙauyen Samariyawa, don su shirya masa abubuwa.
Ya aiki wadansu manzanni su shirya wuri dominsa kafin ya zo. Suka shiga wani kauye a cikin kauyen Samariya domin su shirya masa wuri a can.
53 Amma mutanen ƙauyen ba su karɓe shi ba, don yana kan hanyar zuwa Urushalima ne.
Amma mutanen can ba su karbe shi ba tun da ya ke Urushalima zai tafi.
54 Da almajiransa, Yaƙub da Yohanna suka ga haka, sai suka yi tambaya suka ce, “Ubangiji, kana so mu kira wuta ta sauka daga sama ta hallaka su?”
Sa'adda biyu daga cikin almajiransa, wato Yakubu da Yahaya suka ga haka, suka ce, “Ubangiji, kana so mu umarci wuta ta sauko daga sama, ta hallaka su?”
55 Amma Yesu ya juya, ya kwaɓe su.
Amma, ya juya ya tsauta masu.
56 Sai shi da almajiransa suka tafi wani ƙauye.
Sai suka tafi wani kauye dabam.
57 Suna kan tafiya a hanya, sai wani mutum ya ce masa, “Zan bi ka, duk inda za ka.”
Da suna cikin tafiya a kan hanya, sai wani mutum ya ce da shi, “Zan bi ka dukan inda za ka tafi.”
58 Yesu ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”
Yesu ya amsa masa, “Dila suna da ramuka a kasa inda za su shiga, tsuntsaye kuma suna da sheka, amma Dan Mutum ba shi da inda zai kwanta.”
59 Ya kuma ce wa wani mutum, “Ka bi ni.” Amma mutumin ya amsa ya ce, “Ubangiji, bari in je in binne mahaifina tukuna.”
Yesu, ya ce da wani mutumin kuma, “Ka biyo ni.” Amma mutumin ya ce, “Ubangiji, ka bari in koma gida in bizine mahaifina tukuna.”
60 Yesu ya ce masa, “Ka bar matattu su binne matattunsu, amma kai, ka je ka yi shelar mulkin Allah.”
Amma Yesu ya ce masa, “Ka bar matattu su bizine matattunsu; amma kai ka tafi ka yi wa mutane shelar mulkin Allah a ko'ina.”
61 Har wa yau, wani ya ce, “Zan bi ka, Ubangiji, amma ka bar ni in je in yi bankwana da iyalina tukuna.”
Wani kuma ya ce, “Ubangiji zan tafi tare da kai, amma bari in je gida inyi ban kwana da mutanena tukuna.”
62 Yesu ya amsa ya ce, “Babu wani da yakan sa hannunsa a garman shanu, sa’an nan ya waiwaya baya, da ya isa ya shiga hidima a cikin mulkin Allah ba.”
Yesu ya ce da shi, “Dukan wanda ya fara huda a gonarsa idan ya dubi baya, bai isa ya shiga mulkin Allah ba.”

< Luka 9 >