< Firistoci 22 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa,
וַיְדַבֵּר יְהוָה אֶל־מֹשֶׁה לֵּאמֹֽר׃
2 “Faɗa wa Haruna da’ya’yansa maza, su lura da tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka keɓe gare ni da bangirma, saboda ba za su ƙazantar da sunana mai tsarki ba. Ni ne Ubangiji.
דַּבֵּר אֶֽל־אַהֲרֹן וְאֶל־בָּנָיו וְיִנָּֽזְרוּ מִקָּדְשֵׁי בְנֵֽי־יִשְׂרָאֵל וְלֹא יְחַלְּלוּ אֶת־שֵׁם קָדְשִׁי אֲשֶׁר הֵם מַקְדִּשִׁים לִי אֲנִי יְהוָֽה׃
3 “Faɗa musu cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, in wani zuriyarku ya ƙazantu, duk da haka ya kusaci tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka keɓe ga Ubangiji, dole a raba wannan mutum daga gabana. Ni ne Ubangiji.
אֱמֹר אֲלֵהֶם לְדֹרֹתֵיכֶם כָּל־אִישׁ ׀ אֲשֶׁר־יִקְרַב מִכָּל־זַרְעֲכֶם אֶל־הַקֳּדָשִׁים אֲשֶׁר יַקְדִּישׁוּ בְנֵֽי־יִשְׂרָאֵל לַֽיהוָה וְטֻמְאָתוֹ עָלָיו וְנִכְרְתָה הַנֶּפֶשׁ הַהִוא מִלְּפָנַי אֲנִי יְהוָֽה׃
4 “‘In zuriyar Haruna yana da kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga,
אִישׁ אִישׁ מִזֶּרַע אַהֲרֹן וְהוּא צָרוּעַ אוֹ זָב בַּקֳּדָשִׁים לֹא יֹאכַל עַד אֲשֶׁר יִטְהָר וְהַנֹּגֵעַ בְּכָל־טְמֵא־נֶפֶשׁ אוֹ אִישׁ אֲשֶׁר־תֵּצֵא מִמֶּנּוּ שִׁכְבַת־זָֽרַע׃
5 da duk kuma wanda ya taɓa wani abu mai rarrafe wanda yake ƙazantarwa, ko kuwa wani mutum mai ƙazanta,
אוֹ־אִישׁ אֲשֶׁר יִגַּע בְּכָל־שֶׁרֶץ אֲשֶׁר יִטְמָא־לוֹ אוֹ בְאָדָם אֲשֶׁר יִטְמָא־לוֹ לְכֹל טֻמְאָתֽוֹ׃
6 duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har yamma, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka tukuna.
נֶפֶשׁ אֲשֶׁר תִּגַּע־בּוֹ וְטָמְאָה עַד־הָעָרֶב וְלֹא יֹאכַל מִן־הַקֳּדָשִׁים כִּי אִם־רָחַץ בְּשָׂרוֹ בַּמָּֽיִם׃
7 Sa’ad da rana ta fāɗi, zai zama tsarkakakke, bayan wannan kuwa zai iya cin tsarkakakkun hadayu, gama abincinsa ne.
וּבָא הַשֶּׁמֶשׁ וְטָהֵר וְאַחַר יֹאכַל מִן־הַקֳּדָשִׁים כִּי לַחְמוֹ הֽוּא׃
8 Kada yă ci wani abin da ya mutu mushe, ko wanda namun jeji suka yayyaga, don kada yă ƙazantar da kansa. Ni ne Ubangiji.
נְבֵלָה וּטְרֵפָה לֹא יֹאכַל לְטָמְאָה־בָהּ אֲנִי יְהוָֽה׃
9 “‘Firistoci za su kiyaye umarnaina don kada su yi laifi su mutu saboda sun rena su. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da su masu tsarki.
וְשָׁמְרוּ אֶת־מִשְׁמַרְתִּי וְלֹֽא־יִשְׂאוּ עָלָיו חֵטְא וּמֵתוּ בוֹ כִּי יְחַלְּלֻהוּ אֲנִי יְהוָה מְקַדְּשָֽׁם׃
10 “‘Duk wanda ba daga cikin iyalin firistoci ba, ko da yake yana zama tare da su, ko kuwa an ɗauke shi yana yin musu aiki, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun hadayun ba.
וְכָל־זָר לֹא־יֹאכַל קֹדֶשׁ תּוֹשַׁב כֹּהֵן וְשָׂכִיר לֹא־יֹאכַל קֹֽדֶשׁ׃
11 Amma in firist ya sayi bawa da kuɗi, ko kuwa in an haifi bawan a gidansa, wannan bawan zai iya cin tsattsarkan abincin.
וְכֹהֵן כִּֽי־יִקְנֶה נֶפֶשׁ קִנְיַן כַּסְפּוֹ הוּא יֹאכַל בּוֹ וִילִיד בֵּיתוֹ הֵם יֹאכְלוּ בְלַחְמֽוֹ׃
12 In’yar firist ta auri wani da ba firist ba, ba za tă ci wani tsarkakakkun sadaka ba.
וּבַת־כֹּהֵן כִּי תִהְיֶה לְאִישׁ זָר הִוא בִּתְרוּמַת הַקֳּדָשִׁים לֹא תֹאכֵֽל׃
13 Amma idan’yar firist ta zama gwauruwa ko sakakkiya, ba ta da’ya’ya, ta kuwa dawo don tă zauna a gidan mahaifinta kamar matashiya, za tă iya cin abincin.
וּבַת־כֹּהֵן כִּי תִהְיֶה אַלְמָנָה וּגְרוּשָׁה וְזֶרַע אֵין לָהּ וְשָׁבָה אֶל־בֵּית אָבִיהָ כִּנְעוּרֶיהָ מִלֶּחֶם אָבִיהָ תֹּאכֵל וְכָל־זָר לֹא־יֹאכַל בּֽוֹ׃
14 “‘In wani ya ci tsarkakakken abinci cikin kuskure, dole yă maido wa firist hadayar, yă kuma ƙara kashi ɗaya bisa biyar na tamanin abin.
וְאִישׁ כִּֽי־יֹאכַל קֹדֶשׁ בִּשְׁגָגָה וְיָסַף חֲמִֽשִׁיתוֹ עָלָיו וְנָתַן לַכֹּהֵן אֶת־הַקֹּֽדֶשׁ׃
15 Firist ɗin ba zai ƙasƙantar da tsarkakakkun hadayun da Isra’ilawa suka kawo ga Ubangiji
וְלֹא יְחַלְּלוּ אֶת־קָדְשֵׁי בְּנֵי יִשְׂרָאֵל אֵת אֲשֶׁר־יָרִימוּ לַיהוָֽה׃
16 ta wurin barinsu su ci tsarkakakkun hadayu, ta yin haka su jawo wa kansu laifin da zai bukaci biya ba. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.’”
וְהִשִּׂיאוּ אוֹתָם עֲוֺן אַשְׁמָה בְּאָכְלָם אֶת־קָדְשֵׁיהֶם כִּי אֲנִי יְהוָה מְקַדְּשָֽׁם׃
17 Ubangiji ya ce wa Musa,
וַיְדַבֵּר יְהוָה אֶל־מֹשֶׁה לֵּאמֹֽר׃
18 “Yi wa Haruna da’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa magana ka ce musu, ‘In waninku, ko mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a Isra’ila, ya kawo kyauta don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, ko don yă cika alkawari, ko kuwa a matsayin hadaya ta yardar rai,
דַּבֵּר אֶֽל־אַהֲרֹן וְאֶל־בָּנָיו וְאֶל כָּל־בְּנֵי יִשְׂרָאֵל וְאָמַרְתָּ אֲלֵהֶם אִישׁ אִישׁ מִבֵּית יִשְׂרָאֵל וּמִן־הַגֵּר בְּיִשְׂרָאֵל אֲשֶׁר יַקְרִיב קָרְבָּנוֹ לְכָל־נִדְרֵיהֶם וּלְכָל־נִדְבוֹתָם אֲשֶׁר־יַקְרִיבוּ לַיהוָה לְעֹלָֽה׃
19 dole ku miƙa dabba namiji marar lahani, daga shanu, tumaki, ko awaki, domin yă zama yardajje a madadinku.
לִֽרְצֹנְכֶם תָּמִים זָכָר בַּבָּקָר בַּכְּשָׂבִים וּבָֽעִזִּֽים׃
20 Kada ku kawo wani abu mai lahani, domin ba zai zama yardajje ba a madadinku.
כֹּל אֲשֶׁר־בּוֹ מוּם לֹא תַקְרִיבוּ כִּי־לֹא לְרָצוֹן יִהְיֶה לָכֶֽם׃
21 Sa’ad da wani ya kawo hadaya ta salama daga garken shanu, ko na tumaki, ga Ubangiji don yă cika wani alkawari na musamman, ko hadaya ta yardar rai, dole yă zama marar lahani, ko tabo, don yă zama yardajje.
וְאִישׁ כִּֽי־יַקְרִיב זֶֽבַח־שְׁלָמִים לַיהוָה לְפַלֵּא־נֶדֶר אוֹ לִנְדָבָה בַּבָּקָר אוֹ בַצֹּאן תָּמִים יִֽהְיֶה לְרָצוֹן כָּל־מוּם לֹא יִהְיֶה־בּֽוֹ׃
22 Kada ku miƙa wa Ubangiji dabbobi makafi, ko naƙasassu, ko masu gundumi, ko masu ɗiga, ko masu susa, ko masu kirci. Kada ku sa wani daga cikin waɗannan a bisa bagade a matsayin hadaya, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
עַוֶּרֶת אוֹ שָׁבוּר אוֹ־חָרוּץ אֽוֹ־יַבֶּלֶת אוֹ גָרָב אוֹ יַלֶּפֶת לֹא־תַקְרִיבוּ אֵלֶּה לַיהוָה וְאִשֶּׁה לֹא־תִתְּנוּ מֵהֶם עַל־הַמִּזְבֵּחַ לַיהוָֽה׃
23 Za ku iya miƙa hadaya ta yardar rai da maraƙi, ko tunkiya mai naƙasa, ko marar cikakken lafiya, amma ba za tă zama yardajje don cika alkawarin da aka yi ba.
וְשׁוֹר וָשֶׂה שָׂרוּעַ וְקָלוּט נְדָבָה תַּעֲשֶׂה אֹתוֹ וּלְנֵדֶר לֹא יֵרָצֶֽה׃
24 Ba za ku miƙa wa Ubangiji dabbar da lunsayinta yake da ƙujewa, ko dandaƙewa, ko yagewa, ko yankewa ba.
וּמָעוּךְ וְכָתוּת וְנָתוּק וְכָרוּת לֹא תַקְרִיבוּ לַֽיהוָה וּֽבְאַרְצְכֶם לֹא תַעֲשֽׂוּ׃
25 Ba za ku kuma karɓi irin waɗannan dabbobi daga hannun baƙi ku miƙa su a matsayin abinci ga Allahnku ba. Ba za su zama yardajje a madadinku ba, domin sun naƙasa, suna kuma da lahani.’”
וּמִיַּד בֶּן־נֵכָר לֹא תַקְרִיבוּ אֶת־לֶחֶם אֱלֹהֵיכֶם מִכָּל־אֵלֶּה כִּי מָשְׁחָתָם בָּהֶם מוּם בָּם לֹא יֵרָצוּ לָכֶֽם׃
26 Ubangiji ya ce wa Musa,
וַיְדַבֵּר יְהוָה אֶל־מֹשֶׁה לֵּאמֹֽר׃
27 “Sa’ad da aka haifi ɗan maraƙi, tunkiya, ko akuya, sai yă kasance da mahaifiyarsa kwana bakwai. Daga rana ta takwas zuwa gaba, zai zama yardajje hadaya, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
שׁוֹר אוֹ־כֶשֶׂב אוֹ־עֵז כִּי יִוָּלֵד וְהָיָה שִׁבְעַת יָמִים תַּחַת אִמּוֹ וּמִיּוֹם הַשְּׁמִינִי וָהָלְאָה יֵרָצֶה לְקָרְבַּן אִשֶּׁה לַיהוָֽה׃
28 Kada a yanka saniya, ko tunkiya da ɗanta rana ɗaya.
וְשׁוֹר אוֹ־שֶׂה אֹתוֹ וְאֶת־בְּנוֹ לֹא תִשְׁחֲטוּ בְּיוֹם אֶחָֽד׃
29 “Sa’ad da kuka miƙa hadaya ta godiya ga Ubangiji, ku miƙa ta a yadda za tă zama yardajje a madadinku.
וְכִֽי־תִזְבְּחוּ זֶֽבַח־תּוֹדָה לַיהוָה לִֽרְצֹנְכֶם תִּזְבָּֽחוּ׃
30 Dole a ci hadayar a ranar; kada a bar saura sai da safe. Ni ne Ubangiji.
בַּיּוֹם הַהוּא יֵאָכֵל לֹֽא־תוֹתִירוּ מִמֶּנּוּ עַד־בֹּקֶר אֲנִי יְהוָֽה׃
31 “Ku kiyaye dokokina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji.
וּשְׁמַרְתֶּם מִצְוֺתַי וַעֲשִׂיתֶם אֹתָם אֲנִי יְהוָֽה׃
32 Kada ku ƙasƙantar da sunana mai tsarki. Dole Isra’ilawa su gane Ni mai tsarki ne. Ni ne Ubangiji, wanda ya keɓe ku a matsayin tsarkaka
וְלֹא תְחַלְּלוּ אֶת־שֵׁם קָדְשִׁי וְנִקְדַּשְׁתִּי בְּתוֹךְ בְּנֵי יִשְׂרָאֵל אֲנִי יְהוָה מְקַדִּשְׁכֶֽם׃
33 da kuma wanda ya fitar da ku daga Masar don in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji.”
הַמּוֹצִיא אֶתְכֶם מֵאֶרֶץ מִצְרַיִם לִהְיוֹת לָכֶם לֵאלֹהִים אֲנִי יְהוָֽה׃

< Firistoci 22 >