< Firistoci 17 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa,
The Lord told Moses,
2 “Yi magana da Haruna da’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji ya umarta.
“Tell Aaron, his sons, and all the Israelites that this is what the Lord commands:
3 Duk mutumin Isra’ilan da ya yanka sa, ɗan rago ko akuya a sansani ko waje da shi
Any Israelite who kills a bull, a lamb, or a goat, whether inside the camp or outside of it,
4 a maimakon kawo shi a matsayin hadaya ga Ubangiji a gaban tabanakul na Ubangiji, za a ɗauki wannan mutum a matsayi mai laifin zub da jini, ya zub da jini, kuma dole a raba shi da mutanensa.
instead of bringing it to the entrance to the Tent of Meeting to present it as an offering to the Lord there, that person shall be held guilty of illegal killing. They have shed blood and must be expelled from their people.
5 Wannan ya zama haka saboda Isra’ilawa su kawo wa Ubangiji hadayun da suke yi a filaye. Dole su kawo su ga firist, wato, ga Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, su miƙa su a matsayin hadayun salama.
This is why the Israelites have to bring to the Lord the sacrifices they currently offer out in the fields. They must bring them to the priest at the entrance to the Tent of Meeting and offer them as peace offerings to the Lord.
6 Firist zai yayyafa jinin a bagaden Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, yă kuma ƙone kitsen kamar ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.
The priest will sprinkle the blood on the altar of the Lord at the entrance to the Tent of Meeting, and burn the fat to be accepted by the Lord.
7 Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare su wa tsararraki masu zuwa.’
They must not continue to offer their sacrifices to the goat devils with whom they have acted like prostitutes. This is a regulation for all time and for all future generations.
8 “Faɗa musu, ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko wani baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ko sadaka
Warn them that any Israelite or any foreigner living among them who offers a burnt offering or a sacrifice
9 kuma bai kawo shi a ƙofar Tentin Sujada don yă miƙa shi ga Ubangiji ba, dole a raba wannan mutum da mutanensa.
without bringing it to the entrance to the Tent of Meeting to sacrifice it to the Lord must be expelled from their people.
10 “‘Duk mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya ci wani jini, zan yi gāba da wannan mutum wanda ya ci jinin, za a kuma raba shi da mutanensa.
I will disown any Israelite or any foreigner living among them who eats any blood and I will expel them from their people.
11 Gama ran halitta yana a cikin jinin, kuma na ba da shi gare ku don kafara a kan bagade, jini ne yake kafara saboda ran mutum.
Life is in the body's blood. I have given it to you so that by putting it on the altar your lives can be made right, for it is the lifeblood that makes people's lives right.
12 Saboda haka na ce wa Isra’ilawa, “Babu waninku da zai ci jini, babu wani baƙon da yake zama a cikinku da zai ci jini.”
That's why I'm warning the Israelites: None of you is allowed to eat blood, and no foreigner living among you is allowed to eat blood.
13 “‘Duk wani mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinku wanda ya ji wa wani dabba ko tsuntsu wanda ake ci ciwo, dole yă tsiyaye jinin yă rufe shi da ƙasa,
Any Israelite or foreigner living among them who hunts and kills a wild animal or a bird which are allowed be eaten must drain the blood from its body and cover it with earth,
14 domin ran kowace halitta yana cikin jini. Shi ya sa na ce wa Isra’ilawa, “Kada ku ci jinin wani halitta, domin ran kowace halitta yana cikin jinin; duk wanda ya ci shi dole a fid da shi.”
for life is in the body's blood. That's why I have warned the Israelites: You are not allowed to eat the blood of anything living, for life is in the body's blood. Anyone who eats it must be expelled.
15 “‘Kowa, ko haifaffe ɗan ƙasa ko baƙo, da ya ci wani abin da aka sami a mace, ko naman jeji ya yayyage, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma; sa’an nan zai tsarkake.
Anyone, Israelite or foreigner, who eats anything found dead or killed by wild animals must wash their clothes and wash with water, and they will be unclean until the evening. Then they will be clean.
16 Amma in bai wanke rigunansa ya kuma yi wanka ba, alhaki zai kasance a kansa.’”
But if they don't wash their clothes and wash themselves with water, then they bear responsibility for their guilt.”

< Firistoci 17 >