< Firistoci 10 >

1 ’Ya’yan Haruna maza, Nadab da Abihu suka ɗauki farantansu, suka sa wuta a ciki, suka zuba turare a kai; suka kuma miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba.
ויקחו בני אהרן נדב ואביהוא איש מחתתו ויתנו בהן אש וישימו עליה קטרת ויקריבו לפני יהוה אש זרה--אשר לא צוה אתם
2 Sai wuta ta fito daga Ubangiji ta cinye su, suka kuma mutu a gaban Ubangiji.
ותצא אש מלפני יהוה ותאכל אותם וימתו לפני יהוה
3 Sai Musa ya ce Haruna, “Ga abin da Ubangiji yake nufi sa’ad da ya ce, “‘A cikin waɗanda suka kusace ni za a tabbata ni mai tsarki ne; a fuskar dukan mutane za a kuwa girmama ni.’” Haruna ya yi shiru.
ויאמר משה אל אהרן הוא אשר דבר יהוה לאמר בקרבי אקדש ועל פני כל העם אכבד וידם אהרן
4 Sai Musa ya kira Mishayel da Elzafan,’ya’yan Uzziyel kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan; ku ɗauki’yan’uwanku waje da sansani, daga gaban wuri mai tsarki.”
ויקרא משה אל מישאל ואל אלצפן בני עזיאל דד אהרן ויאמר אלהם קרבו שאו את אחיכם מאת פני הקדש אל מחוץ למחנה
5 Sai suka zo suka ɗauke su, suna nan cikin taguwoyinsu, zuwa waje da sansani yadda Musa ya umarta.
ויקרבו וישאם בכתנתם אל מחוץ למחנה--כאשר דבר משה
6 Sa’an nan Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar’ya’yansa maza, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku yage tufafinku, don kada ku mutu. Yin haka zai jawo fushin Ubangiji a kan dukan jama’a. Amma dangoginku, wato, dukan Isra’ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya hallaka da wuta.
ויאמר משה אל אהרן ולאלעזר ולאיתמר בניו ראשיכם אל תפרעו ובגדיכם לא תפרמו ולא תמתו ועל כל העדה יקצף ואחיכם כל בית ישראל--יבכו את השרפה אשר שרף יהוה
7 Kada ku bar ƙofar Tentin Sujada ko kuwa ku mutu, domin man Shafan Ubangiji yana kanku.” Saboda haka suka yi kamar yadda Musa ya faɗa.
ומפתח אהל מועד לא תצאו פן תמתו--כי שמן משחת יהוה עליכם ויעשו כדבר משה
8 Sa’an nan Ubangiji ya yi magana da Haruna ya ce,
וידבר יהוה אל אהרן לאמר
9 “Kai da’ya’yanka maza, ba za ku sha ruwan inabi ko wani abu mai sa jiri ba a duk sa’ad da za ku shiga cikin Tentin Sujada, in ba haka ba za ku mutu. Wannan dawwammamiyar farilla ce wa tsararraki masu zuwa.
יין ושכר אל תשת אתה ובניך אתך בבאכם אל אהל מועד--ולא תמתו חקת עולם לדרתיכם
10 Dole ku bambanta tsakanin mai tsarki da marar tsarki, tsakanin marar tsabta da mai tsabta,
ולהבדיל בין הקדש ובין החל ובין הטמא ובין הטהור
11 za ku kuma koyar da Isra’ilawa dukan farillan da Ubangiji ya ba su ta wurin Musa.”
ולהורת את בני ישראל--את כל החקים אשר דבר יהוה אליהם ביד משה
12 Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar’ya’yansa maza da suka ragu, “Ku ɗauki ragowar hadaya ta gari wadda aka yi hadaya ta ƙonawa da ita ga Ubangiji ku ci ba tare da yisti ba, a gefen bagaden, gama tsattsarka ne.
וידבר משה אל אהרן ואל אלעזר ואל איתמר בניו הנותרים קחו את המנחה הנותרת מאשי יהוה ואכלוה מצות אצל המזבח כי קדש קדשים הוא
13 Ku ci shi a tsattsarkan wuri, gama rabonka ne da na’ya’yanka daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji; gama haka aka umarce ni.
ואכלתם אתה במקום קדוש כי חקך וחק בניך הוא מאשי יהוה כי כן צויתי
14 Amma kai da’ya’yanka maza da mata za su iya ci ƙirjin da aka kaɗa, da kuma cinyar da aka miƙa. Ku ci su a wuri mai tsabta; an ba da su gare ku da kuma’ya’yanku a matsayin rabo daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa.
ואת חזה התנופה ואת שוק התרומה תאכלו במקום טהור--אתה ובניך ובנתיך אתך כי חקך וחק בניך נתנו מזבחי שלמי בני ישראל
15 Cinyar da aka miƙa da kuma ƙirjin da aka kaɗa, dole a kawo su tare da ɓangarori kitsen hadayun da aka yi ta wuri wuta, don a kaɗa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Wannan zai zama na kullayaumi gare ka da’ya’yanka, yadda Ubangiji ya umarta.”
שוק התרומה וחזה התנופה על אשי החלבים יביאו להניף תנופה לפני יהוה והיה לך ולבניך אתך לחק עולם כאשר צוה יהוה
16 Sa’ad da Musa ya nemi sani game da akuyar hadaya don zunubi, ya kuwa gane cewa an ƙone shi, sai ya yi fushi da Eleyazar da kuma Itamar,’ya’yan Haruna maza da suka ragu, ya kuma yi tambaya,
ואת שעיר החטאת דרש דרש משה--והנה שרף ויקצף על אלעזר ועל איתמר בני אהרן הנותרם לאמר
17 “Me ya sa ba ku ci hadaya don zunubi a cikin wuri mai tsarki ba? Mafi tsaki ne; an ba ku ne don a ɗauke laifin jama’a ta wurin yin kafara saboda su a gaban Ubangiji.
מדוע לא אכלתם את החטאת במקום הקדש--כי קדש קדשים הוא ואתה נתן לכם לשאת את עון העדה לכפר עליהם לפני יהוה
18 Da yake ba a kai jininsa cikin wuri mai tsarki ba, ya kamata ku ci akuyar a wuri mai tsarki, kamar yadda na umarta.”
הן לא הובא את דמה אל הקדש פנימה אכול תאכלו אתה בקדש כאשר צויתי
19 Sai Haruna ya amsa wa Musa, “Yau sun miƙa hadayarsu don zunubi da kuma hadayarsu ta ƙonawa a gaban Ubangiji, ga kuma irin waɗannan abubuwa da suka same ni, da a ce na ci hadaya don zunubi yau, da zai yi kyau ke nan a gaban Ubangiji?”
וידבר אהרן אל משה הן היום הקריבו את חטאתם ואת עלתם לפני יהוה ותקראנה אתי כאלה ואכלתי חטאת היום הייטב בעיני יהוה
20 Da Musa ya ji haka, sai ya gamsu.
וישמע משה וייטב בעיניו

< Firistoci 10 >