< Firistoci 23 >
1 Ubangiji ya ce wa Musa,
locutus est Dominus ad Mosen dicens
2 “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Ga ƙayyadaddun bukukkuwa, ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji, da za ku sanar wa mutane su riƙa kiyayewa, su zama lokutan tarurruka masu tsarki.
loquere filiis Israhel et dices ad eos hae sunt feriae Domini quas vocabitis sanctas
3 “‘Akwai kwanaki shida da za ku iya yin aiki, amma rana ta bakwai, Asabbaci ne na hutu, rana mai tsarki ga jama’a. Kada ku yi wani aiki a ko’ina kuke da zama, Asabbaci ne ga Ubangiji.
sex diebus facietis opus dies septimus quia sabbati requies est vocabitur sanctus omne opus non facietis in eo sabbatum Domini est in cunctis habitationibus vestris
4 “‘Waɗannan su ne bukukkuwan da Ubangiji ya kafa da tsarkakakkun taron jama’a za su yi a ƙayyadaddun lokuta.
hae sunt ergo feriae Domini sanctae quas celebrare debetis temporibus suis
5 Bikin Ƙetarewar Ubangiji, zai fara da yamma a ranar goma sha huɗu na wata na fari.
mense primo quartadecima die mensis ad vesperum phase Domini est
6 A rana ta goma sha biyar na wannan wata, za a fara Bikin Burodi Marar Yisti na Ubangiji. Za ku yi kwana bakwai kuna cin burodi marar yisti.
et quintadecima die mensis huius sollemnitas azymorum Domini est septem diebus azyma comedetis
7 A rana ta fari, ku yi taro mai tsarki, ba kuwa za ku yi aiki na kullum ba.
dies primus erit vobis celeberrimus sanctusque omne opus servile non facietis in eo
8 Kwana bakwai za ku miƙa hadaya ga Ubangiji da wuta. A rana ta bakwai ɗin ku yi taro mai tsarki, ba za ku kuwa yi aiki na kullum ba.’”
sed offeretis sacrificium in igne Domino septem diebus dies autem septimus erit celebrior et sanctior nullumque servile opus fiet in eo
9 Ubangiji ya ce wa Musa,
locutusque est Dominus ad Mosen dicens
10 “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, kuka kuma girbe amfanin gonarta, sai ku kawo wa firist damin hatsi na farko da kuka girbe.
loquere filiis Israhel et dices ad eos cum ingressi fueritis terram quam ego dabo vobis et messueritis segetem feretis manipulos spicarum primitias messis vestrae ad sacerdotem
11 Zai kaɗa damin a gaban Ubangiji domin yă zama yardajje a madadinku; firist ɗin zai kaɗa shi a kashegarin Asabbaci.
qui elevabit fasciculum coram Domino ut acceptabile sit pro vobis altero die sabbati et sanctificabit illum
12 A ranar da kuka kaɗa damin, dole ku miƙa hadaya ta ƙonawa na ɗan rago bana ɗaya, marar lahani ga Ubangiji,
atque in eodem die quo manipulus consecratur caedetur agnus inmaculatus anniculus in holocaustum Domini
13 tare da hadaya ta gari mai laushi, humushi biyu haɗe da mai, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji, mai daɗin ƙanshi, da kuma abin sha kwalaba ɗaya na ruwan inabi.
et libamenta offerentur cum eo duae decimae similae conspersae oleo in incensum Domini odoremque suavissimum liba quoque vini quarta pars hin
14 Ba za ku ci wani burodi, ko gasasshen hatsi, ko sabon hatsi ba, sai ran nan da kuka kawo wannan hadaya ga Allahnku. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa, a duk inda kuke zama.
panem et pulentam et pultes non comedetis ex segete usque ad diem qua offeratis ex ea Deo vestro praeceptum est sempiternum in generationibus cunctisque habitaculis vestris
15 “‘Daga kashegarin Asabbaci, ranar da kuka kawo dami don hadaya ta kaɗawa, ku ƙirga cikakku makoni bakwai.
numerabitis ergo ab altero die sabbati in quo obtulistis manipulum primitiarum septem ebdomadas plenas
16 Ku ƙirga kwana hamsin har zuwa kashegarin Asabbaci na bakwai, sa’an nan ku miƙa hadaya ta sabon hatsi ga Ubangiji.
usque ad alteram diem expletionis ebdomadae septimae id est quinquaginta dies et sic offeretis sacrificium novum Domino
17 Daga ko’ina kuke da zama, ku kawo dunƙule biyu na humushin gari mai laushi da aka tuya da yisti, a matsayin hadaya ta kaɗawa ta’ya’yan fari na itatuwa ga Ubangiji.
ex omnibus habitaculis vestris panes primitiarum duos de duabus decimis similae fermentatae quos coquetis in primitias Domini
18 Tare da wannan, ku miƙa’yan raguna bakwai, kowanne bana ɗaya-ɗaya marar lahani, bijimi da kuma raguna biyu. Za su zama hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, tare da hadayunsu na hatsi, da hadayunsu na sha, hadaya da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
offeretisque cum panibus septem agnos inmaculatos anniculos et vitulum de armento unum et arietes duos et erunt in holocausto cum libamentis suis in odorem suavissimum Domino
19 Sa’an nan ku miƙa bunsuru ɗaya na hadaya don zunubi, da’yan raguna biyu, kowanne bana ɗaya-ɗaya, don hadaya ta salama.
facietis et hircum pro peccato duosque agnos anniculos hostias pacificorum
20 Firist zai kaɗa’yan raguna biyun a gaban Ubangiji, a matsayin hadaya ta kaɗawa, tare da burodin sababbin’ya’yan fari na itatuwan. Tsarkaken hadaya ce ga Ubangiji ga firist.
cumque elevaverit eos sacerdos cum panibus primitiarum coram Domino cedent in usum eius
21 A wannan rana za ku yi taro mai tsarki, ba kuwa za ku yi aiki na kullum ba. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa, a ko’ina kuke da zama.
et vocabitis hunc diem celeberrimum atque sanctissimum omne opus servile non facietis in eo legitimum sempiternum erit in cunctis habitaculis et generationibus vestris
22 “‘Sa’ad da kuka yi girbin gonarku, kada ku girbe har ƙarshen gefen gonar, ko ku yi kalar girbinku. Ku bar su wa matalauta da baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.’”
postquam autem messueritis segetem terrae vestrae non secabitis eam usque ad solum nec remanentes spicas colligetis sed pauperibus et peregrinis dimittetis eas ego Dominus Deus vester
23 Ubangiji ya ce wa Musa,
locutusque est Dominus ad Mosen dicens
24 “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘A ranar farko ga wata na bakwai, za tă zama ranar hutu, rana ce ta tuni da yin taro mai tsarki na sujada da za a fara busar ƙaho.
loquere filiis Israhel mense septimo prima die mensis erit vobis sabbatum memorabile clangentibus tubis et vocabitur sanctum
25 Kada ku yi aiki na kullum, amma ku miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.’”
omne opus servile non facietis in eo et offeretis holocaustum Domino
26 Ubangiji ya ce wa Musa,
locutusque est Dominus ad Mosen dicens
27 “Rana ta goma ta wata bakwai, za tă zama Ranar Kafara. Sai ku yi taro mai tsarki don ku yi mūsun kanku ku kuma miƙa hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji.
decimo die mensis huius septimi dies expiationum erit celeberrimus et vocabitur sanctus adfligetisque animas vestras in eo et offeretis holocaustum Domino
28 Kada ku yi aiki a ranar, gama Ranar Kafara ce, sa’ad da za a yi kafara saboda ku a gaban Ubangiji Allahnku.
omne opus non facietis in tempore diei huius quia dies propitiationis est ut propitietur vobis Dominus Deus vester
29 Duk wanda bai yi mūsun kansa a wannan rana ba, dole a raba shi daga mutanensa.
omnis anima quae adflicta non fuerit die hoc peribit de populis suis
30 Zan hallaka duk wani da ya yi aiki a wannan rana daga mutanensa.
et quae operis quippiam fecerit delebo eam de populo suo
31 Sam ba za ku yi wani aiki ba. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce, wa tsararraki masu zuwa, a ko’ina kuke da zama.
nihil ergo operis facietis in eo legitimum sempiternum erit vobis in cunctis generationibus et habitationibus vestris
32 Asabbaci ne na hutu dominku, kuma dole ku yi mūsun kanku. Daga yamman rana ta tara ga wata, har zuwa yamma na biye, za ku kiyaye Asabbacinku.”
sabbatum requietionis est adfligetis animas vestras die nono mensis a vespero usque ad vesperum celebrabitis sabbata vestra
33 Ubangiji ya ce wa Musa,
et locutus est Dominus ad Mosen dicens
34 “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘A ranar goma sha biyar ga wata na bakwai, za a fara Bikin Tabanakul na Ubangiji, zai kuma ɗauki kwana bakwai.
loquere filiis Israhel a quintodecimo die mensis huius septimi erunt feriae tabernaculorum septem diebus Domino
35 A ranar farko za tă zama ta taro mai tsarki, kada ku yi aiki na kullum.
dies primus vocabitur celeberrimus atque sanctissimus omne opus servile non facietis
36 Kwana bakwai za ku miƙa hadayun da aka yi da wuta ga Ubangiji, a rana ta takwas, ku yi taro mai tsarki, ku kuma miƙa hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji. Wannan ranar rufewar taro ce; kada ku yi aiki na kullum.
et septem diebus offeretis holocausta Domino dies quoque octavus erit celeberrimus atque sanctissimus et offeretis holocaustum Domino est enim coetus atque collectae omne opus servile non facietis in eo
37 (“‘Waɗannan su ne bukukkuwan da Ubangiji ya kafa, waɗanda za ku yi a matsayin tsarkakakkun taro, don kawo hadayun da aka yi da wuta ga Ubangiji, hadayu na ƙonawa da hadayu na hatsi, sadaka da kuma hadayu na sha, da ake bukata kowace rana.
hae sunt feriae Domini quas vocabitis celeberrimas et sanctissimas offeretisque in eis oblationes Domino holocausta et libamenta iuxta ritum uniuscuiusque diei
38 Waɗannan hadayu, ƙari ne a kan waɗannan na Asabbatan Ubangiji, haɗe kuma da kyautanku, da kome da kuka yi alkawari, da kuma hadayu yardar ran da za ku ba wa Ubangiji.)
exceptis sabbatis Domini donisque vestris et quae offertis ex voto vel quae sponte tribuitis Domino
39 “‘Saboda haka, farawa daga ranar goma sha biyar ga watan bakwai, bayan kun tara hatsin gona, ku yi bikin Ubangiji kwana bakwai; rana ta fari, rana hutu ce, rana ta takwas kuma rana hutu ce.
a quintodecimo ergo die mensis septimi quando congregaveritis omnes fructus terrae vestrae celebrabitis ferias Domini septem diebus die primo et die octavo erit sabbatum id est requies
40 A rana ta fari, za ku ɗebi zaɓaɓɓun’ya’yan itatuwa daga itatuwa, da rassan dabino, rassa masu ganye, da kuma ganyayen itacen wardi na rafi, ku yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku, kwana bakwai.
sumetisque vobis die primo fructus arboris pulcherrimae spatulasque palmarum et ramos ligni densarum frondium et salices de torrente et laetabimini coram Domino Deo vestro
41 Za ku kiyaye bikin nan har kwana bakwai a kowace shekara ga Ubangiji. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsarraraki masu zuwa, ku kiyaye ta a wata na bakwai.
celebrabitisque sollemnitatem eius septem diebus per annum legitimum sempiternum erit in generationibus vestris mense septimo festa celebrabitis
42 Ku zauna a bukkoki kwana bakwai. Dukan’yan ƙasa haifaffun Isra’ilawa, za su zauna a bukkoki
et habitabitis in umbraculis septem diebus omnis qui de genere est Israhel manebit in tabernaculis
43 don zuriyarku tă san cewa na sa Isra’ilawa suka zauna a bukkoki sa’ad da na fitar da su daga Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.’”
ut discant posteri vestri quod in tabernaculis habitare fecerim filios Israhel cum educerem eos de terra Aegypti ego Dominus Deus vester
44 Saboda haka Musa ya sanar wa Isra’ilawa ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji.
locutusque est Moses super sollemnitatibus Domini ad filios Israhel