< Firistoci 24 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa,
וידבר יהוה אל משה לאמר
2 “Ka umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen mai na zaitun da aka matse, don ƙuna fitilun yadda harshen wutar ba zai taɓa mutuwa ba.
צו את בני ישראל ויקחו אליך שמן זית זך כתית--למאור להעלת נר תמיד
3 Za a ajiye su waje da labulen Wuri Mafi Tsarki a Tentin Sujada, Haruna zai riƙa kula da fitilun a gaban Ubangiji, daga yamma zuwa safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa.
מחוץ לפרכת העדת באהל מועד יערך אתו אהרן מערב עד בקר לפני יהוה--תמיד חקת עולם לדרתיכם
4 Dole a ci gaba da shirya fitilu a kan wurin ajiye fitila na zinariya, a gaban Ubangiji.
על המנרה הטהרה יערך את הנרות לפני יהוה תמיד
5 “Ɗauki gari mai laushi a gasa dunƙulen burodi goma sha biyu, a yi amfani da humushi biyu na garwan gari don kowace burodi.
ולקחת סלת--ואפית אתה שתים עשרה חלות שני עשרנים יהיה החלה האחת
6 A shirya su jeri biyu, guda shida a kowane jeri a kan teburin da aka yi da zinariya zalla, a gaban Ubangiji.
ושמת אותם שתים מערכות שש המערכת על השלחן הטהר לפני יהוה
7 Za a zuba turare a kowane layin dunƙulen burodin don yă kasance abin tunawa a bisa burodin. Turaren zai ƙone a madadin burodin don yă zama kamar hadayar da aka miƙa da wuta ga Ubangiji.
ונתת על המערכת לבנה זכה והיתה ללחם לאזכרה אשה ליהוה
8 Za a shirya wannan gurasa a gaban Ubangiji kowane Asabbaci, a madadin Isra’ilawa a matsayin madawwamin alkawari.
ביום השבת ביום השבת יערכנו לפני יהוה--תמיד מאת בני ישראל ברית עולם
9 Wannan burodin zai zama na Haruna da’ya’yansa maza, waɗanda za su ci a tsattsarkan wuri, gama sashe ne mafi tsarki na rabonsu na kullum na hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji.”
והיתה לאהרן ולבניו ואכלהו במקום קדש כי קדש קדשים הוא לו מאשי יהוה--חק עולם
10 To, ɗan wata mutuniyar Isra’ila wanda mahaifinsa mutumin Masar ne, ya je cikin Isra’ilawa, sai faɗa ta tashi tsakaninsa da wani mutumin Isra’ila a cikin sansani.
ויצא בן אשה ישראלית והוא בן איש מצרי בתוך בני ישראל וינצו במחנה בן הישראלית ואיש הישראלי
11 Ɗan mutuniyar Isra’ila ya saɓi Sunan Ubangiji, ya kuma la’ana shi, saboda haka aka kawo shi wa Musa. (Sunan mahaifiyarsa Shelomit ne,’yar Dibri na kabilar Dan.)
ויקב בן האשה הישראלית את השם ויקלל ויביאו אתו אל משה ושם אמו שלמית בת דברי למטה דן
12 Suka sa shi a gidan tsaro sai lokacin da nufin Ubangiji ya nuna musu abin da za su yi da shi.
ויניחהו במשמר לפרש להם על פי יהוה
13 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
וידבר יהוה אל משה לאמר
14 “Ka kai mai saɓon nan waje da sansani. Duk waɗanda suka ji maganar da mai saɓon nan ya yi su ɗibiya hannuwansu a kansa, taron jama’a kuwa gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu.
הוצא את המקלל אל מחוץ למחנה וסמכו כל השמעים את ידיהם על ראשו ורגמו אתו כל העדה
15 Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Duk wanda ya zagi Allahnsa, alhakin zai rataya a wuyansa,
ואל בני ישראל תדבר לאמר איש איש כי יקלל אלהיו ונשא חטאו
16 duk wanda ya saɓi sunan Ubangiji, dole a kashe shi. Dole jama’a gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu. Ko baƙo, ko haifaffen ɗan ƙasa, sa’ad da ya saɓi Sunan Ubangiji, dole a kashe shi.
ונקב שם יהוה מות יומת רגום ירגמו בו כל העדה כגר כאזרח--בנקבו שם יומת
17 “‘Duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi.
ואיש כי יכה כל נפש אדם--מות יומת
18 Duk wanda ya kashe dabbar wani, dole yă biya, rai domin rai.
ומכה נפש בהמה ישלמנה--נפש תחת נפש
19 Duk wanda ya yi wa maƙwabcinsa rauni, sai a yi masa abin da ya yi;
ואיש כי יתן מום בעמיתו--כאשר עשה כן יעשה לו
20 karaya don karaya, ido don ido, haƙori don haƙori. Kamar yadda ya yi wa wani rauni, shi ma a yi masa.
שבר תחת שבר עין תחת עין שן תחת שן--כאשר יתן מום באדם כן ינתן בו
21 Duk wanda ya kashe dabba, dole yă biya, amma duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi.
ומכה בהמה ישלמנה ומכה אדם יומת
22 Za ku kasance da doka iri ɗaya wa baƙo da kuma wa haifaffen ɗan ƙasa. Ni ne Ubangiji Allahnku.’”
משפט אחד יהיה לכם כגר כאזרח יהיה כי אני יהוה אלהיכם
23 Sai Musa ya yi wa Isra’ilawa magana, suka kuwa kai mai saɓon waje da sansani, suka jajjefi shi da duwatsu. Isra’ilawa suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.
וידבר משה אל בני ישראל ויוציאו את המקלל אל מחוץ למחנה וירגמו אתו אבן ובני ישראל עשו כאשר צוה יהוה את משה

< Firistoci 24 >