< Makoki 5 >

1 Ka tuna, ya Ubangiji, abin da ya faru da mu; duba, ka ga kunyar da muka sha.
זכר יהוה מה היה לנו הביט (הביטה) וראה את חרפתנו
2 An ba wa baƙi gādonmu, gidajenmu kuma aka ba bare.
נחלתנו נהפכה לזרים בתינו לנכרים
3 Mun zama marayu marasa ubanni, uwayenmu kamar gwauraye.
יתומים היינו אין (ואין) אב אמתינו כאלמנות
4 Dole mu sayi ruwan da muke sha; sai mun biya mu sami itace.
מימינו בכסף שתינו עצינו במחיר יבאו
5 Masu fafararmu sun kusa kama mu; mun gaji kuma ba dama mu huta.
על צוארנו נרדפנו יגענו לא (ולא) הונח לנו
6 Mun miƙa kanmu ga Masar da Assuriya don mu sami isashen abinci.
מצרים נתנו יד אשור לשבע לחם
7 Kakanninmu sun yi zunubi kuma ba sa nan yanzu, mu ne aka bari muna shan hukuncinsu.
אבתינו חטאו אינם (ואינם) אנחנו (ואנחנו) עונתיהם סבלנו
8 Bayi suna mulki a kanmu, kuma ba wanda zai’yantar da mu daga hannuwansu.
עבדים משלו בנו פרק אין מידם
9 Muna samun burodi a bakin rayukanmu domin takobin da yake a jeji.
בנפשנו נביא לחמנו מפני חרב המדבר
10 Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu, muna jin zazzaɓi domin yunwa.
עורנו כתנור נכמרו מפני זלעפות רעב
11 An yi wa mata fyaɗe a cikin Sihiyona, da kuma budurwai a cikin garuruwan Yahuda.
נשים בציון ענו בתלת בערי יהודה
12 An rataye’ya’yan sarakuna da hannuwansu; ba a ba wa dattawa girma.
שרים בידם נתלו פני זקנים לא נהדרו
13 Samari suna faman yin niƙa; yara kuma suna fama da ƙyar da nauyin kayan itace.
בחורים טחון נשאו ונערים בעץ כשלו
14 Dattawan sun bar ƙofar birnin, samari sun daina rera waƙa.
זקנים משער שבתו בחורים מנגינתם
15 Farin ciki ya rabu da zuciyarmu; rayuwarmu ta zama makoki.
שבת משוש לבנו נהפך לאבל מחלנו
16 Rawani ya fāɗi daga kanmu. Kaiton mu gama mun yi zunubi!
נפלה עטרת ראשנו אוי נא לנו כי חטאנו
17 Domin wannan zuciyarmu ta yi sanyi; domin waɗannan abubuwa idanunmu sun dushe
על זה היה דוה לבנו--על אלה חשכו עינינו
18 gama Tudun Sihiyona ya zama kufai, sai diloli ke yawo a wurin.
על הר ציון ששמם שועלים הלכו בו
19 Ya Ubangiji, kai ne mai iko har abada; kursiyinka ya dawwama cikin dukan zamani.
אתה יהוה לעולם תשב כסאך לדור ודור
20 Don mene ne kake mantawa da mu koyaushe? Me ya sa ka yashe mu da jimawa?
למה לנצח תשכחנו תעזבנו לארך ימים
21 Ka sāke jawo mu gare ka, ya Ubangiji, don mu komo; ka sabunta kwanakinmu su zama kamar yadda suke a dā
השיבנו יהוה אליך ונשוב (ונשובה) חדש ימינו כקדם
22 sai dai in ka ƙi mu gaba ɗaya kana fushi da mu fiye da yadda za a iya aunawa.
כי אם מאס מאסתנו קצפת עלינו עד מאד

< Makoki 5 >