< Luka 8 >

1 Bayan wannan sai Yesu ya zazzaga gari da ƙauye, yana wa’azin bisharar mulkin Allah. Sha Biyun nan kuwa suna tare da shi,
以後,耶穌走遍各城各村講道,宣傳天主國的喜訊,同祂在一起的有那十二們徒,
2 da kuma waɗansu mata waɗanda aka warkar da su daga cututtukansu, da kuma mugayen ruhohi. Cikinsu akwai Maryamu (wadda ake kira Magdalin) wadda aljanu bakwai suka fito daga cikinta.
還有幾個曾附過惡魔或患病而得治好的婦女,有號稱瑪達肋納的瑪利亞,從她身上趕出了七個魔鬼;
3 Da Yowanna matar Kuza, manajan iyalin Hiridus; da Suzana; da waɗansu mata da yawa. Waɗannan mata suna taimaka musu cikin hidima, daga cikin abin da suke da shi na zaman gari.
還有約安納,即黑落德的家宰雇撒的妻子,又有蘇撒納;還有別的許多婦女,她們都用自己的財產資助他們。
4 Yayinda taron mai girma na taruwa, mutane kuma daga garuruwa dabam-dabam suna zuwa wurin Yesu, sai ya ba da wannan misali ya ce,
那時,有大夥群眾聚集了來,並有從各城來到耶穌跟前的,祂就用比喻說:
5 “Wani manomi ya fita domin ya shuka irinsa. Da yana watsa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, aka tattaka su, tsuntsayen sararin sama kuma suka cinye su.
「有一個撒種子的,出去撒種子;他撒的時候,有的落在路在路旁,就被踐踏了,並有天的飛鳥把它吃了。
6 Waɗansu suka fāɗi a kan dutse, da suka tsira sai suka yanƙwane don babu ruwa a wurin.
有的落在路在石頭上,一長起來,就乾枯了,因為沒有濕氣。
7 Waɗansu kuma suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma tare, sai ƙayan suka shaƙe su.
有的落在荊棘中,荊棘同它一起畏起來,把它窒息了。
8 Waɗansu kuma har yanzu, suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka yi girma, suka ba da amfani riɓi ɗari-ɗari, fiye da abin da aka shuka.” Da faɗin haka sai ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”
又有的落在好地裏,長起來,結了百倍的果實。」祂說完這些話,就高呼說:「有耳聽的,就聽吧! 」
9 Almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali.
祂的們徒問祂這比喻有什麼意思。
10 Sai ya ce, “Ku ne aka ba sanin asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane kam, ina magana da misalai, saboda, “‘ko da yake suna kallo, ba za su gani ba, ko da yake suna ji, ba za su gane ba.’
祂說:「天主國的奧秘,是給你們知道;對於其餘的人,就用比喻,使那看的,卻看不見,聽的,卻聽不懂。
11 “Ga ma’anar misalin, irin, shi ne maganar Allah.
這比喻的意思是:種子是天主的話。
12 Waɗanda suka fāɗi a kan hanya su ne mutanen da suka ji, amma Iblis, yakan zo ya ɗauke maganar daga zuciyarsu, don kada su gaskata, su sami ceto.
那些在路旁的,是指那人聽了,隨後就有鬼來到,從他們心中把那話奪去,使他們不致信從而得救。
13 Na kan dutse kuwa, su ne da jin maganar, sukan karɓa da murna, amma ba su da saiwa. Sukan gaskata na ɗan lokaci, amma lokacin gwaji, sai su ja da baya.
那在石頭上的,是指那些人,他們聽的時候,高興的接受那話,但這些人沒有根,暫時相信,一到試探的時候,就退避了。
14 Irin da suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa, su ne mutanen da suka ji, amma a kwana a tashi, tunanin kayan duniya, da neman arziki, da son jin daɗi, sukan hana su ba da’ya’ya.
那落在荊棘中的,是指那些聽了的人,還在中途就被掛慮、錢財及生活的逸樂所蒙蔽,沒有結出成熟的果實。
15 Amma irin da suka fāɗi a ƙasa mai kyau kuwa, su ne mutane masu kyakkyawar zuciya, mai kyau, da suka ji, suka riƙe, suka kuma jimre har suka ba da’ya’ya.”
那在好地裏的,是指那些以善良和誠實的心傾聽的人,他們把這話保存起來,以堅忍結出果實。
16 “Ba mai ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta a cikin tulu, ko kuma ya sa ta a ƙarƙashin gado ba. A maimakon haka, yakan sa ta a kan wurin ajiye fitila, saboda mutane masu shigowa su ga haske.
沒有人點上燈,用器皿遮蓋住,或放在床底下的,而是放在燈台上,為叫進來的人看見光明。
17 Ba abin da yake ɓoye da ba za a fallasa ba. Kuma ba abin da yake rufe, da ba za a sani ba, ko a fitar da shi a fili ba.
因為沒有隱藏的事,不成為顯露的;沒有秘密的事,不被知道而公開出來的。
18 Saboda haka, ku yi tunani da kyau yadda kuke saurara. Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda ba shi da shi kuma, abin da yake tsammani yana da shi ma, za a karɓe daga gare shi.”
所以,你們要留心要怎樣聽;因為凡有的,還要給他,凡沒有的,連他自以為有的,也要從他奪去。」
19 Sai uwar Yesu da’yan’uwansa suka zo, domin su gan shi, amma ba su iya zuwa kusa da shi ba, saboda taron.
耶穌的母親和兄弟到祂這裏來了,因為人多,不能與祂相會。
20 Sai wani ya faɗa masa cewa, “Ga uwarka da’yan’uwanka suna tsaye a waje suna so su gan ka.”
有人告訴祂說:「你的母親和你的兄弟站在在外邊,願意見你。」
21 Ya amsa ya ce, “Mahaifiyata da’yan’uwana, su ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma aikata ta.”
祂卻回答說:「聽了天主的話而實行的,才是我的母親和兄弟。」
22 Wata rana Yesu ya ce wa almajiransa, “Mu haye zuwa wancan gefen tafkin.” Sai suka shiga jirgin ruwa suka fara tafiya.
有一天,耶穌和們徒上了船,對他們說:「我們渡到湖那去。」他們便開了船。
23 Da suna cikin tafiya, sai barci ya kwashe shi. Sai wata babban iska ta taso kan tafkin, har ruwa ya fara shiga cikin jirgin. Suka shiga babban hatsari.
正在航行時,他睡著了。忽然有狂風降到湖上,進入船中的水,使他們處於危險中。
24 Almajiran suka je suka tashe shi daga barci, suka ce, “Ubangiji, Ubangiji, za mu nutse!” Ya tashi ya kwaɓe iskar da kuma haukar ruwan. Sai ruwan da iskar suka natsu. Kome ya yi tsit.
們徒們前來叫醒耶穌,說:「老師! 老師! 我們要喪亡了! 」祂醒起來,叱責了狂風和波浪,風浪就止息平靜了。
25 Sai ya tambayi almajiransa, “Ina bangaskiyarku?” A cikin tsoro da mamaki, suka ce wa junansu, “Wane ne wannan? Yana ba da umarni ga iska da ruwa ma, kuma suna biyayya da shi?”
遂對他們說:「你們的信德在那裏? 」他們又害怕又驚奇,彼此說:「這人到底是誰? 因為祂一出命,風和水也都服從祂。」
26 Suka shiga jirgin ruwa zuwa yankin Gerasenawa da yake a hayin tafkin, daga wajen Galili.
他們航行到革辣撒人的地方,就是加利肋亞的對面。
27 Da Yesu ya sauka daga jirgin, sai ga wani mutum mai aljanu daga garin. Mutumin ya daɗe bai sa tufafi ba, kuma ba ya zama a gida. Yana zama a cikin kaburbura.
耶穌一上了岸,迎面來了一個那城中附魔的人,他很久不穿衣服,也不住在家裏,而住在墳墓中。
28 Da ya ga Yesu, sai mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi, ya fāɗi a gabansa, yana ihu cewa, “Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ina roƙonka, kada ka ba ni wahala!”
他一看見耶穌,就喊叫起來,跪伏在祂在面前大聲說:「至高天主之子耶穌,我與你有什麼相干? 我求你不要磨難我! 」
29 Gama Yesu ya riga ya umarci mugun ruhun ya fita daga mutumin. Sau da yawa mugun ruhun ya sha kamunsa. Ko da yake akan daure shi hannu da ƙafa, da sarƙa, a kuma yi gadinsa, amma yakan tsinke sarƙoƙinsa, aljanun kuma su kore shi zuwa wuraren kaɗaici, inda ba kowa.
因為祂曾命令邪魔從那人身上出去,原來邪魔已多次抓住他,他曾被鐵鏈和腳鐐捆縳起來,被看管著;他卻掙斷鐵鏈,被魔鬼趕到荒野中。
30 Yesu ya tambaye shi, “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa, “Tuli,” gama aljanu masu ɗumbun yawa ne suna cikinsa.
耶穌問他說:「你叫什麼名字? 」他說:「軍旅。」因為有許多魔鬼進入了他身內。
31 Suka yi ta roƙonsa kada yă umarce su su shiga ramin Abis. (Abyssos g12)
魔鬼求耶穌,不要命他們到深淵中去。 (Abyssos g12)
32 A wurin kuwa, akwai babban garken aladu da suke kiwo a gefen tudu. Aljanun suka roƙi Yesu ya bar su, su shiga cikin aladun, ya kuwa yardar musu.
在那裡有一大群豬在山上牧放著,魔鬼就請求耶穌許他們進入那些豬內;耶穌准許了他們。
33 Da aljanun suka fita daga cikin mutumin, sai suka shiga cikin aladun. Garken kuma ya gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, kuma suka nutse.
於是,從那人身上出去,進入豬內,那群豬就從山崖上直衝到湖裏淹死了。
34 Da masu kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka ruga da gudu zuwa garin da kewaye suka kai labari.
放豬的看見發生的事,就逃去,到城裏和鄉間傳報開了。
35 Mutanen kuma suka fito don su ga abin da ya faru. Da suka iso wurin Yesu, sai suka tarar da mutumin da aljanun suka fita daga cikinsa, yana zaune kusa da Yesu sanye da tufafi, kuma cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su.
人就出來看那發生的事,來到耶穌前,發現脫離魔鬼的那人,穿著衣服,神智清醒,坐在耶穌跟前前;他們就害怕起來,
36 Waɗanda suka ga abin da faru, suka gaya wa mutanen yadda aka warkar da mai aljanun.
那些見過這事的人就對他們述說:那附魔的人怎樣被治好了。
37 Sai dukan mutanen yankin Gerasenawa suka roƙi Yesu ya bar su, don sun tsorata sosai. Sai Yesu ya shiga jirgin ruwa ya tafi.
革辣撒所有的人民要尸離開他們,因為他們十分恐懼。祂便上船回去。
38 Mutumin da aka fitar da aljanun daga cikinsa, ya roƙi Yesu don yă tafi tare da shi, amma Yesu ya sallame shi ya ce,
脫離魔鬼的那人祈求耶穌:要同耶穌在一起;但耶穌打發他回去,說:
39 “Koma gida, ka shaida babban alherin da Allah ya yi maka.” Sai mutumin ya tafi yana faɗin abin da Yesu ya yi masa a duk garin.
「你回家去吧!傳述天主為你做了何等大事。」
40 Da Yesu ya koma, taron suka marabce shi, don dā ma duk suna jiransa.
耶穌回來時,群眾都迎接祂,因為眾人都在等候祂。
41 Sai wani mutum mai suna Yayirus, wani mai mulkin majami’a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, yana roƙonsa ya zo gidansa,
來弓一個人,名叫雅依洛,這人是一個會堂長,跪伏在尸腳前,求祂到自己家中去,
42 domin diyarsa ɗaya tak, wadda ta kai shekara goma sha biyu, tana bakin mutuwa. Da Yesu yake kan hanyarsa, taron mutane masu yawa suka yi ta matsa shi a kowane gefe.
因為他有一個獨生女,約十二歲,快要死了。當耶穌去的時候,眾人都擁擠祂。
43 A wurin kuwa, akwai wata mace wadda tana da ciwon zubar da jini, har na shekara goma sha biyu, amma babu wanda ya iya warkar da ita.
有一個婦人,十二年來患血漏病,把全部家產都花在醫生身上,卻沒有一個能治好她。
44 Sai ta zo ta bayansa, ta taɓa bakin rigarsa. Nan da nan, zubar da jininta ya tsaya.
她來到耶穌後邊摸了摸祂衣服的繸頭,她的血漏立刻就止住了。
45 Yesu ya yi tambaya, “Wa ya taɓa ni?” Bayan kowa ya yi musu, sai Bitrus ya ce, “Ubangiji, ai, mutane da yawa suna matsinka ta kowane gefe.”
耶穌說:「誰摸了我? 」人都否認,伯多祿說:「老師,眾人都在擁擠著你! 」
46 Amma Yesu ya ce, “Wani ya taɓa ni, na san cewa iko ya fita daga wurina.”
耶穌卻說:「有人摸了我,因為我覺得有能力從我身上出去了。」
47 Sai macen, da ta ga ba halin ɓoyewa, sai ta fita, jikinta na rawa, ta fāɗi a gabansa. A gaban dukan mutanen, ta faɗi dalilin da ya sa ta taɓa shi, da yadda ta warke nan take.
那婦人看不能隱瞞,就戰戰競競地來跪伏在耶穌跟前,把自己摸祂的緣故和如何立刻病好的事,在眾百姓面前說了出來。
48 Sai Yesu ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”
耶穌遂對她說:「女兒,妳的信德救了妳,平安去吧! 」
49 Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’ar ya ce, “Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu.”
祂還在話話時,有人從會堂長家裏來說:「你的女兒死了,不必煩勞師傅了。」
50 Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita.”
耶穌聽了,就對他說:「不要害怕,只管信,她必得救。」
51 Da ya iso gidan Yayirus, sai ya hana kowa yă bi shi cikin ɗakin, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma mahaifin da mahaifiyar.
耶穌到了那家裏,除了伯多祿、若望、雅各伯和女孩子的父母外,不讓任何人同祂進去。
52 Ana cikin haka, dukan mutanen kuma sai kuka da makoki suke ta yi, domin yarinyar. Sai Yesu ya ce, “Ka daina yin kuka, ba tă mutu ba, tana barci ne.”
眾人都在痛哭哀弔女孩子。祂卻說:「不要哭泣,她並沒有死,只是睡著了。」
53 Sai suka yi masa dariya, da yake sun san cewa, ta mutu.
那些明知她己死的人,都譏笑祂。
54 Amma Yesu ya kama ta a hannu ya ce, “Diyata, tashi.”
耶穌拿起她的手來,喊說:「女孩,起來! 」
55 Ruhunta ya dawo, kuma ta tashi, nan take. Yesu ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci.
她的靈魂回來了,她就立起來了。耶穌吩咐給她吃的。
56 Iyayenta suka yi mamaki, amma ya ba su umarni kada su faɗa wa kowa abin da ya faru.
她的父母驚訝的出神。耶穌卻警告他們不要傳揚這事。

< Luka 8 >