< Firistoci 1 >
1 Ubangiji ya kira Musa ya yi masa magana daga cikin Tentin Sujada ya ce,
While Moses/I was [standing near the entrance] to the Sacred Tent, Yahweh called to him/me from inside the tent. He said to Moses/me,
2 “Yi magana da Isra’ilawa ka ce musu, ‘Duk sa’ad da waninku ya kawo hadaya ga Ubangiji, ku kawo hadayarku ta dabba daga garkenku ta shanu ko kuwa daga tumakinku.
“Tell this to the Israeli people: ‘When any of you brings an offering to Yahweh, bring one of your sheep or goats or cattle.
3 “‘In hadaya ta ƙonawar daga shanu ne, sai yă miƙa namiji marar lahani. Dole yă kawo shi a ƙofar Tentin Sujada don yă zama yardajje ga Ubangiji.
‘If what you are offering is a bull that will be completely burned [on the altar], it must not have any defects. You must take it to the entrance to the Sacred Tent, in order that it will be acceptable to Yahweh.
4 Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya ta ƙonawar, za a kuwa karɓa a madadinsa don a yi kafara dominsa.
You must lay your hands on the head of the bull. When you do that, Yahweh will accept [its death in your place] to forgive/pardon you for the sins that you have committed.
5 Zai yanka ɗan bijimin a gaban Ubangiji, Haruna kuwa da’ya’yansa maza firist, za su kawo jinin su kuma yafa shi a kan bagaden a kowane gefe a mashigin Tentin Sujada.
You must slaughter the bull in front of Yahweh. Then Aaron’s sons, who are priests, will bring the blood and sprinkle it against all sides of the altar near the entrance to the Sacred Tent.
6 Zai feɗe hadaya ta ƙonawar, yă yayyanka shi gunduwa-gunduwa.
You must remove the skin of the animal and cut the animal into pieces. You must wash the inner parts and the legs of the bull.
7 ’Ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci za su hura wuta a bagade, su kuma shirya itace a kan wutar.
Then Aaron’s sons will put wood on the altar and light a fire.
8 Sa’an nan’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci za su shirya gunduwa-gunduwar haɗe da kan da kuma kitsen a kan itace mai cin wuta wanda yake a kan bagaden.
Then they will arrange the pieces, including the head and the fat, on the burning wood.
9 Zai wanke kayan cikin da kuma ƙafafun da ruwa, firist ɗin kuwa zai ƙone dukan waɗannan a kan bagade. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
Then one of the priests will completely burn all of it on the altar. And the aroma will be pleasing to Yahweh.
10 “‘In hadaya ta ƙonawar daga garke ne, ko na tumaki, ko na awaki, zai miƙa namiji ne marar lahani.
‘If you are offering a sheep or a goat, it must be a male without any defect.
11 Zai yanka shi a gefen arewa na bagaden a gaban Ubangiji,’ya’yan Haruna firistoci kuwa za su yayyafa jinin dabbar a bagaden a kowane gefe.
You must slaughter it in front of Yahweh, on the north side of the altar, [and drain all the blood into a bowl]. Then Aaron’s sons will sprinkle the blood against all sides of the altar.
12 Zai yanka shi gunduwa-gunduwa, firist kuwa zai shirya su haɗe da kan, da kuma kitsen a kan itace mai cin wutar da yake a kan bagade.
You must cut the animal into pieces. You must wash the inner parts and the legs of the animal. Then the priests will arrange the pieces, including the head and the fat, on the burning wood.
13 Zai wanke kayan cikin da kuma ƙafafun da ruwa, firist ɗin kuwa zai ƙone dukan waɗannan a kan bagade. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
Then one of the priests will take all of it and completely burn all of it on the altar. And the aroma as it burns will be pleasing to Yahweh.
14 “‘In hadaya ga Ubangiji ɗin, hadaya ta ƙonawa ta tsuntsaye ce, zai miƙa kurciya ko’yar tattabara.
‘If what you are offering to Yahweh is a bird, you must offer a dove or a young pigeon.
15 Firist zai kawo ta bagade, yă murɗe wuyan tsuntsun yă ƙone shi a kan bagade; zai tsiyaye jininsa tsuntsun a gefen bagaden.
The priest will take it to the altar and wring/twist off its head. Then he will burn the head on the altar. He will drain out the bird’s blood onto the side of the altar.
16 Amma zai ɗauki kayan cikin tsuntsun da gashin yă zubar da su a gefen bagaden a wajen gabas a wurin zuba toka.
Then he will remove the bird’s (craw/food-grinding pouch) and what is inside it, and throw it on the east side of the altar, where the ashes are thrown.
17 Zai tsaga shi biyu a tsaka, amma ba zai raba shi ba. Firist ɗin zai ɗibiya shi a bisa itacen da yake bisa bagaden, yă ƙone shi. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
Then he will grasp the bird’s wings and partially tear the bird open. Then he will burn it completely in the fire on the altar. And the aroma will be pleasing to Yahweh.’