< Luka 20 >

1 Wata rana da Yesu yana koyar da mutane, yana musu wa’azin bishara a filin haikalin, sai manyan firistoci da malaman dokoki, tare da dattawan suka zo wurinsa.
And it came to pass, that, on one of those days, while he was teaching the people in the temple, and preaching the gospel, the chief priests and the scribes, with the elders, came to him,
2 Suka ce masa, “Gaya mana, da wane iko kake yin waɗannan abubuwa. Wa ya ba ka wannan ikon?”
and spoke to him, saying: Tell us by what authority you do these things? or, who is he that gave you this authority?
3 Ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku faɗa mini,
And he answered and said to them: I also will ask you one thing, and do you answer me.
4 baftismar Yohanna, daga sama ne ta fito, ko kuwa daga wurin mutane ne?”
Was the immersion of John from heaven, or from men?
5 Sai suka yi shawara da junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai tambaya, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’
And they reasoned among themselves, saying: If we say, From heaven, he will reply: Why, then, did you not believe him?
6 Amma in kuma muka ce, ‘Daga mutane ne,’ dukan mutanen za su jajjefe mu da duwatsu, domin sun tabbata cewa, Yohanna annabi ne.”
But if we say, From men, all the people will stone us; for they believe that John was a prophet.
7 Don haka, sai suka amsa cewa, “Ba mu san inda ta fito ba.”
And they answered, that they knew not whence it was.
8 Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku, ko da wane iko ne, nake yin waɗannan abubuwa ba.”
And Jesus said to them: Nor do I tell you by what authority I do these things.
9 Sai ya ci gaba da gaya wa mutanen wannan misali ya ce, “Wani mutum ya yi gonar inabi, sai ya ba da hayarta ga waɗansu manoma, sa’an nan ya yi wata doguwar tafiya.
And he began to speak this parable to the people: A man planted a vineyard, and let it out to vine-dressers, and was absent from home for a long time.
10 A lokacin girbi, sai ya aiki bawa zuwa wurin masu hayan, don su ba shi daga cikin’ya’yan inabin. Amma’yan hayan suka yi wa bawan nan dūka, suka kore shi hannu wofi.
And at the proper season, he sent a servant to those vine-dressers, that they should give him of the fruit of the vineyard. But the vine-dressers scourged him, and sent him away empty-handed.
11 Ya sāke aikan wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka kunyata shi, suka kuma kore shi hannu wofi.
And he then sent another servant. But they scourged him also, and treated him shamefully, and sent him away empty-handed.
12 Har yanzu, ya sāke aikan na uku, amma suka ji masa rauni, suka jefar da shi waje.
And he also sent a third; but they wounded him, and drove him out.
13 “Sai mai gonar inabin ya ce, ‘Me zan yi? Zan aiki ɗana da nake ƙauna, wataƙila za su girmama shi.’
And the owner of the vineyard said: What shall I do? I will send my beloved son; perhaps, when they see him, they will reverence him.
14 “Amma da’yan hayan suka gan shi, sai suka tattauna zancen, suka ce, ‘Wannan shi ne magājin, mu kashe shi sa’an nan gādon zai zama namu!’
But when the vine-dressers saw him, they reasoned among themselves, saying: This is the heir; come, let us kill him, that the inheritance may be ours.
15 Sai suka fitar da shi waje, suka kashe shi. “To, me mai gonar inabin zai yi da su?
And they drove him out of the vineyard, and killed him. What, then, will the owner of the vineyard do to them?
16 Zai zo ya karkashe masu hayan nan, ya ba wa waɗansu gonar inabin.” Da mutanen suka ji wannan, sai suka ce, “Allah ya sawwaƙa!”
He will come and destroy these vine-dressers, and will give his vineyard to others. And when they heard it, they said: Be it not so!
17 Yesu ya zura musu ido ya ce, “To, mene ne ma’anar abin da aka rubuta cewa, “‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kan ginin’
And he looked on them and said: What, then, does this mean, which is written, The stone which the builders rejected has become the head of the corner?
18 Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Kuma in dutsen nan ya fāɗi a kan wani, zai murƙushe shi.”
Whoever shall fall on this stone, shall be dashed to pieces; but on whomever it shall fall, it will make him as chaff for the wind.
19 Malaman dokoki da manyan firistoci, suka nemi hanyar kama shi nan da nan, domin sun san cewa, ya yi wannan misali a kansu ne, amma suna jin tsoron mutane.
And the chief priests and the scribes sought to lay hands on him, the same hour; (and yet they feared the people; ) for they knew that he spoke this parable against them.
20 Sai suka sa masa ido, suka aiki’yan leƙen asiri, waɗanda suka nuna kamar su masu gaskiya ne, suna nufin su kama shi game da abin da zai faɗa, domin su ba da shi ga gwamna mai mulki, da mai iko.
And they watched him, and sent spies, who feigned them selves to be just men, that they might take hold of his words, in order to deliver him up to the power and authority of the governor.
21 Sai’yan leƙen asirin suka tambaye shi, suka ce, “Malam, mun sani kana faɗin, kuma kana koyar da abin da yake daidai, ba ka kuma nuna bambanci, amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya.
And they asked him, saying: Teacher, we know that you speak and teach rightly, and do not regard the person of any, but teach the way of God in truth.
22 Daidai ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?”
Is it lawful for us to give tribute to Cæsar, or not?
23 Ya gane makircinsu, sai ya ce musu,
But he perceived their cunning, and said to them: Why do you tempt me?
24 “Nuna mini dinari. Hoton wane ne, kuma rubutun wane ne a kai?” Suka amsa, “Na Kaisar.”
Show me a denarius. Whose image and superscription has it? They answered and said: Cæsar’s.
25 Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”
He said to them: Give, therefore, to Cæsar the things that are Cæsar’s, and to God the things that are God’s.
26 Ba su iya kama shi a kan abin da ya faɗa a fili ba. Amsarsa ya ba su mamaki, shi ya sa suka yi shiru.
And they were not able to take hold of his words before the people. And they were astonished at his answer, and were silent.
27 Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa,
Then there came to him some of the Sadducees, (these deny that there is any resurrection, ) and asked him,
28 “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, ‘In ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata amma ba’ya’ya, dole mutumin ya aure gwauruwar, ya samo wa ɗan’uwansa’ya’ya.’
saying: Teacher, Moses wrote for us, If any man’s brother die, having a wife, and he die without children, that his brother should take his wife, and raise up children for his brother.
29 To, an yi waɗansu’yan’uwa bakwai. Na fari ya auri wata mace, ya mutu ba’ya’ya.
There were, therefore, seven brothers; and the first took a wife, and died without children;
30 Na biyun,
and the second took his wife, and he died without children;
31 da na ukun suka aure ta. Haka nan dukansu bakwai suka mutu babu’ya’ya.
and the third took her; and in like manner also the seven; and they left no children, and died.
32 A ƙarshe, ita macen ma ta mutu.
Last of all, the woman also died.
33 Shin, a tashin matattu, matar wa za tă zama? Tun da su bakwan nan, sun aure ta.”
Therefore, in the resurrection, of which of them shall she be the wife? for the seven had her as a wife.
34 Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure, (aiōn g165)
And Jesus answered and said to them: The children of this age marry, and are given in marriage. (aiōn g165)
35 amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba. (aiōn g165)
But those who shall be accounted worthy to attain that age, and the resurrection from the dead, neither marry, nor are given in marriage. (aiōn g165)
36 Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar mala’iku ne. Su’ya’yan Allah ne, tun da su’ya’yan tashin matattu ne.
For they can die no more; for they are like the angels, and are the sons of God, being the sons of the resurrection.
37 Amma bisa ga labari na bishiya nan, mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, ko Musa ma, ya nuna cewa, matattu suna tashi. Gama ya kira Ubangiji, ‘Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yaƙub.’
But: that the dead are raised, even Moses showed at The Bush, since he calls the Lord the God of Abraham, and the God of Isaac, and the God of Jacob.
38 Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai ne, gama a gare shi, duka na da rai.”
He is not a God of the dead, but of the living; for all live to him.
39 Sai waɗansu malaman dokoki suka amsa suka ce, “Ka faɗi daidai, malam!”
And certain of the scribes answered and said: Teacher, thou hast answered well.
40 Kuma ba wanda ya sami ƙarfin halin yin masa waɗansu tambayoyi.
And after this they durst not ask him any question at all.
41 Sai Yesu ya ce musu, “Yaya suke cewa, ‘Kiristi ɗan Dawuda ne?’
But he said to them: How say they that the Christ is the son of David?
42 Dawuda da kansa ya faɗa a cikin Zabura, “‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana,
Even David himself says, in the book of Psalms: The Lord said to my Lord, Sit at my right hand,
43 sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.”’
till I make thy enemies thy footstool.
44 Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji.’ Ta, yaya zai zama ɗansa?”
David, therefore, calls him Lord; and how is he his son?
45 Yayinda dukan mutane suna cikin sauraronsa, sai Yesu ya ce wa almajiransa,
And while all the people were listening, he said to his disciples:
46 “Ku yi hankali da malaman dokoki. Sukan so sa manyan riguna suna zaga, suna sha’awan karɓan gaisuwa a wuraren kasuwanci, da kuma wuraren zama mafi daraja a majami’u, da wuraren bangirma a bukukkuwa.
Beware of the scribes, who delight to walk in robes, and love greetings in the markets, and the first seats in the synagogues, and the first places at suppers;
47 Suna mamaye gidajen gwauraye, kuma don burga, suna dogayen addu’o’i. Ga irin waɗannan mutane, za a yi musu hukunci mai tsanani sosai.”
who eat up the houses of widows, and, for a pretext, make long prayers. These shall receive the greater condemnation.

< Luka 20 >