< Luka 6 >

1 A wata ranar Asabbaci, Yesu yana bi ta gonakin hatsi, sai almajiran suka fara kakkarya kan hatsi suna murjewa a hannuwansu suna ci.
And it came to pass, on the first sabbath after the second day of the feast, that he was going through the fields of grain; and his disciples pulled the ears and ate, rubbing them in their hands.
2 Sai waɗansu Farisiyawa suka ce, “Me ya sa kuke yin abin da doka ta hana yi a ranar Asabbaci?”
And some of the Pharisees said to them: Why are you doing what it is not lawful to do on the sabbath-days?
3 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi, sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa ba?
And Jesus answered and said to them: Have you not read even that which David did, when he was hungry himself, and those who were with him,
4 Ya shiga gidan Allah, ya ɗauki keɓaɓɓen burodi, sa’an nan ya ci abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka. Ya kuma ba wa abokan tafiyarsa?”
that he entered the house of God, and took the loaves of the presence, and ate, and gave to those also who were with him, which it is not lawful, except for the priests alone, to eat?
5 Sai Yesu ya ce musu, “Ai, Ɗan Mutum ne Ubangijin Asabbaci.”
And he said to them: The Son of man is Lord also of the sabbath.
6 A wata ranar Asabbaci kuma, Yesu ya shiga majami’a yana koyarwa. To, a nan kuwa akwai wani mutumin da hannun damansa ya shanye.
And it came to pass, on another sabbath, that he entered the synagogue and taught; and a man was there, whose right hand was withered.
7 Farisiyawa da malaman dokoki suka zuba wa Yesu ido, su ga ko zai warkar a ranar Asabbaci, don su sami dalilin zarginsa.
And the scribes and Pharisees watched closely, whether he would heal on the sabbath-day, that they might find an accusation against him.
8 Amma Yesu ya san abin da suke tunani. Sai ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.” Sai ya tashi ya tsaya.
But he knew their thoughts; and he said to the man that had the withered hand: Rise, and stand forth in the midst. And he arose, and stood.
9 Yesu ya ce musu, “Ina tambayarku, me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a hallaka shi?”
Then Jesus said to them, I will ask you a question: Which is lawful on the sabbath, to do good, or to do evil? to save life, or to kill?
10 Sai ya kalle su duka, sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙe, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.
And looking round upon them all, he said to him: Stretch forth your hand. And he did so; and his hand was restored like the other.
11 Amma Farisiyawa da malaman Doka suka fusata, suka fara tattauna da junansu a kan abin da za su yi wa Yesu.
But they were filled with madness, and began to consult with one another what they should do to Jesus.
12 Wata rana, a cikin kwanakin nan, Yesu ya je wani dutse domin yă yi addu’a, ya kuma kwana yana addu’a ga Allah.
And it came to pass in those days, that he went out into the mountain to pray; and he spent the night in prayer to God.
13 Da gari ya waye, sai ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya zaɓi guda goma sha biyu daga cikinsu, waɗanda ya kira su, Manzanni.
And when it was day, he called to him his disciples; and from them he chose twelve, whom he also named apostles:
14 Siman (wanda ya kira Bitrus), ɗan’uwansa Andarawus, Yaƙub, Yohanna, Filibus, Bartolomeyu,
Simon, whom he also named Peter, and Andrew his brother, James and John, Philip and Bartholomew,
15 Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Siman wanda ake kira Zilot,
Matthew and Thomas, James the son of Alphæus, and Simon who is called Zelotes,
16 Yahuda ɗan Yaƙub, da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.
Judas the brother of James, and Judas Iscariot, who was also the traitor.
17 Sai ya sauko tare da su, ya tsaya a wani fili. A can, akwai taro mai yawa na almajiransa, da kuma mutane masu yawan gaske daga ko’ina a Yahudiya, Urushalima da kuma Taya da Sidon da suke bakin teku,
And he came down with them, and stood in a plain; and with him stood a multitude of his disciples, and a great number of people from all Judea and Jerusalem, and the sea-coast of Tyre and Sidon, who had come to hear him, and to be healed of their diseases,
18 waɗanda suka zo domin su ji shi, a kuma warkar da cututtukansu. Waɗanda suke fama da mugayen ruhohi kuwa aka warkar da su.
and those who were oppressed by evil spirits; and they were cured.
19 Kuma dukan mutane suka yi ƙoƙari su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.
And the whole multitude sought to touch him: for power went forth from him, and healed them all.
20 Da ya dubi almajiransa, sai ya ce, “Masu albarka ne ku da kuke matalauta, gama mulkin Allah naku ne.
And he lifted up his eyes on his disciples, and said: Blessed are you that are poor, for yours is the kingdom of God.
21 Masu albarka ne ku da kuke jin yunwa yanzu, gama za ku ƙoshi. Masu albarka ne ku da kuke kuka yanzu, gama za ku yi dariya.
Blessed are you that hunger now, for you shall be satisfied. Blessed are you that weep now, for you shall laugh.
22 Masu albarka ne sa’ad da mutane suka ƙi ku, suka ware ku, suka zage ku, suna ce da ku mugaye, saboda Ɗan Mutum.
Blessed are you when men shall hate you, and shall withdraw themselves from you, and reproach you, and cast out your name as evil, on account of the Son of man.
23 “Ku yi farin ciki a wannan rana, ku kuma yi tsalle don murna, saboda ladarku yana da yawa a sama. Gama haka kakanninsu suka yi wa annabawa.
Rejoice in that day, and leap for joy; for behold, your reward is great in heaven: for so did their fathers to the prophets.
24 “Amma kaitonku da kuke da arziki, gama kun riga kun sami ta’aziyyarku.
But alas for you that are rich! for you have received your consolation.
25 Kaitonku da kuke ƙosassu yanzu, gama za ku zauna da yunwa. Kaitonku da kuke dariya yanzu, gama za ku yi makoki da kuka.
Alas for you that are full! for you shall be hungry. Alas for you that laugh now! for you shall mourn and weep.
26 Kaitonku sa’ad da dukan mutane suna magana mai kyau a kanku, gama haka kakanninsu suka yi da annabawan ƙarya.
Alas for you, when men shall speak well of you! for so did their fathers to the false prophets.
27 “Amma ina faɗa muku, ku da kuke ji na, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku yi wa masu ƙinku alheri.
But I say to you that hear: Love your enemies; do good to them that hate you;
28 Ku albarkaci waɗanda suke la’anta ku, ku kuma yi wa waɗanda suke wulaƙanta ku addu’a.
bless them that curse you; pray for them that abuse you.
29 In wani ya mare ka a wannan kumatu, juya masa ɗayan ma, in wani ya ƙwace maka babban riga, kada ma ka hana masa’yar cikin ma.
To him that strikes you on one cheek, offer also the other; and from him that takes away your mantle, withhold not your coat.
30 Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema yă mayar maka.
Give to every one that asks of you; and of him that takes away your goods, ask them not again.
31 Ka yi wa waɗansu abin da kai kake so su yi maka.
And as you would that men should do to you, do you also in like manner to them.
32 “In kana ƙaunar masu ƙaunarka ne kawai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma suna ƙaunar waɗanda suke ƙaunarsu.
And if you love them that love you, what thanks have you? for even sinners love those who love them.
33 In kuma kana yin alheri ga masu yi maka ne kaɗai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma suna yin haka.
And if you do good to them that do good to you, what thanks have you? for even sinners do the same.
34 In kana ba da bashi ga mutanen da za su iya biyan ka ne kawai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma, suna ba da bashi ga masu zunubi, da fata za a biya su tsab.
And if you lend to them from whom you hope to receive, what thanks have you? for even sinners lend to sinners, that they may receive the same.
35 Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama’ya’yan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye.
But love your enemies, and do good, and lend, hoping for nothing in return; and your reward shall be great, and you shall be sons of the Most High: for he is kind to the unthankful and the evil.
36 Ku zama masu jinƙai, kamar yadda Ubanku mai jinƙai ne.
Be you, therefore, merciful, as your Father also is merciful.
37 “Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku.
Judge not, and you shall not be judged; condemn not, and you shall not be condemned. Forgive, and you shall be forgiven.
38 Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yă yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku.”
Give, and it shall be given to you; good measure, pressed down, shaken together, and running over, shall men give into your lap. For with the same measure with which you measure, it shall be measured to you in return.
39 Ya kuma faɗa musu wannan misali cewa, “Makaho yana iya jagoran makaho ne? Ba sai dukansu biyu su fāɗa a rami ba?
And he spoke a parable to them: Can the blind lead the blind? Will not both fall into the pit?
40 Ɗalibi bai fi malaminsa ba, sai dai kowane ɗalibi wanda ya sami cikakkiyar koyarwa, zai zama kamar malaminsa.
The disciple is not above his teacher; but every accomplished disciple shall be as his teacher.
41 “Don me kake duban ɗan tsinke da yake idon ɗan’uwanka, amma ba ka kula da gungumen da yake a naka ido ba?
And why do you look at the splinter that is in your brother’s eye, but perceive not the beam that is in your own eye?
42 Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Ɗan’uwa, bari in cire maka ɗan tsinke da yake idonka,’ alhali kuwa, kai kanka ka kāsa ganin gungumen da yake a naka ido? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen daga idonka, sa’an nan za ka iya gani sosai, ka kuma cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka.”
Or, how can you say to your brother: Brother, let me pull out the splinter that is in your eye, when you yourself see not the beam that is in your own eye? Hypocrite, first pull the beam out of your own eye, and then you shall see clearly to pull out the splinter that is in your brother’s eye.
43 “Ba itace mai kyau da yake ba da munanan’ya’ya. Mummunan itace kuma ba ya ba da’ya’ya masu kyau.
For a good tree does not produce unsound fruit; nor does an unsound tree produce good fruit.
44 Kowane itace da irin’ya’yansa ne ake saninsa. Mutane ba sa tsinke’ya’yan ɓaure daga ƙaya, ko kuwa’ya’yan inabi daga sarƙaƙƙiya.
For every tree is known by its own fruit. For figs are not gathered from thorns, nor are grapes gathered from brambles.
45 Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne.”
The good man, out of the good treasury of his heart, brings forth that which is good; and the evil man, out of the evil treasury of his heart, brings forth that which is evil. For out of the abundance of his heart his mouth speaks.
46 “Don me kuke ce da ni, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ amma ba kwa yin abin da na faɗa?
But why call me Lord, Lord, and do not the things which I command?
47 Zan nuna muku kwatancin mutumin da yakan zo wurina, yă ji kalmomina, yă kuma aikata.
Every one that comes to me, and hears my words, and does them, I will show you to whom he is like.
48 Yana kama da mutumin da ya gina gida, wanda ya haƙa ƙasa da zurfi, sa’an nan ya kafa tushen ginin a kan dutse. Da ambaliyar ruwa ta taso, ƙarfin ruwa kuwa ya buga gidan, wannan bai jijjiga shi ba, domin an yi masa tushen gini na ainihi.
He is like a man that, when building a house, digged deep, and laid the foundation on the rock. And when a flood arose, the torrent dashed against that house, and it was not able to shake it, for it was founded on the rock.
49 Amma wanda yakan ji kalmomina, ba ya kuma aikata su, yana kama da mutumin da ya gina gida a ƙasa, ba tare da ya kafa tushen gini ba. A sa’ad da ƙarfin ruwa ya buga gidan, sai gidan yă rushe, mummunar rushewa kuwa.”
But he that hears, and does not, is like a man that built a house upon the earth, without a foundation, against which the torrent dashed with violence, and immediately it fell, and the ruin of that house was great.

< Luka 6 >