< Firistoci 18 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa,
Locutus est Dominus ad Moysen, dicens:
2 “Yi wa Isra’ilawa magana ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku.
Loquere filiis Israel, et dices ad eos: Ego Dominus Deus vester:
3 Kada ku yi yadda suke yi a Masar inda da kuke zama, kuma ba a ku yi kamar yadda suke yi a ƙasar Kan’ana inda nake kawo ku ba. Kada ku yi yadda suke yin abubuwa.
iuxta consuetudinem Terræ Ægypti, in qua habitastis, non facietis: et iuxta morem Regionis Chanaan, ad quam ego introducturus sum vos, non agetis, nec in legitimis eorum ambulabitis.
4 Dole ku kiyaye dokokina kuma ku lura ku bi farillaina. Ni ne Ubangiji Allahnku.
Facietis iudicia mea, et præcepta mea servabitis, et ambulabitis in eis. Ego Dominus Deus vester.
5 Ku kiyaye farillaina da dokokina, gama mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji.
Custodite leges meas atque iudicia, quæ faciens homo, vivet in eis. Ego Dominus.
6 “‘Kada wani ya kusaci wani dangi na kusa don yă yi jima’i. Ni ne Ubangiji.
Omnis homo ad proximam sanguinis sui non accedet, ut revelet turpitudinem eius. Ego Dominus.
7 “‘Kada ka ƙasƙantar da mahaifinka ta wurin kwana da mahaifiyarka. Ita mahaifiyarka ce; kada ka yi jima’i da ita.
Turpitudinem patris tui et turpitudinem matris tuæ non discooperies: mater tua est, non revelabis turpitudinem eius.
8 “‘Kada ka yi jima’i da matar mahaifinka, wannan zai ƙasƙantar da mahaifinka.
Turpitudinem uxoris patris tui non discooperies: turpitudo enim patris tui est.
9 “‘Kada ka yi jima’i da’yar’uwarka, ko’yar mahaifinka ko’yar mahaifiyarka, ko an haife ta a gida ɗaya da kai ko kuwa a wani wuri dabam.
Turpitudinem sororis tuæ ex patre, sive ex matre, quæ domi vel foris genita est, non revelabis.
10 “‘Kada ka yi jima’i da’yar ɗanka ko’yar’yarka, wannan zai ƙasƙantar da kai.
Turpitudinem filiæ filii tui vel neptis ex filia non revelabis: quia turpitudo tua est.
11 “‘Kada ka yi jima’i da’yar matar mahaifinka wadda aka haifa wa mahaifinka; ita’yar’uwarka ce.
Turpitudinem filiæ uxoris patris tui, quam peperit patri tuo, et est soror tua, non revelabis.
12 “‘Kada ka yi jima’i da’yar’uwar mahaifinka, ita dangin mahaifinka ne na kusa.
Turpitudinem sororis patris tui non discooperies: quia caro est patris tui.
13 “‘Kada ka yi jima’i da’yar’uwar mahaifiyarka, domin ita dangin mahaifiyarka ce na kusa.
Turpitudinem sororis matris tuæ non revelabis, eo quod caro sit matris tuæ.
14 “‘Kada ka ƙasƙantar da ɗan’uwan mahaifinka ta wurin kusaci matarsa don ka yi jima’i da ita, ita bābarka ce.
Turpitudinem patrui tui non revelabis, nec accedes ad uxorem eius, quæ tibi affinitate coniungitur.
15 “‘Kada ka yi jima’i da matar ɗanka. Ita matar ɗanka ne; kada ka yi jima’i da ita.
Turpitudinem nurus tuæ non revelabis, quia uxor filii tui est, nec discooperies ignominiam eius.
16 “‘Kada ka yi jima’i da matar ɗan’uwanka; wannan zai ƙasƙanta ɗan’uwanka.
Turpitudinem uxoris fratris tui non revelabis: quia turpitudo fratris tui est.
17 “‘Kada ka yi jima’i da mace da kuma’yarta. Kada ka yi jima’i da’yar ɗanta ko’yar’yarta; su danginta ne na kusa. Wannan mugun abu ne.
Turpitudinem uxoris tuæ et filiæ eius non revelabis. Filiam filii eius, et filiam filiæ illius non sumes, ut reveles ignominiam eius: quia caro illius sunt, et talis coitus incestus est.
18 “‘Kada ka auri’yar’uwar matarka ta zama kishiyar matarka ka kuma yi jima’i da ita yayinda matarka tana da rai.
Sororem uxoris tuæ in pellicatum illius non accipies, nec revelabis turpitudinem eius adhuc illa vivente.
19 “‘Kada ka kusaci mace don ka yi jima’i da ita a lokacin ƙazantar al’adarta.
Ad mulierem, quæ patitur menstrua, non accedes, nec revelabis fœditatem eius.
20 “‘Kada ka yi jima’i da matar maƙwabcinka ka ƙazantar da kanka tare da ita.
Cum uxore proximi tui non coibis, nec seminis commistione maculaberis.
21 “‘Kada ku ba da wani daga cikin’ya’yanku don a yi hadaya wa Molek, gama ba za ku ƙasƙantar da sunan Allahnku ba. Ni ne Ubangiji.
De semine tuo non dabis ut consecretur idolo Moloch, nec pollues nomen Dei tui. Ego Dominus.
22 “‘Kada ka kwana da namiji kamar yadda namiji yakan kwana da ta mace, wannan abin ƙyama ne.
Cum masculo non commiscearis coitu femineo, quia abominatio est.
23 “‘Kada ka yi jima’i da dabba ka ƙazantar da kanka. Mace ba za tă ba da kanta ga dabba don yă yi jima’i da ita ba; wannan abin ƙyama ne.
Cum omni pecore non coibis, nec maculaberis cum eo. Mulier non succumbet iumento, nec miscebitur ei: quia scelus est.
24 “‘Kada ku ƙazantar da kanku da wani daga cikin waɗannan, domin haka al’umman da zan kora a gabanku suka ƙazantu.
Nec polluamini in omnibus his, quibus contaminatæ sunt universæ gentes, quas ego eiiciam ante conspectum vestrum,
25 Har ƙasar ma ta ƙazantu, saboda haka na hukunta ta saboda zunubinta, ƙasar kuwa ta amayar da mazaunanta.
et quibus polluta est terra: cuius ego scelera visitabo, ut evomat habitatores suos.
26 Amma dole ku kiyaye farillaina da kuma dokokina. Kada haifaffe ɗan ƙasa da baƙin da suke zama a cikinku yă yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama,
Custodite legitima mea atque iudicia, et non faciatis ex omnibus abominationibus istis, tam indigena quam colonus qui peregrinantur apud vos.
27 gama mutanen da suka zauna a wannan ƙasa kafin ku sun aikata dukan waɗannan abubuwa, suka kuma ƙazantu.
Omnes enim execrationes istas fecerunt accolæ terræ qui fuerunt ante vos, et polluerunt eam.
28 Kuma in kuka ƙazantar da ƙasar, za tă amayar da ku kamar yadda ta amayar da al’umman da suka riga ku.
Cavete ergo ne et vos similiter evomat, cum paria feceritis, sicut evomuit gentem, quæ fuit ante vos.
29 “‘Duk wanda ya yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama, dole a fid da mutumin daga cikin mutanensa.
Omnis anima, quæ fecerit de abominationibus his quippiam, peribit de medio populi sui.
30 Ku kiyaye umarnaina kuma kada yi ku wata al’ada mai banƙyamar da aka yi kafin ku zo kuma kada ku ƙazantar da kanku da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.’”
Custodite mandata mea. Nolite facere quæ fecerunt hi qui fuerunt ante vos, et ne polluamini in eis. Ego Dominus Deus vester.

< Firistoci 18 >