< Firistoci 11 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
The Lord told Moses and Aaron,
2 “Ku ce wa Isra’ilawa, ‘Cikin dabbobin da suke a doron ƙasa, waɗannan ne za ku ci.
“Give these instructions to the Israelites. These are the animals you are allowed to eat:
3 Za ku iya cin dabbobin da suke da rababben kofato, waɗanda suke kuma tuƙa.
any animal that both has a divided hoof and also chews the cud.
4 “‘Akwai waɗanda suke tuƙa ko kuwa suna da rababben kofato kawai, duk da haka ba za ku ci su ba. Waɗannan kuwa su ne, raƙumi, ko da yake yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato; saboda haka cin namansa haram ne gare ku.
However, if it either chews the cud, or has a divided hoof, then you may not eat it. These include: the camel, which though it chews the cud doesn't have a divided hoof, so it is unclean for you.
5 Rema, ko da yake tana tuƙa, duk da haka ba ta da rababben kofato; saboda haka namanta haram ne gare ku.
The rock hyrax, which though it chews the cud doesn't have a divided hoof, so it is unclean for you.
6 Zomo, ko da yake yana tuƙa, duk da haka ba shi da rababben kofato; saboda haka namansa haram ne gare ku.
The hare, which though it chews the cud doesn't have a divided hoof, so it is unclean for you.
7 Alade, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa, saboda haka namansa haram ne gare ku.
The pig, which though it has a divided hoof doesn't chew the cud, so it is unclean for you.
8 Ba za ku ci namansu ba, ko ku taɓa gawawwakinsu, gama haram ne gare ku.
You are not to eat their meat or touch their bead bodies. They are unclean for you.
9 “‘Cikin dukan halittu masu rai da suke a cikin ruwan tekuna da rafuffuka, za ku iya cin kowane da yake da ƙege da kamɓori.
You are allowed to eat any creature with fins and scales that lives in the water, whether in the sea or in fresh water.
10 Amma kowace halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, ko cikin dukan abubuwa masu rai a ruwa ko kuma sauran halittu a cikin ruwa za ku ɗauka su marasa tsaki ne gare ku.
But you are not allowed to eat any of the many creatures that don't have fins and scales that live in the water, whether in the sea or in fresh water.
11 Da yake abubuwan ƙyama ne a gare ku, ba za ku ci namansu ba, kuma dole ku yi ƙyamar gawawwakinsu.
They are repulsive. You must not eat their meat, and you must treat their dead bodies as repulsive.
12 Duk abin da yake a ruwa amma ba shi da ƙege ko kamɓori, za ku yi ƙyamarsa.
All such water creatures that don't have fins and scales are to be repulsive to you.
13 “‘Waɗannan su ne tsuntsayen da za ku yi ƙyamarsu, ba za ku ci su ba domin sun zama abin ƙyama. Tsuntsayen kuwa su ne, gaggafa, ungulu, baƙin ungulu,
As for the birds, these must not be eaten because they are repulsive: eagle, griffon vulture, bearded vulture,
14 shirwa, da duk wani irin baƙin shirwa,
buzzard, kite and similar birds of prey,
15 kowane irin hankaka,
any raven or crow,
16 mujiya mai ƙaho, jimina, shaho, da kowane irin shaho,
tawny owl, long-eared owl, gulls, any kind of hawk,
17 ƙaramin ƙururu, babba da jaka, zalɓe,
little owl, fish owl, eagle owl,
18 kazar ruwa, kwasakwasa, da ungulu,
barn owl, desert owl, Egyptian vulture,
19 shamuwa, kowane irin jinjimi, katutu da kuma jamage.
storks and any kind of heron, hoopoe, and bats.
20 “‘Dukan ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu abin ƙyama ne gare ku.
All flying insects that crawl are repulsive to you.
21 Sai dai akwai ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu da za ku ci; waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle.
But you can eat the following kinds of flying insects that crawl: those that have jointed legs they use to jump.
22 Za ku iya cin kowane irin fāra, gyare, ƙwanso da danginsu.
So in this category you can eat any kind of locust, bald locust, cricket, or grasshopper.
23 Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, suna kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku.
All other flying insects that crawl are repulsive to you,
24 “‘Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har fāɗuwar rana.
and will make you unclean. If you touch their dead bodies you will be unclean until the evening,
25 Duk wanda ya ɗauki ɗaya daga cikin gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har zuwa yamma.
and if you pick up one of their dead bodies you must wash your clothes, and you will be unclean until the evening.
26 “‘Kowace dabbar da ba ta da rababben kofato ko ba ta tuƙa, haram ce gare ku; duk wanda ya taɓa gawarsu zai ƙazantu.
Every animal with hooves that are not divided, or that does not chew the cud, is unclean for you. If you touch any of them you will be unclean.
27 Duk abin da yake tafiya a kan dāginsa cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa yamma.
Any four-legged animal that walks on its paws are unclean for you. If you touch their dead bodies you will be unclean until the evening,
28 Duk wanda ya ɗauki gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har yamma. Waɗannan dabbobi za su zama marasa tsabta a gare ku.
and if you pick up one of their dead bodies you must wash your clothes, and you will be unclean until the evening. They are unclean for you.
29 “‘Waɗannan ƙananan dabbobi da suke rarrafe a ƙasa, haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa,
The following animals that run along the ground are unclean for you: rats, mice, any kind of large lizard,
30 da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo.
gecko, monitor lizard, wall lizard, skinks, and chameleon.
31 Dukan waɗanda suke rarrafe, za su zama marasa tsarki gare ku. Duk wanda ya taɓa su sa’ad da suka mutu, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma.
These animals that run along the ground are unclean for you. If you touch a dead one of them you will be unclean until the evening.
32 Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai, zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma, sa’an nan zai tsarkaka.
Anything that one of them dies and lands on becomes unclean. Whatever it is—something made of wood, clothing, leather, sackcloth, or any work tool—it must be washed with water and will be unclean until the evening. Then it will become clean.
33 In waninsu ya fāɗi a cikin tukunyar laka, kome da yake a tukunyar zai ƙazantu, kuma dole a fashe tukunyar.
If one of them falls into a clay pot, all that's in it becomes unclean. You must smash the pot.
34 Duk abincin da aka yarda a ci, wanda ya taɓa ruwa daga irin tukunyan nan zai zama marar tsabta, kuma duk ruwan da za a sha daga irin tukunyan nan ƙazantacce ne.
If water from that pot touches any food, that food becomes unclean, and any drink from a pot like that also becomes unclean.
35 Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai ya ƙazantu ke nan; ko a kan murhu, ko a tukunyar dahuwa, dole a farfashe su. Su haramtattu ne kuma dole ku ɗauke su haramtattu.
Anything that one of their dead bodies falls on becomes unclean. If it's an oven or a stove, it must be smashed. It is permanently unclean for you.
36 Maɓuɓɓuga ko tafki na tarin ruwa zai ci gaba da zauna mai tsabta, amma duk wanda ya taɓa ɗaya daga cikin waɗannan gawawwakin ya haramtu.
On the other hand, if it's a spring or cistern containing water then it will remain clean, but if you touch one of these dead bodies in it you will be unclean.
37 In gawa ta fāɗi a irin da za a shuka, irin zai ci gaba da zama mai tsabta.
Similarly, if one of their dead bodies falls on any seed used for sowing, the seed remains clean;
38 Amma in an sa ruwa a irin sai kuma gawar ta fāɗi a kai, to, irin ya zama haram gare ku.
but if the seed has been soaked in water and one of their dead bodies falls on it, it is unclean for you.
39 “‘In dabbar aka yarda a ci ta mutu, duk wanda ya taɓa gawarta zai ƙazantu har yamma.
If an animal that you are allowed to eat dies, anyone who touches the dead body will be unclean until the evening.
40 Duk wanda ya ci wani sashe na gawar dole yă wanke rigunansa, kuma zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ɗauki gawar dole yă wanke rigunansa, zai kuwa ƙazantu har yamma.
If you eat anything from the dead body you must wash your clothes and you will be unclean until the evening. If you pick up the dead body you must wash your clothes and you will be unclean until the evening.
41 “‘Duk dabba mai rarrafe a ƙasa abin ƙyama ne; ba kuwa za a ci shi ba.
Every animal that crawls along the ground is repulsive—you must not eat it.
42 Ba za ku ci wani halittar da take rarrafe a ƙasa, ko tana jan ciki, ko tana tafiya a kan ƙafafu huɗu, ko a kan ƙafafu da yawa ba; abin ƙyama ne.
Don't eat any animal that crawls along the ground, whether it moves on its belly or walks on four feet or many feet. All such animals are repulsive.
43 Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani daga waɗannan halittu. Kada ku ƙazantar da kanku ta dalilinsu, ko a mai da ku haramtattu ta wurinsu.
Don't defile yourselves by any such crawling animal. Don't make yourselves unclean or defiled by them,
44 Ni ne Ubangiji Allahnku; ku tsarkake kanku ku kuma zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani halittar da take rarrafe a ƙasa.
because I am the Lord your God; so dedicate yourselves and be holy, because I am holy. Don't defile yourselves by any animal that crawls along the ground.
45 Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da ku daga Masar don in zama Allahnku; saboda haka ku zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne.
I am the Lord who led you out of Egypt so that I could be your God. So be holy, because I am holy.
46 “‘Waɗannan ne ƙa’idodi game da dabbobi, tsuntsaye, da kowane abu mai rai da yake motsi a cikin ruwa, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa.
These are the regulations about animals, birds, everything that lives in the water, and all animals that crawl along the ground.
47 Dole ku bambanta tsakanin haramtacce da halaltacce, tsakanin halittu masu ran da za a iya ci da waɗanda ba za a iya ci ba.’”
You must recognize the difference between unclean and clean, between those animals that can be eaten and those that can't.”

< Firistoci 11 >