< Firistoci 2 >
1 “‘Sa’ad da wani ya kawo hadaya ta gari ga Ubangiji, hadayarsa za tă zama gari mai laushi ne. Zai zuba mai a kai, yă sa turare a kansa
Аще же душа принесет дар жертву Господу, мука пшенична да будет дар его, и да возлиет на ню елей, и возложит на ню ливан: жертва есть:
2 yă kai wa’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci. Firist zai ɗiba gari mai laushin a tafin hannu da kuma man, tare da dukan turaren, yă ƙone wannan a sashen tunawa a kan bagade, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
и да принесет ю к сыном Аароним жерцем, и возмет от нея полну горсть муки пшеничны с елеем и весь ливан ея, и да возложит жрец память ея на олтарь: жертва воня благоухания Господу:
3 Sauran hadaya ta garin zai zama na Haruna da’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta.
и останок от жертвы Аарону и сыном его: святое святых от жертв Господних.
4 “‘In kuka kawo toyayyen hadayar gari da aka yi daga matoya, zai ƙunshi gari mai laushi, toyayye ba tare da yisti ba, gauraye kuma da mai, ko kuwa ƙosai da aka yi ba tare da yisti ba, aka kuma kwaɓa da mai.
Аще же принесет дар жертву печену в пещи от муки пшеничны, хлебы пресны спряжены с елеем и опресноки помазаны елеем.
5 In an toya hadaya ta garinku a kasko, sai a yi shi da gari mai laushi haɗe da mai, ba kuwa da yisti ba.
Аще же жертва от сковрады дар твой, мука пшенична смешена со елеем, пресна да будут:
6 A gutsuttsura shi, a zuba mai a kansa, hadaya ce ta hatsi.
и да разломиши я на укрухи, и возлиеши на на елей: жертва есть Господу.
7 In hadayarku ta hatsin da aka dafa ne a tukunya, sai a yi shi da gari mai laushi da kuma mai.
Аще же жертву от огнища дар твой, мука пшенична с елеем да сотворена будет:
8 A kawo hatsin da aka yi da waɗannan abubuwa ga Ubangiji; a ba wa firist wanda zai ɗauka yă kai bagade.
и принесет жертву, юже аще сотворит от сих Господу, и да принесет к жерцу:
9 Zai fid da sashen tunawa daga hadaya ta gari, yă ƙone shi a kan bagade kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
и приступив ко олтарю, да отимет жрец от жертвы память ея, и да возложит жрец на олтарь: приношение воня благовония Господу:
10 Sauran hadaya ta garin za tă zama ta Haruna da’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayun da aka yi ga Ubangiji ta wuta.
останок же от жертвы Аарону и сыном его: святая святых от приношений Господу.
11 “‘Kowace hadaya ta garin da kuka kawo ga Ubangiji, dole a yi shi ba tare da yisti ba, gama ba za ku ƙone wani yisti, ko zuma a cikin hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta ba.
Всяку жертву, юже аще приносите Господу, не сотворите квасну: всяк бо квас и всяк мед да не принесете от него, еже приносити Господу дар.
12 Za ku iya kawo su ga Ubangiji kamar hadaya ta’ya’yan fari, amma ba za a miƙa su a bagade kamar turare mai ƙanshi ba.
От начатков да принесете я Господу: на олтарь же да не вознесутся в воню благовония Господу.
13 A sa gishiri a dukan hadayunku na hatsi. Kada a rasa sa gishirin alkawari na Allahnku a hadayunku na hatsi, a sa gishiri a dukan hadayunku.
И всяк дар жертвы вашея солию да осолится: да не отставите соли завета Господня от жертв ваших, во всяком даре вашем да принесете Господу Богу вашему соль.
14 “‘In kuka kawo hadaya ta gari na’ya’yan fari ga Ubangiji, sai ku miƙa ɓarzajjen kawunan sabon hatsin da aka gasa a wuta.
Аще же принесеши жертву от начатков жит Господу, новы спряжены зелены класы истлачены Господу, и принесеши жертву от начатков жит:
15 A sa mai da turare a kansa, hadaya ce ta hatsi.
и да возлиеши на ню елей, и да возложиши на ню ливан: жертва есть:
16 Firist zai ƙone sashe na ɓarzajjen hatsin da kuma mai, tare da turare don tunawa, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
и да вознесет жрец память ея от спряженых с елеем, и весь ливан ея: принос есть Господу.