< Makoki 4 >
1 Zinariya ta rasa kyanta, hasken zinariya ya dushe! An warwatsar da tsarkakakkun duwatsu masu daraja a kan tituna.
2 Dubi samarin Sihiyona masu daraja, waɗanda a dā darajarsu ta isa nauyin zinariya, yanzu ana ɗaukar su a matsayin tukwanen ƙasa, aikin maginin tukwane!
3 Ko diloli suna ba’ya’yansu nono su sha, amma mutanena sun zama marasa zuciya kamar jiminai a cikin jeji.
4 Domin ƙishirwa harshen jarirai ya manne a rufin bakinsu; yaran suna roƙo a ba su burodi, amma ba wanda ya ba su.
5 Waɗanda a dā sukan ci abinci mai daɗi yanzu su ne masu bara a tituna. Waɗanda a dā suke sa kaya masu kyau yanzu suna kwance a kan tarin toka.
6 Horon mutanena ya fi na Sodom girma, wadda aka hallaka farat ɗaya ba wani hannu da ya juya ya taimake ta.
7 ’Ya’yan sarakunansu sun fi ƙanƙara haske sun kuma fi madara fari, jikunansu sun fi murjani ja, kyansu kamar shuɗin yakutu.
8 Amma yanzu sun fi dare duhu; ba a iya gane su a tituna. Fatar jikinsu ta manne da ƙasusuwansu; sun bushe kamar itace.
9 Gara waɗanda aka kashe su da takobi da waɗanda suke mutuwa da yunwa; sun rame domin rashin abinci a gona.
10 Da hannuwansu mata masu tausayi sun dafa yaransu, suka zama masu abinci sa’ad da aka hallaka mutanena.
11 Ubangiji ya saki fushinsa; ya zuba zafin fushinsa. Ya hura wuta a Sihiyona ta kuma cinye harsashin gininta.
12 Sarakunan duniya ba su gaskata ba, haka ma mutanen duniya, cewa magabta da maƙiya za su iya shiga ƙofofin Urushalima.
13 Amma ya faru domin zunuban annabawanta da muguntar firistocinta, waɗanda suka zub da jinin masu adalci a cikinsu.
14 Yanzu suna yawo barkatai a tituna kamar makafi. Sun ƙazantu da jini yadda ba wanda zai kuskura ya taɓa rigunansu.
15 “Ku tafi! Ba ku da tsabta!” Haka mutane suke ihu suke ce musu. “Ku tashi daga nan! Ku tashi daga nan! Kada ku taɓa mu!” Sa’ad da suka gudu suna yawo, mutanen waɗansu ƙasashe suka ce, “Ba za su ci gaba da zama a nan ba.”
16 Ubangiji kansa ya warwatsa su; ya daina duban su. Ba a ba firistoci girma, ba su ba dattawa gata.
17 Idanunmu sun gaji, suna ta dubawa ko taimako zai zo; mu sa ido ko za mu ga ƙasar da za tă iya taimakon mu.
18 Ana bin sawunmu, ba za mu iya tafiya kan tituna ba. Ƙarshenmu ya kusa, kwanakinmu sun ƙare, gama ƙarshenmu ya zo.
19 Masu fafarar mu sun fi gaggafa mai firiya a sararin sama sauri; sun fafare mu a kan duwatsu suna fakon mu a jeji.
20 Shafaffe na Ubangiji, numfashin ranmu, ya fāɗi cikin tarkonsu. Muna tunani cewa za mu iya rayuwa cikin sauran mutane a ƙarƙashin inuwarsa.
21 Ku yi murna da farin ciki, ya Diyar Edom, ke mai zama a ƙasar Uz. Amma ke ma za a ba ki kwaf; za ki bugu ki zama tsirara.
22 Ya Diyar Sihiyona, hukuncinki zai ƙare; ba zai sa zaman bautarki yă yi tsayi ba. Amma ya Diyar Edom, zai hukunta zunubinki yă tona tsiraicinki.