< Firistoci 25 >

1 Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai ya ce,
וידבר יהוה אל משה בהר סיני לאמר
2 “Yi wa Isra’ilawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, dole ƙasar kanta ta kiyaye Asabbaci ga Ubangiji.
דבר אל בני ישראל ואמרת אלהם כי תבאו אל הארץ אשר אני נתן לכם--ושבתה הארץ שבת ליהוה
3 Shekara shida, za ku yi shuki, shekara shida kuma za ku aske gonakin inabinku, ku kuma tattara hatsinsu.
שש שנים תזרע שדך ושש שנים תזמר כרמך ואספת את תבואתה
4 Amma a shekara ta bakwai, ƙasar za tă sami hutun Asabbaci, Asabbaci ga Ubangiji. Kada ku yi shuki a gonakinku, ko kuwa ku aske gonakinku na inabi.
ובשנה השביעת שבת שבתון יהיה לארץ--שבת ליהוה שדך לא תזרע וכרמך לא תזמר
5 Kada ku girbe abin da ya yi girma ba tare da ku kuka shuka ba, ko ku girbe inabin da ba ku aske ba. Ƙasar za tă kasance da shekarar hutu.
את ספיח קצירך לא תקצור ואת ענבי נזירך לא תבצר שנת שבתון יהיה לארץ
6 Duk abin da gonar ta ba da amfani a shekara ta Asabbaci, zai zama abinci gare ku, wa kanku, bayinku maza da mata, da ma’aikatan da kuka ɗauka aiki, da kuma waɗanda ba zama ɗinɗinɗin suke yi tare da ku ba,
והיתה שבת הארץ לכם לאכלה--לך ולעבדך ולאמתך ולשכירך ולתושבך הגרים עמך
7 haka ma zai zama abinci domin dabbobinku, da kuma namun jeji a ƙasarku. Duk abin da ƙasar ta bayar za a ci.
ולבהמתך--ולחיה אשר בארצך תהיה כל תבואתה לאכל
8 “‘Ku ƙirga asabbatai bakwai na shekaru bakwai, sau bakwai. Gama asabbatai bakwai na shekaru bakwai za su yi daidai da shekaru arba’in da tara.
וספרת לך שבע שבתת שנים--שבע שנים שבע פעמים והיו לך ימי שבע שבתת השנים תשע וארבעים שנה
9 Sa’an nan a busa ƙaho a ko’ina, a rana ta goma ga wata na bakwai; a Ranar Kafara, a busa ƙaho a dukan ƙasarku.
והעברת שופר תרועה בחדש השבעי בעשור לחדש ביום הכפרים תעבירו שופר בכל ארצכם
10 Ku keɓe shekara ta hamsin ku kuma yi shelar’yanci a dukan ƙasar ga mazaunanta. Za tă zama shekarar murna gare ku; kowannenku zai koma ga mallakar iyalinsa, kuma kowa ga danginsa.
וקדשתם את שנת החמשים שנה וקראתם דרור בארץ לכל ישביה יובל הוא תהיה לכם ושבתם איש אל אחזתו ואיש אל משפחתו תשבו
11 Shekara ta hamsin za tă zama ta murna a gare ku; kada ku yi shuki, kada kuma ku yi girbi abin da ya yi girma da kansa, ko ku girbe inabin da ba ku lura da shi ba.
יובל הוא שנת החמשים שנה--תהיה לכם לא תזרעו--ולא תקצרו את ספיחיה ולא תבצרו את נזריה
12 Gama shekara ce ta murna, za tă kuma zama mai tsarki a gare ku, ku dai ci abin da aka ɗauka kai tsaye daga gonaki.
כי יובל הוא קדש תהיה לכם מן השדה--תאכלו את תבואתה
13 “‘A wannan Shekara ta Murna, kowa zai koma ga mallakarsa.
בשנת היובל הזאת תשבו איש אל אחזתו
14 “‘In ka sayar da gona wa wani daga mutanen ƙasarka, ko ka saya wata gona daga gare shi, kada ku cuci juna.
וכי תמכרו ממכר לעמיתך או קנה מיד עמיתך--אל תונו איש את אחיו
15 Sa’ad da mutum ya sayi fili daga abokin zamansa, kuɗin zai kasance bisa ga yawan shekara hamsin ta murna da suka wuce, da kuma bisa ga yawan shekarun noma da suka rage kafin wata shekara hamsin ta murna.
במספר שנים אחר היובל תקנה מאת עמיתך במספר שני תבואת ימכר לך
16 Idan shekarun suna da yawa, sai ku kara kuɗin filin, idan kuma shekarun ba su da yawa, sai ku rage kuɗin filin, gama ainihin abin da ake sayar maka shi ne yawan hatsin.
לפי רב השנים תרבה מקנתו ולפי מעט השנים תמעיט מקנתו כי מספר תבואת הוא מכר לך
17 Kada ku cuci juna, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.
ולא תונו איש את עמיתו ויראת מאלהיך כי אני יהוה אלהיכם
18 “‘Ku bi farillaina, ku kuma yi hankali ga kiyaye dokokina, za ku kuwa zauna lafiya a ƙasar.
ועשיתם את חקתי ואת משפטי תשמרו ועשיתם אתם--וישבתם על הארץ לבטח
19 Sa’an nan ƙasar za tă ba da amfaninta, za ku kuwa ci ku ƙoshi, ku kuma zauna lafiya.
ונתנה הארץ פריה ואכלתם לשבע וישבתם לבטח עליה
20 Mai yiwuwa ku ce, “Me za mu ci a shekara ta bakwai in ba mu yi shuki ko girbin hatsinmu ba?”
וכי תאמרו מה נאכל בשנה השביעת הן לא נזרע ולא נאסף את תבואתנו
21 Zan aika muku da irin albarka a shekara ta shida har da ƙasar za tă ba da amfani isashe na shekara uku.
וצויתי את ברכתי לכם בשנה הששית ועשת את התבואה לשלש השנים
22 Yayinda kuke shuki a shekara ta takwas, za ku kasance da raguwa hatsi na shekarar da ta wuce, za ku kuma ci gaba da ci daga gare shi har girbin shekara ta tara yă shigo.
וזרעתם את השנה השמינת ואכלתם מן התבואה ישן עד השנה התשיעת עד בוא תבואתה--תאכלו ישן
23 “‘Kada a sayar da gona ɗinɗinɗin, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi ne kawai, kuma’yan haya nawa.
והארץ לא תמכר לצמתת--כי לי הארץ כי גרים ותושבים אתם עמדי
24 Ko’ina a ƙasar da kuke da mallaka, dole ku tanadar da dama fansar ƙasar.
ובכל ארץ אחזתכם גאלה תתנו לארץ
25 “‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta, ya kuma sayar da mallakarsa, sai danginsa na kusa yă je yă fanshi abin da mutumin ƙasarsa ya sayar.
כי ימוך אחיך ומכר מאחזתו--ובא גאלו הקרב אליו וגאל את ממכר אחיו
26 In mutumin ba shi da wanda zai fansa masa ita, shi kansa kuwa ya wadace, ya kuma sami isashen halin fansarta,
ואיש כי לא יהיה לו גאל והשיגה ידו ומצא כדי גאלתו
27 sai yă lasafta yawan shekarun da aka yi tun da an sayar da filin. Kuɗin filin zai dangana ga yawan shekarun da suka rage kafin shekara hamsin ta murna da za tă zo; sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.
וחשב את שני ממכרו והשיב את העדף לאיש אשר מכר לו ושב לאחזתו
28 Amma in bai sami halin sāke biyansa ba, abin nan da ya sayar zai ci gaba da zama mallakar mai sayan, sai Shekara ta Murna. Za a maido masa da ita a Shekara ta Murna, sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa.
ואם לא מצאה ידו די השיב לו--והיה ממכרו ביד הקנה אתו עד שנת היובל ויצא ביבל ושב לאחזתו
29 “‘In mutum ya sayar da gida a birni mai katanga, yana da izini yă fanshe shi a ƙarshen shekara guda, bayan ya sayar da shi.
ואיש כי ימכר בית מושב עיר חומה--והיתה גאלתו עד תם שנת ממכרו ימים תהיה גאלתו
30 In ba a fanshe shi a ƙarshen shekara ba, gidan da yake a birni mai katanga, zai zama mallakar na ɗinɗinɗin na mai sayan da kuma zuriyarsa. Ba za a mai da shi a Shekara ta Murna ba.
ואם לא יגאל עד מלאת לו שנה תמימה--וקם הבית אשר בעיר אשר לא (לו) חמה לצמיתת לקנה אתו לדרתיו לא יצא ביבל
31 Amma za a ɗauki gidaje a ƙauyuka marasa katanga kewaye da su daidai da gonaki. Za a iya fanshe su, a kuma mayar da su a Shekara ta Murna.
ובתי החצרים אשר אין להם חמה סביב--על שדה הארץ יחשב גאלה תהיה לו וביבל יצא
32 “‘Kullum, Lawiyawa suna da izini su fanshi gidajensu a biranen Lawiyawa waɗanda suka mallaka.
וערי הלוים--בתי ערי אחזתם גאלת עולם תהיה ללוים
33 Saboda haka ana iya fansa mallakar Lawiyawa, wato, gidan da aka sayar a duk birnin da yake nasu, za a kuma mayar a Shekara ta Murna, gama gidaje a biranen Lawiyawa, mallakar Isra’ilawa ne.
ואשר יגאל מן הלוים ויצא ממכר בית ועיר אחזתו ביבל כי בתי ערי הלוים הוא אחזתם בתוך בני ישראל
34 Amma kada a sayar da filayen kiwo na waɗannan birane; mallakarsu ce, ta ɗinɗinɗin.
ושדה מגרש עריהם לא ימכר כי אחזת עולם הוא להם
35 “‘In ɗaya daga ciki mutanen ƙasarku ya talauta, ba ya kuma iya tallafa wa kansa a cikinku, sai ku taimake shi kamar yadda za ku yi da baƙo a cikinku.
וכי ימוך אחיך ומטה ידו עמך--והחזקת בו גר ותושב וחי עמך
36 Kada ku karɓi riba ta kowace iri daga gare shi, amma ku ji tsoron Allahnku, saboda mutumin ƙasarku yă ci gaba da zama a cikinku.
אל תקח מאתו נשך ותרבית ויראת מאלהיך וחי אחיך עמך
37 Kada ku ba shi rancen kuɗi da ruwa, ko ku sayar masa abinci don samun riba.
את כספך--לא תתן לו בנשך ובמרבית לא תתן אכלך
38 Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, don in ba ku ƙasar Kan’ana in kuma zama Allahnku.
אני יהוה אלהיכם אשר הוצאתי אתכם מארץ מצרים--לתת לכם את ארץ כנען להיות לכם לאלהים
39 “‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta a cikinku, ya kuma sayar da kansa gare ku, kada ku sa yă yi kamar bawa.
וכי ימוך אחיך עמך ונמכר לך--לא תעבד בו עבדת עבד
40 Amma a ɗauke shi a matsayin ma’aikacin da aka ɗauka aiki, ko mazaunan da ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, sai yă yi muku aiki sai Shekara ta Murna.
כשכיר כתושב יהיה עמך עד שנת היבל יעבד עמך
41 Sa’an nan a sake shi da’ya’yansa, yă kuma koma ga danginsa da mallakar kakanninsa.
ויצא מעמך--הוא ובניו עמו ושב אל משפחתו ואל אחזת אבתיו ישוב
42 Gama Isra’ilawa bayina ne, waɗanda na saya daga Masar, kada a sayar da su a matsayin bayi.
כי עבדי הם אשר הוצאתי אתם מארץ מצרים לא ימכרו ממכרת עבד
43 Kada ku gwada musu azaba, amma ku ji tsoron Allahnku.
לא תרדה בו בפרך ויראת מאלהיך
44 “‘Bayinku maza da mata, za su zo daga al’ummai da suke kewaye da ku, daga gare su za ku iya saya bayi.
ועבדך ואמתך אשר יהיו לך מאת הגוים אשר סביבתיכם--מהם תקנו עבד ואמה
45 Za ku iya saya waɗansu mutanen da ba sa zama ɗinɗinɗin a cikinku, da kuma membobin danginsu da aka haifa a ƙasarku.
וגם מבני התושבים הגרים עמכם מהם תקנו וממשפחתם אשר עמכם אשר הולידו בארצכם והיו לכם לאחזה
46 Za ku iya ba da su ga’ya’yanku a matsayin kayan gādo, za ku kuma iya mai da su bayi dukan rayuwarsu, amma kada ku yi mulki a bisa’yan’uwanku Isra’ilawa da tsanani.
והתנחלתם אתם לבניכם אחריכם לרשת אחזה--לעלם בהם תעבדו ובאחיכם בני ישראל איש באחיו לא תרדה בו בפרך
47 “‘In baƙo, ko wani da yake zama ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, ya wadace, ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku kuwa ya talauta, ya kuma sayar da kansa ga baƙon da yake zama a cikinku, ko memba na dangin baƙon,
וכי תשיג יד גר ותושב עמך ומך אחיך עמו ונמכר לגר תושב עמך או לעקר משפחת גר
48 yana da izini samun fansa, bayan ya sayar da kansa. Ɗaya daga cikin danginsa zai iya fansarsa.
אחרי נמכר גאלה תהיה לו אחד מאחיו יגאלנו
49 Kawu ko yaron ɗan’uwan mahaifin wannan mutum, ko kuwa wani dangi a cikin zuriyarsa, zai iya fanshe shi. Ko kuma in ya azurta, zai iya fansar kansa.
או דדו או בן דדו יגאלנו או משאר בשרו ממשפחתו יגאלנו או השיגה ידו ונגאל
50 Da shi da mai sayansa, za su ƙirga lokaci daga shekarar da ya sayar da kansa har zuwa Shekara ta Murna. Farashin sakinsa zai dangana a kuɗin da ake biyan ma’aikacin da aka ɗauka aiki, na yawan shekarun ne.
וחשב עם קנהו משנת המכרו לו עד שנת היבל והיה כסף ממכרו במספר שנים כימי שכיר יהיה עמו
51 In shekaru sun ragu, dole yă biya don fansarsa da kuɗi mai yawa fiye da wanda aka saye shi.
אם עוד רבות בשנים--לפיהן ישיב גאלתו מכסף מקנתו
52 In shekarun sun rage kaɗan ne kafin Shekara ta Murna, sai yă yi lissafin wannan, yă kuma biya fansarsa daidai wa daida.
ואם מעט נשאר בשנים עד שנת היבל--וחשב לו כפי שניו ישיב את גאלתו
53 Sai a yi da shi kamar ma’aikacin da aka ɗauka aiki, daga shekara zuwa shekara; dole ku tabbata mai shi bai mallake shi da tsanani ba.
כשכיר שנה בשנה יהיה עמו לא ירדנו בפרך לעיניך
54 “‘Ko ma ba a fanshe shi a ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi ba, sai a sake shi da’ya’yansa a Shekara ta Murna,
ואם לא יגאל באלה--ויצא בשנת היבל הוא ובניו עמו
55 gama Isra’ilawa nawa ne a matsayin bayi. Su bayina ne waɗanda na saya daga Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.
כי לי בני ישראל עבדים--עבדי הם אשר הוצאתי אותם מארץ מצרים אני יהוה אלהיכם

< Firistoci 25 >