< Luka 24 >
1 Da sassafe a ranar farko ta mako, matan suka je kabarin, da kayan ƙanshin da suka shirya.
On the first day of the week, at early dawn, the women came to the tomb, bringing the spices they had prepared, and some other women were with them.
2 Suka iske an riga an gungurar da dutsen daga bakin kabarin.
They found the stone rolled away from the tomb,
3 Amma da suka shiga ciki, ba su iske jikin Ubangiji Yesu ba.
but when they went in, they did not find the body of the Lord Jesus.
4 Yayinda suna cikin tunani a kan wannan, nan take, ga waɗansu mutum biyu tsaye kusa da su, sanye da kaya masu ƙyalli, kamar walƙiya.
While they were greatly perplexed about this, behold, two men stood by them in dazzling clothes.
5 A cikin tsoro, matan suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa, amma mutanen suka ce musu, “Me ya sa kuke neman mai rai a cikin matattu?
The women were terrified and bowed their faces to the ground, but the men said to them, “Why do you seek the living among the dead?
6 Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili cewa,
He is not here, but is risen. Remember how he told you, while he was still in Galilee,
7 ‘Dole a ba da Ɗan Mutum ga hannun masu zunubi, a kuma gicciye shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.’”
that the Son of Man must be delivered up into the hands of sinful men, be crucified, and on the third day rise again.”
8 Sai suka tuna da maganarsa.
Then they remembered his words.
9 Da suka dawo daga kabarin, sai suka faɗa wa Sha Ɗayan nan da sauransu, dukan waɗannan abubuwa.
When they returned from the tomb, they told all these things to the eleven and to all the others.
10 Matan da suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa su ne, Maryamu Magdalin, da Yowanna, da Maryamu uwar Yaƙub, da waɗansu da suke tare da su.
It was Mary Magdalene, Joanna, Mary the mother of James, and the other women with them, who told these things to the apostles.
11 Amma ba su gaskata matan ba, domin sun ɗauki kalmominsu wani zancen banza ne.
But their words came across to the apostles as nonsense, and they did not believe them.
12 Duk da haka, Bitrus ya tashi a guje zuwa kabarin. Da ya sunkuya, sai ya ga ƙyallayen lilin kaɗai a kwance. Sai ya koma yana tunani a ransa, a kan abin da ya faru.
Peter, however, got up and ran to the tomb. When he stooped down to look in, he saw the linen cloths lying there by themselves. So he went away, wondering to himself what had happened.
13 A wannan rana kuma, biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani ƙauye, da ake kira Emmawus, da suke kusan mil bakwai daga Urushalima.
That same day two of Jesus' disciples were going to a village called Emmaus, which was about seven miles from Jerusalem.
14 Suna magana da juna a kan dukan abubuwan da suka faru.
They were talking with each other about everything that had happened.
15 Da suna magana, kuma suna tattauna waɗannan abubuwa da junansu, sai Yesu da kansa ya zo yana tafiya tare da su.
As they were talking and discussing these things, Jesus himself drew near and went along with them,
16 Amma ba a ba su ikon gane shi ba.
but their eyes were kept from recognizing him.
17 Sai ya tambaye, su ya ce, “Mene ne kuke tattaunawa da juna a cikin tafiyarku?” Suka tsaya shiru, da damuwa a fuskarsu.
He said to them, “What are you discussing with each other as you walk along, looking downcast?”
18 Ɗaya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai baƙo ne a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, a cikin kwanakin nan ba?”
Then the one whose name was Cleopas answered him, “Are yoʋ the only visitor in Jerusalem who does not know the things that have happened there in these last few days?”
19 Sai ya yi tambaya, “Waɗanne abubuwa?” Suka amsa suka ce, “Game da Yesu Banazare. Shi annabi ne, mai iko ne kuma cikin ayyukansa da maganarsa, a gaban Allah da kuma dukan mutane.
He said to them, “What things?” So they said to him, “The things concerning Jesus of Nazareth, who was a prophet mighty in deed and word before God and all the people,
20 Manyan firistoci da masu mulkinmu sun ba da shi a yi masa hukuncin mutuwa, suka kuwa gicciye shi.
and how the chief priests and our rulers handed him over to a sentence of death and crucified him.
21 Amma da, muna sa zuciya cewa, shi ne wanda zai fanshi Isra’ila. Bugu da ƙari kuma yau kwana uku ke nan tun da wannan abin ya faru.
But we had hoped that he was the one who would redeem Israel. And besides all this, today is now the third day since these things happened.
22 Har wa yau, waɗansu daga cikin matanmu sun ba mu mamaki. Sun je kabarin da sassafen nan,
Moreover, some women from our group amazed us. They were at the tomb early this morning,
23 amma ba su sami jikinsa ba. Sun dawo sun faɗa mana cewa, sun ga wahayi na mala’iku, da suka ce yana da rai.
and when they did not find his body, they came back saying that they had seen a vision of angels, who said that he was alive.
24 Sa’an nan, waɗansu abokanmu suka je kabarin, suka kuma tarar da kome kamar yadda matan suka faɗa, amma shi, ba su gan shi ba.”
Then some of our companions went to the tomb and found it to be so, just as the women had said, but they did not see him.”
25 Sai ya ce musu, “Ashe, ku marasa azanci ne, masu nauyin zuciyar gaskata, da dukan abin da annabawa suka faɗa!
Then Jesus said to them, “O foolish men, how slow of heart you are to believe all that the prophets have spoken!
26 Ai, dole Kiristi yă sha waɗannan wahalolin, kafin yă shiga ɗaukakarsa.
Was it not necessary for the Christ to suffer these things and enter into his glory?”
27 Sai ya fara bayyana musu daga Musa da dukan Annabawa, abin da dukan Nassi ya faɗa a kansa.”
And beginning from Moses and all the Prophets, he explained to them the things written about himself in all the Scriptures.
28 Da suka yi kusa da ƙauyen da za su, sai Yesu ya yi kamar zai ci gaba.
As they drew near to the village where they were headed, Jesus acted as if he were going farther.
29 Amma suka matsa masa suka ce, “Sauka wurinmu, don dare ya kusa, rana ta kusa fāɗuwa.” Sai ya sauka wurinsu.
But they urged him not to do so, saying, “Stay with us, for it is nearly evening, and the day is drawing to a close.” So he went in to stay with them.
30 Da ya zauna a tebur tare da su, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya ya fara ba su.
As he was reclining at the table with them, he took the bread, blessed and broke it, and gave it to them.
31 Sa’an nan idanunsu suka buɗe, suka gane shi. Sai ya ɓace musu.
Then their eyes were opened, and they recognized him, but he disappeared from their sight.
32 Suka tambayi juna, “Ashe, shi ya sa zukatanmu suka kuna a cikinmu, sa’ad da yake magana da mu a hanya, yana bayyana mana Nassi.”
They said to each other, “Were not our hearts burning within us as he spoke to us on the road and explained the Scriptures to us?”
33 Suka tashi nan da nan suka koma Urushalima. A can suka sami Sha Ɗayan nan da waɗanda suke tare da su a wuri ɗaya,
So they rose that very hour and returned to Jerusalem, where they found the eleven gathered together with their companions,
34 suna cewa, “Gaskiya ne! Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman”
saying, “The Lord is risen indeed and has appeared to Simon!”
35 Sai su biyun nan suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane Yesu yayinda ya kakkarya burodin.
Then they began describing what had happened on the road, and how Jesus had been made known to them when he broke the bread.
36 Suna cikin wannan zance, sai ga Yesu da kansa tsaye a tsakiyarsu. Sai ya ce musu, “Salama a gare ku!”
As they were saying these things, Jesus himself stood among them and said to them, “Peace be with you.”
37 Suka firgita, suka tsorota, suna tsammani fatalwa ce suka gani.
But they were startled and terrified, thinking they had seen a spirit.
38 Sai ya ce musu, “Don me kuke damuwa, kuke kuma shakka a zuciyarku?
Then he said to them, “Why are you troubled, and why are doubts arising in your hearts?
39 Ku duba hannuwana da ƙafafuna. Ai, ni ne da kaina! Ku taɓa ni ku ji, ai, fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.”
Look at my hands and my feet and see that it is I myself. Touch me and look at me, for a spirit does not have flesh and bones as you see that I have.”
40 Da ya faɗi haka, sai ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa.
After saying this, he showed them his hands and his feet.
41 Kuma har yanzu, suna cikin rashin gaskatawa, saboda murna da mamaki, sai ya tambaye su, “Kuna da abinci a nan?”
And while they were still amazed and in disbelief because of their joy, he said to them, “Do you have anything here to eat?”
42 Suka ba shi ɗan gasasshen kifi,
So they gave him a piece of broiled fish and some honeycomb.
43 ya karɓa ya ci a gabansu.
And he took them and ate in their presence.
44 Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.”
Then he said to them, “These are the words I spoke to you while I was still with you, that everything written about me in the Law of Moses, the Prophets, and the Psalms must be fulfilled.”
45 Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi.
Then he opened their minds to understand the Scriptures
46 Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu.
and said to them, “Thus it is written, and thus it was necessary for the Christ to suffer and to rise from the dead on the third day,
47 Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima.
and for repentance and remission of sins to be preached in his name to all nations, beginning from Jerusalem.
48 Ku ne shaidun waɗannan abubuwa.
You are witnesses of these things.
49 Zan aika muku da abin da Ubana ya yi alkawari. Amma ku dakata a birnin tukuna, sai an rufe ku da iko daga sama.”
And behold, I am sending the promise of my Father upon you, but stay in the city of Jerusalem until you are clothed with power from on high.”
50 Bayan ya kai su waje kusa da Betani, sai ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka.
Then he led them out as far as Bethany, and lifting up his hands he blessed them.
51 Yana cikin sa musu albarka, sai ya rabu da su. Aka ɗauke shi zuwa cikin sama.
While he was blessing them, he parted from them and was carried up into heaven.
52 Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai.
So they worshiped him and returned to Jerusalem with great joy.
53 Sai suka ci gaba da zama a cikin haikalin, suna yabon Allah.
And they were continually in the temple courts, praising and blessing God. Amen.