< Firistoci 19 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa,
The Lord told Moses,
2 “Yi wa taron jama’ar Isra’ila gaba ɗaya magana, ka ce musu, ‘Ku zama masu tsarki, domin Ni, Ubangiji Allahnku, mai tsarki ne.
“Tell all the Israelites: You must be holy because I am holy; I am the Lord your God.
3 “‘Dole kowannenku yă girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, dole kuma ku kiyaye Asabbacina. Ni ne Ubangiji Allahnku.
Show respect for your mother and father, and keep my Sabbaths. I am the Lord your God.
4 “‘Kada ku juyo ga gumaka, ko ku yi wa kanku allolin da aka yi zubi da ƙarfe. Ni ne Ubangiji Allahnku.
Don't turn to idols for help or make for metal images of gods. I am the Lord your God.
5 “‘Sa’ad da kuka miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, ku miƙa ta yadda za tă karɓu a madadinku.
When you sacrifice a peace offering to the Lord, make sure you do it correctly so God will accept you.
6 Za a ci ta a ranar da kuka miƙa ta, ko kuwa a kashegarin; duk abin da ya rage har kwana ta uku dole a ƙone shi.
It needs to be eaten the day you sacrifice it, or the next day. Whatever is left over on the third day must be burned.
7 In aka ci ta a rana ta uku, marar tsabta ce, ba kuma za a karɓe ta ba.
If you do eat some of it on the third day, the sacrifice becomes repulsive and won't be accepted.
8 Duk wanda ya ci ta zai zama da laifi domin ya ƙazantar da abin da yake da tsarki ga Ubangiji, dole a raba mutumin nan da mutanensa.
Anyone who eats it eats it will bear responsibility for their guilt, for they have made unclean what is holy to the Lord. They must be expelled from their people.
9 “‘Sa’ad da kuka yi girbin amfanin gonarku, kada ku girbe har zuwa gefen gonar, ko ku yi kalan girbinku.
When you harvest the crops grown on your land, don't harvest right up to the edges of your field, or collect what has been missed.
10 Kada ku koma gonar inabinku kuna kala, ko ku tattara’ya’yan inabin da suka fāffāɗi. Ku bar su domin matalauta da kuma baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.
Don't take every last grape from your vineyard or pick up the ones that have fallen. Leave them for the poor people and foreigners. I am the Lord your God.
11 “‘Kada ku yi sata. “‘Kada ku yi ƙarya. “‘Kada ku ruɗe juna.
Don't steal. Don't lie. Don't deceive each other.
12 “‘Kada ku rantse bisa ƙarya da sunana, ta haka har ku ƙasƙantar da sunan Allahnku. Ni ne Ubangiji.
Don't swear oaths in my name that are not true, otherwise you defame the character of your God. I am the Lord.
13 “‘Kada ku zalunci maƙwabcinku, ko ku yi masa ƙwace. “‘Kada ku riƙe albashin ma’aikaci yă kwana.
Don't cheat others or rob them. Don't refuse to pay wages due to workers until the morning.
14 “‘Kada ku zagi kurma, ko ku sa abin tuntuɓe a gaban makaho, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji.
Don't speak badly about deaf people. Don't put objects in the way of blind people to trip them up. Instead show respect to your God. I am the Lord.
15 “‘Kada ku yi rashin adalci cikin shari’a; kada ku nuna sonkai ga matalauci, ko ku goyi bayan mai arziki, amma ku shari’anta maƙwabci cikin gaskiya.
Don't be a corrupt judge. Don't show favoritism to the poor or to the rich. Judge others fairly.
16 “‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku. “‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji.
Don't go around spreading false rumors about people. Don't keep quiet when the lives of others are at risk. I am the Lord.
17 “‘Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa.
Don't hold onto hateful feelings towards others. Talk honestly with your neighbors, so that you don't sin because of them.
18 “‘Kada ka nemi yin ramuwa, ko ka riƙe wani cikin mutanenka a zuciya, amma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Ubangiji.
Don't look for revenge or hold a grudge against anybody, but love your neighbor as yourself. I am the Lord.
19 “‘Ku kiyaye farillaina. “‘Kada ku sa dabbobin da ba iri ɗaya ba su yi barbara. “‘Kada ku yi shuki iri biyu a gonarku. “‘Kada ku sa rigar da aka saƙa da yadi iri biyu.
Do what I tell you! Don't make different kinds of livestock breed together. Don't sow your fields with two different kinds of seed. Don't wear clothes made of two different kinds of material.
20 “‘In wani ya kwana da mace wadda take baiwa, wadda aka yi wa wani alkawari amma bai fanshe ta ba, ko kuwa ba a’yantar da ita ba, dole a yi hukuncin da ya dace. Duk da haka ba za a kashe su ba, domin ba a’yantar da ita ba.
If a man has sex with a servant girl promised to become another man's wife, but who hasn't yet been bought or set free, then compensation has to be paid. However, they are not to be killed, because she hadn't been set free.
21 Dole mutumin da ya kwana da ita yă kawo rago a ƙofar Tentin Sujada domin hadaya don laifi ga Ubangiji.
But the man must bring a ram as his guilt offering to the Lord at the entrance of the Tent of Meeting.
22 Da ragon hadaya don laifin ne firist zai yi kafara saboda mutumin a gaban Ubangiji saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta zunubinsa.
The priest will set things right for him before the Lord using the ram of the guilt offering for the sin he has committed, and his sin will be forgiven.
23 “‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar kuka kuma shuka kowane irin itace mai’ya’ya na ci, ku ɗauki’ya’yan itatuwan nan a matsayi an hana ku ci. Shekara uku za ku ɗauka a matsayi an hana ku, ba za ku ci su ba.
When you enter the land and plant any kind of fruit tree, treat the fruit at first as unclean. For three years you are forbidden to eat it.
24 A shekara ta huɗu, dukan’ya’yansu za su zama tsarkakakku, hadaya ta yabo ga Ubangiji.
The fourth year all the fruit must be dedicated to the Lord as a praise offering.
25 Amma a shekara ta biyar, za ku iya cin’ya’yan itatuwan. Ta haka girbinku zai ƙaru. Ni ne Ubangiji Allahnku.
However, the fifth year you may eat the fruit and in this way you will have an even greater harvest. I am the Lord your God.
26 “‘Kada ku ci wani abinci tare da jini a cikinsa. “‘Kada ku yi duba ko sihiri.
Don't eat meat with blood in it. Don't use fortune-telling or witchcraft.
27 “‘Ba za ka aske gefe-gefe na gashin kanka ba, ko ku aske gemunku.
Don't cut your hair on the sides of your head or trim the sides of your beard,
28 “‘Kada ku tsattsaga jikunanku saboda matattu, ba kuwa za ku yi wa kanku zāne-zāne a jiki ba. Ni ne Ubangiji.
don't cut your bodies in some pagan ritual for the dead, and don't get yourselves tattoos. I am the Lord.
29 “‘Kada ka ƙasƙantar da’yarka ta wurin mai da ita karuwa, in ba haka ba ƙasar za tă juya ga karuwanci tă kuma cika da mugunta.
Don't bring shame on your daughter by making her a prostitute, otherwise the land will become morally and spiritually depraved.
30 “‘Ku kiyaye Asabbacina, ku kuma girmama wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji.
Keep my Sabbaths and show respect for my sanctuary. I am the Lord.
31 “‘Kada ku juya ga masu duba, ko ku nemi shawarar bokaye, gama za ku ƙazantu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji Allahnku.
Don't try and find help from mediums or spiritists—don't even go looking for them, otherwise they will corrupt you. I am the Lord your God.
32 “‘Ku miƙe tsaye a gaban tsofaffi, ku nuna bangirma ga waɗanda suka tsufa, ku kuma girmama Allahnku. Ni ne Ubangiji.
Stand up and be respectful of older people. Show reverence for your God. I am the Lord.
33 “‘Sa’ad da baƙo yana zama tare da ku a ƙasarku, kada ku wulaƙanta shi.
Don't mistreat foreigners who live in your country.
34 Dole ku ɗauki baƙon da yake zama tare da ku kamar haifaffe ɗan ƙasa. Ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.
Treat them in the same way as a fellow citizen, and love them as you love yourself, because you were once foreigners living in Egypt. I am the Lord your God.
35 “‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu.
Don't use dishonest weights and measures.
36 Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar.
Make sure your scales and weights are accurate, that your measures of ephah and hin are correct. I am the Lord your God who led you out of Egypt.
37 “‘Ku kiyaye dukan farillaina da kuma dukan dokokina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji.’”
Keep all my rules and regulations, and make sure you follow them. I am the Lord.”

< Firistoci 19 >