< Firistoci 21 >
1 Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi magana da firistoci,’ya’yan Haruna maza, ka ce musu, ‘Kada firist yă ƙazantar da kansa saboda wani cikin mutanensa da suka mutu,
2 sai dai na danginsa na kusa, kamar mahaifiyarsa ko mahaifinsa, ɗansa ko’yarsa, ɗan’uwansa,
3 ko’yar’uwarsa da ba tă riga ta yi aure ba, wadda take dogara gare shi, da yake ba ta da miji, saboda ita zai iya ƙazantar da kansa.
4 Kada yă ƙazantar da kansa saboda mutanen da suke da dangantakar da shi ta wurin aure, ta yin haka zai ƙazantar da kansa.
5 “‘Kada firistoci su aske kansu ƙwal ko su kwakkwafe gemunsu, ko su tsattsage jikunansu.
6 Dole su kasance masu tsarki ga Allahnsu, kada kuma su ɓata sunan Allahnsu. Domin sukan miƙa hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta, abincin Allahnsu, saboda haka sai su kasance da tsarki.
7 “‘Ba za su auri matan da karuwanci ya ɓata su, ko waɗanda mazansu suka sake su ba, gama firistoci masu tsarki ne ga Allahnsu.
8 An ɗauke su da tsarki, domin suna miƙa abincin Allahnku. An ɗauka su masu tsarki gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, Ni wanda ya mai da ku masu tsarki.
9 “‘In’yar firist ta ɓata kanta ta wurin zama karuwa, ta kunyatar da mahaifinta ke nan; dole a ƙone ta da wuta.
10 “‘Babban firist, wanda yake ɗaya cikin’yan’uwansa wanda aka shafe da mai a kansa, wanda kuma aka naɗa don yă sa rigunan firistoci, kada yă bar gashin kansa buzu-buzu, ko ya kyakketa rigunansa.
11 Ba zai shiga inda akwai gawa ba. Kada yă ƙazantar da kansa, ko ma ta mahaifinsa ce ko ta mahaifiyarsa.
12 An keɓe shi domina, kada yă ƙazantar da kansa, kada kuwa yă ɓata Tentin Sujada ta wurin shiga gidan da gawa take, ko ta mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa ce. Ni ne Ubangiji.
13 “‘Dole macen da zai aura ta kasance budurwa.
14 Ba zai auri matan da mijinta ya mutu, ko macen da mijinta ya rabu da ita, ko macen da ta ɓata kanta ta wurin karuwanci ba, sai dai yă auri budurwa daga cikin mutanensa,
15 don kada yă ƙazantar da’ya’yansa a cikin mutanensa. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da shi mai tsarki.’”
16 Ubangiji ya ce wa Musa,
17 “Faɗa wa Haruna cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, kada ko ɗaya daga cikin zuriyarka, da yake da lahani yă zo kusa domin yă miƙa hadaya ta ci gare ni.
18 Duk mai lahani, ko makaho, ko gurgu, ko mai naƙasa, ko mai wani lahani a jiki;
19 ko mai karyayyen ƙafa, ko mai karyayyen hannu,
20 ko mai ƙusumbi, ko wada, ko wanda yake da lahani a ido, ko mai cuta mai sa ƙaiƙayi, ko mai kirci, ko wanda aka daƙe, ba zai yi kusa domin yă miƙa hadaya ba.
21 Ba zuriyar Haruna firist, mai lahanin da zai zo kusa don yă miƙa hadayun da aka yi ga Ubangiji da wuta. Da yake yana da lahani, ba zai zo kusa don yă miƙa abincin Allahnsa ba.
22 Zai iya cin abinci mafi tsarki na Allahnsa, haka ma abinci mai tsarki;
23 duk da haka saboda lahaninsa, ba zai yi kusa da labule, ko yă yi kusa da bagade don kada yă ƙazantar da wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji wanda yake mai da su masu tsarki.’”
24 Sai Musa ya faɗa wannan wa Haruna da’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa.