< Luka 15 >

1 Yanzu fa, masu karɓar haraji da “masu zunubi” duka suna taruwa don jin koyarwar Yesu.
Now the publicans and sinners drew near unto him to hear him.
2 Amma Farisiyawa da malaman dokoki suka yi gunaguni, suna cewa, “Wannan mutum yana karɓan ‘masu zunubi,’ kuma yana ci tare da su.”
And the Pharisees and the scribes murmured, saying: This man receiveth sinners, and eateth with them.
3 Sai Yesu ya faɗa musu wannan misali ya ce,
And he spoke to them this parable, saying:
4 “In ɗayanku yana da tumaki ɗari, sa’an nan ɗayansu ta ɓace. Ashe, ba zai bar tasa’in da tara a fili ya je neman wadda ta ɓace, har sai ya same ta ba?
What man of you that hath an hundred sheep: and if he shall lose one of them, doth he not leave the ninety-nine in the desert, and go after that which was lost, until he find it?
5 In ya same ta, zai sa ta a kafaɗa da murna,
And when he hath found it, lay it upon his shoulders, rejoicing:
6 ya dawo gida. Sa’an nan zai kira abokansa da maƙwabtansa wuri ɗaya ya ce, ‘Ku taya ni murna, na sami tunkiyana da ta ɓata.’
And coming home, call together his friends and neighbours, saying to them: Rejoice with me, because I have found my sheep that was lost?
7 Ina gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi guda ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci tasa’in da tara, waɗanda ba su bukatan tuba.
I say to you, that even so there shall be joy in heaven upon one sinner that doth penance, more than upon ninety-nine just who need not penance.
8 “Ko kuwa in wata mace tana da kuɗi na azurfa guda goma, sa’an nan ɗaya ya ɓata, ashe, ba za tă ƙuna fitila, ta share gidan, ta nema a hankali, har sai ta samu ba?
Or what woman having ten groats; if she lose one groat, doth not light a candle, and sweep the house, and seek diligently until she find it?
9 In ta same shi, sai ta kira ƙawayenta da maƙwabtanta wuri ɗaya, ta ce musu, ‘Ku taya ni murna, na sami kuɗina da ya ɓata.’
And when she hath found it, call together her friends and neighbours, saying: Rejoice with me, because I have found the groat which I had lost.
10 Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban mala’ikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba.”
So I say to you, there shall be joy before the angels of God upon one sinner doing penance.
11 Yesu ya ci gaba da cewa, “Akwai wani mutum wanda yake da’ya’ya biyu maza.
And he said: A certain man had two sons:
12 Ƙaramin ya ce wa mahaifinsu, ‘Baba, ba ni rabon gādona.’ Sai mahaifin ya raba musu dukiyarsa.
And the younger of them said to his father: Father, give me the portion of substance that falleth to me. And he divided unto them his substance.
13 “Bayan’yan kwanaki, sai ƙaramin ɗan ya tattara kayansa duk, ya tashi ya tafi wata ƙasa mai nisa. A can, ya ɓatar da dukiyarsa duka a rayuwar banza.
And not many days after, the younger son, gathering all together, went abroad into a far country: and there wasted his substance, living riotously.
14 Bayan ya ɓatar da kome, sai ga muguwar yunwa a dukan ƙasar, har ya shiga rashi.
And after he had spent all, there came a mighty famine in that country; and he began to be in want.
15 Sai ya je ya sami aiki a wurin wani mutumin ƙasar, wanda ya aike shi a gonakinsa, ya yi kiwon aladu.
And he went and cleaved to one of the citizens of that country. And he sent him into his farm to feed swine.
16 Ya yi marmarin cin dusan da aladun suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu.
And he would fain have filled his belly with the husks the swine did eat; and no man gave unto him.
17 “Da hankalinsa ya dawo, sai ya ce, ‘Kai, bayin mahaifina guda nawa ne, da suke da abinci fiye da isashe, ni kuma ina nan, zan mutu don yunwa!
And returning to himself, he said: How many hired servants in my father’s house abound with bread, and I here perish with hunger?
18 Zan tashi in koma wurin mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi.
I will arise, and will go to my father, and say to him: Father, I have sinned against heaven, and before thee:
19 Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin bayinka.”’
I am not worthy to be called thy son: make me as one of thy hired servants.
20 Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa. “Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba.
And rising up he came to his father. And when he was yet a great way off, his father saw him, and was moved with compassion, and running to him fell upon his neck, and kissed him.
21 “Sai ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba.’
And the son said to him: Father, I have sinned against heaven, and before thee, I am not now worthy to be called thy son.
22 “Amma mahaifin ya ce wa bayinsa, ‘Maza! Ku kawo riga mafi kyau ku sa masa. Ku sa zobe a yatsarsa, da takalma kuma a ƙafafunsa.
And the father said to his servants: Bring forth quickly the first robe, and put it on him, and put a ring on his hand, and shoes on his feet:
23 Ku kawo ɗan saniya mai ƙiba ku yanka. Bari mu yi biki mu yi shagali.
And bring hither the fatted calf, and kill it, and let us eat and make merry:
24 Gama ɗan nan nawa, da ya mutu, amma yanzu yana da rai kuma. Da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ Sai suka fara shagali.
Because this my son was dead, and is come to life again: was lost, and is found. And they began to be merry.
25 “Yayinda ake haka, babban ɗan yana gona. Da ya zo kusa da gida, sai ya ji ana kiɗi ana rawa.
Now his elder son was in the field, and when he came and drew nigh to the house, he heard music and dancing:
26 Sai ya kira ɗaya daga cikin bayin, ya tambaye shi abin da yake faruwa.
And he called one of the servants, and asked what these things meant.
27 Bawan ya ce, ‘Ai, ɗan’uwanka ne ya dawo, shi ne mahaifinka ya yanka ɗan saniya mai ƙiba, gama ya yi murna ya karɓi ɗansa da ya dawo gida lafiyayye, ba abin da ya same shi.’
And he said to him: Thy brother is come, and thy father hath killed the fatted calf, because he hath received him safe.
28 “Sai yayan ya yi fushi, ya ƙi shiga gida. Sai mahaifinsa ya fita ya roƙe shi.
And he was angry, and would not go in. His father therefore coming out began to entreat him.
29 Amma ya amsa wa mahaifinsa ya ce, ‘Duba! Duk waɗannan shekaru, ina yin maka aiki kamar bawa, ban taɓa maka rashin biyayya ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan akuya domin in yi shagali da abokaina ba.
And he answering, said to his father: Behold, for so many years do I serve thee, and I have never transgressed thy commandment, and yet thou hast never given me a kid to make merry with my friends:
30 Amma da wannan ɗan naka, wanda ya ɓatar da dukiyarka a kan karuwai ya dawo, ka yanka masa ɗan saniya mai ƙiba!’
But as soon as this thy son is come, who hath devoured his substance with harlots, thou hast killed for him the fatted calf.
31 “Sai mahaifin ya ce masa, ‘Ɗana, kullum kana nan tare da ni, kuma duk abin da nake da shi, naka ne.
But he said to him: Son, thou art always with me, and all I have is thine.
32 Amma ya zama mana dole, mu yi shagali, mu yi murna, domin ɗan’uwan nan naka, da ya mutu, yanzu kuwa yana da rai, da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’”
But it was fit that we should make merry and be glad, for this thy brother was dead and is come to life again; he was lost, and is found.

< Luka 15 >