< Luka 2 >
1 A waɗancan kwanaki, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa ya kamata a yi ƙidaya a dukan masarautar Roma.
2 (Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.)
3 Sai kowa ya koma garinsa don a rubuta shi.
4 Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne.
5 Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki.
6 Yayinda suke can, sai lokacin haihuwar jaririn ya yi,
7 ta kuwa haifi ɗanta na fari. Ta nannaɗe shi a zane ta kuma kwantar da shi cikin wani kwami, don ba su sami ɗaki a masauƙi ba.
8 Akwai makiyaya masu zama a fili kusa da wurin, suna tsaron garkunan tumakinsu da dare.
9 Sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, suka kuwa tsorata ƙwarai.
10 Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane.
11 Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji.
12 Wannan zai zama alama a gare ku. Za ku tarar da jariri a nannaɗe a zane kwance a kwami.”
13 Ba labari sai ga taron rundunar sama suka bayyana tare da mala’ikan, suna yabon Allah suna cewa,
14 “Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama, a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.”
15 Da mala’ikun suka bar su, su suka koma sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu je Betlehem mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar mana.”
16 Sai suka tafi da sauri, suka tarar da Maryamu da Yusuf, da kuma jaririn kwance a kwami.
17 Sa’ad da suka gan shi, sai suka baza maganar da aka gaya musu game da yaron,
18 duk kuwa waɗanda suka ji wannan, suka yi mamaki a kan abin da makiyayan suka faɗa.
19 Amma Maryamu ta riƙe dukan waɗannan abubuwa ta kuma yi ta tunaninsu a zuciyarta.
20 Makiyayan kuwa suka koma, suna ɗaukaka suna kuma yabon Allah saboda dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.
21 A rana ta takwas, da lokaci ya yi da za a yi masa kaciya, sai aka ba shi suna Yesu, sunan da mala’ika ya ba shi kafin a yi cikinsa.
22 Da lokacin tsarkakewarsu bisa ga Dokar Musa ya cika, sai Yusuf da Maryamu suka ɗauke shi suka haura zuwa Urushalima don su miƙa shi ga Ubangiji
23 (yadda yake a rubuce a Dokar Ubangiji cewa, “Kowane ɗan fari, za a keɓe shi ga Ubangiji”),
24 don kuma su miƙa hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Dokar Ubangiji cewa, “kurciyoyi biyu ko’yan tattabarai biyu.”
25 To, akwai wani mutum a Urushalima mai suna Siman, shi mai adalci da kuma mai ibada. Yana jiran fansar Isra’ila, Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi.
26 An bayyana masa ta wurin Ruhu Mai Tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kiristi na Ubangiji.
27 Da Ruhu ya iza shi, sai ya shiga cikin filin haikali. Sa’ad da iyayen suka kawo jaririn nan Yesu don su yi masa abin da al’adar Doka ta bukaci,
28 sai Siman ya karɓi yaron a hannuwansa ya yabi Allah, yana cewa,
29 “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kamar yadda ka yi alkawari, yanzu ka sallami bawanka lafiya.
30 Gama idanuna sun ga cetonka,
31 wanda ka shirya a gaban dukan mutane,
32 haske don bayyanawa ga Al’ummai da kuma ɗaukaka ga mutanenka Isra’ila.”
33 Mahaifin yaron da kuma mahaifiyarsa suka yi mamaki abin da aka faɗa game da shi.
34 Sa’an nan Siman ya sa musu albarka ya ce wa Maryamu mahaifiyarsa, “An ƙaddara yaron nan yă zama sanadin fāɗuwa da tashin mutane da yawa a Isra’ila, zai kuma zama alamar da mutane ba za su so ba,
35 ta haka za a fallasa tunanin zukatan mutane da yawa. Ke ma, takobi zai soki zuciyarki.”
36 Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure,
37 ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da addu’a.
38 Tana haurawa wurinsu ke nan a wannan lokaci, sai ta yi wa Allah godiya ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke sauraron fansar Urushalima.
39 Bayan da Yusuf da Maryamu suka gama yin dukan abubuwan da Dokar Ubangiji ta bukaci, sai suka koma Galili suka tafi Nazaret garinsu.
40 Yaron kuwa ya yi girma ya yi ƙarfi; ya cika da hikima, alherin Allah kuwa yana bisansa.
41 Kowace shekara, iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa.
42 Da Yesu ya cika shekaru goma sha biyu, sai suka tafi Bikin bisa ga al’ada.
43 Bayan Bikin, da iyayen suka kama hanya don su koma gida, sai Yesu, yaron nan, ya tsaya a Urushalima, ba da saninsu ba.
44 Su kuwa sun ɗauka yana tare da su, saboda haka, suka yi ta tafiya har na yini guda. Sa’an nan suka fara nemansa cikin’yan’uwansu da abokansu.
45 Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima nemansa.
46 Bayan kwana uku, sai suka same shi a filin haikali zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu yana kuma yi musu tambayoyi.
47 Dukan waɗanda suka ji shi, suka yi mamakin fahimtarsa, da amsoshinsa.
48 Da iyayensa suka gan shi sai suka yi mamaki. Mahaifiyarsa ta ce masa, “Ɗana, don me ka yi mana haka? Ni da mahaifinka duk mun damu muna nemanka.”
49 Sai ya ce, “Don me kuke nemana? Ba ku san cewa, dole in kasance a gidan Ubana ba?”
50 Amma ba su fahimci abin da yake faɗin musu ba.
51 Sai ya koma Nazaret tare da su, yana yi musu biyayya. Mahaifiyarsa kuma ta riƙe dukan waɗannan abubuwa a zuciyarta.
52 Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane.