< Makoki 3 >
1 Ni ne mutumin da ya ga azaba ta wurin bulalar fushin Ubangiji.
I am the man that hath seen affliction under the rod of His wrath;
2 Ya kore ni, ya sa na yi tafiya a cikin duhu maimakon a cikin haske;
He hath led me and brought me into darkness, and not into light;
3 ba shakka, ya juya mini baya, yana gāba da ni sau da sau, dukan yini.
Yea, against me doth he again and again turn his hand all the day long.
4 Ya sa fatar jikina da naman jikina sun tsufa ya kuma karya ƙasusuwana.
My flesh and my skin hath he made old; he hath broken my bones.
5 Ya yi mini kwanton ɓauna ya kuma kewaye ni da baƙin ciki da kuma wahala.
He hath builded against me, and encompassed me with bitterness and woe.
6 Ya sa na zauna a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu da jimawa.
He hath set me in dark places, as those that have long been dead.
7 Ya kewaye ni yadda ba zan iya gudu ba; Ya daure ni da sarƙa mai nauyi.
He hath hedged me about, so that I cannot get out; he hath made my chain heavy;
8 Ko lokacin da nake kira don neman taimako, ba ya jin addu’ata.
Yea, when I cry and call aloud, he shutteth out my prayer.
9 Ya tare hanyata da tubula na duwatsu; ya sa hanyata ta karkace.
He blocketh up my way with hewn stone; he maketh my paths crooked.
10 Kamar beyar da take a laɓe tana jira, kamar zaki a ɓoye,
A bear lying in wait hath he been to me, a lion in lurking-places.
11 ya janye ni daga kan hanya ya ɓatar da ni ya bar ni ba taimako.
He hath turned aside my ways, and torn me in pieces; he hath made me desolate.
12 Ya ja kwarinsa ya sa in zama abin baratarsa.
He hath bent his bow, and set me as a mark for the arrow.
13 Ya harbi zuciyata da kibiyoyin kwarinsa.
He hath caused the sons of his quiver to pierce my reins.
14 Na zama abin dariya ga mutanena duka; suna yi mini ba’a cikin waƙa dukan yini.
I have been a laughing-stock to all my people, their song all the day.
15 Ya cika ni da kayan ɗaci ya gundure ni da abinci mai ɗaci.
He hath filled me with bitterness; he hath made me drunk with wormwood.
16 Ya kakkarya haƙorana da tsakuwa; ya tattake ni cikin ƙura.
He hath also broken my teeth with gravel-stones; He hath covered me with ashes.
17 An hana ni salama; na manta da ko mene ne ake kira wadata.
Yea, thou hast removed my soul far from peace; I have forgotten prosperity.
18 Saboda haka na ce, “Darajata ta ƙare da kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji.”
And I say, “My confidence and my hope in Jehovah are gone!”
19 Na tuna da azabata da kuma sintiri, da na yi ta yi da ɗacin rai.
Remember my affliction and my misery, the wormwood and the gall!
20 Na tuna su sosai, sai kuma na ji ba daɗi a raina.
Yea, thou wilt remember them, for my soul sinketh within me!
21 Duk da haka na tuna da wannan na kuma sa bege ga nan gaba.
This I recall to my mind; therefore have I hope;
22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba; gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
It is of the mercy of Jehovah that we are not consumed; yea, his compassion faileth not;
23 Sababbi ne kowace safiya; amincinka kuwa mai girma ne.
It is new every morning; great is thy faithfulness.
24 Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa; saboda haka zan jira shi.”
Jehovah is my portion, saith my soul, therefore do I hope in him.
25 Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa, ga kuma wanda yake neman shi;
Jehovah is good to them that trust in him, to the soul that seeketh him.
26 yana da kyau ka jira shiru domin samun ceton Ubangiji.
It is good that a man hope, and quietly wait for salvation from Jehovah.
27 Yana da kyau mutum yă sha wuya tun yana yaro.
It is good for a man that he bear the yoke in his youth;
28 Bari yă zauna shiru shi kaɗai, gama haka Ubangiji ya sa yă yi.
That he sit alone and keep silence, since He layeth it upon him;
29 Bari yă ɓoye fuskarsa cikin ƙura kila akwai bege.
That he put his mouth in the dust, [[saying to himself, ]] “Perhaps there may be hope!”
30 Bari yă ba da kumatunsa a mare shi, yă kuma bari a ci masa mutunci.
That he offer his cheek to the smiter; that he be filled with reproach.
31 Gama Ubangiji ba ya yashe mutane har abada.
For the Lord will not cast off forever;
32 Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai, ƙaunarsa tana da yawa.
For though he cause grief, yet doth he have compassion according to his great mercy;
33 Gama ba haka kawai yake kawo wahala ko ɓacin rai ga’yan adam ba.
For he doth not willingly afflict and grieve the children of men.
34 Bai yarda a tattake’yan kurkuku a ƙasa ba,
Doth one trample under foot all the prisoners of the earth,
35 ko kuma a danne wa mutum hakkinsa a gaban Maɗaukaki,
Doth he bend the right of a man before the face of the Most High,
36 ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiya ashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba?
Doth he subvert a man in his cause, and shall not the Lord behold it?
37 Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cika in ba Ubangiji ne ya umarta ba?
Who is he that saith, and it cometh to pass, when the Lord hath not commanded?
38 Ba daga bakin Maɗaukaki ne bala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba?
Cometh not evil, as well as good, from the mouth of the Most High?
39 Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa?
Wherefore then murmureth the living man? Let him murmur at his own sin!
40 Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta, sai mu kuma koma ga Ubangiji.
Let us search and try our ways, and turn again to Jehovah!
41 Bari mu ɗaga zuciyarmu da hannuwanmu ga Allah na cikin sama, mu ce,
Let us lift up our hearts with our hands to God in the heavens!
42 “Mun yi zunubi mun yi tawaye ba ka kuwa gafarta ba.
We have transgressed; we have rebelled; thou hast not forgiven!
43 “Ka rufe kanka da fushi, ka fafare mu; ka karkashe mu ba tausayi.
Thou hast hidden thyself in anger, and hast pursued us; thou hast slain and hast not spared;
44 Ka rufe kanka da gajimare don kada addu’armu ta kai wurinka.
Thou hast hidden thyself in a cloud, that our prayer may not pass through;
45 Ka mai da mu tarkace da juji a cikin mutane.
Thou hast made us the offscouring and refuse in the midst of the nations.
46 “Dukan maƙiyanmu suna ta yin mana magana marar daɗi.
All our enemies have opened their mouths against us;
47 Muna cika da tsoro, da lalatarwa da hallakarwa.”
Terror and the pit have come upon us, desolation and destruction;
48 Hawaye na kwararowa daga idanuna domin an hallaka mutanena.
Mine eye runneth down with streams of water for the destruction of the daughter of my people.
49 Idanuna za su ci gaba da kwararowa da hawaye, ba hutawa.
Mine eye trickleth down and ceaseth not, without any intermission,
50 Har sai in Ubangiji ya duba daga sama ya gani.
Until Jehovah look down and behold from heaven.
51 Abin da nake gani yana kawo mini baƙin ciki domin dukan matan birnina.
Mine eye is painful to me on account of all the daughters of my city.
52 Maƙiyana suna farauta ta ba dalili kamar tsuntsu.
They that are my enemies without cause hunt me down like a bird;
53 Sun yi ƙoƙari su kashe ni a cikin rami suka kuma jajjefe ni da duwatsu;
They take away my life in the dungeon; they cast a stone upon me;
54 ruwaye suka rufe kaina, sai na yi tunani cewa na kusa mutuwa.
Waters flow over my head; I say, “I am undone!”
55 Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji, daga rami mai zurfi.
I call upon thy name, O Jehovah, from the deep dungeon;
56 Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwanka ka ƙi jin roƙona na neman taimako.”
Hear thou my voice! hide not thine ear from my cry for relief!
57 Ka zo kusa lokacin da na kira ka, kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.”
Be near to me, when I call upon thee! Say, “Fear not!”
58 Ya Ubangiji, ka goyi bayana; ka fanshi raina.
Thou maintainest my cause, O Lord; thou redeemest my life!
59 Ya Ubangiji, ka ga inda aka yi mini ba daidai ba. Ka shari’anta, ka ba ni gaskiya!
Thou, O Jehovah, seest the wrong done to me; Maintain thou my cause!
60 Ka ga zurfin ramakonsu, da duk mugun shirin da suke yi mini.
Thou seest all their vengeance, all their devices against me.
61 Ya Ubangiji, ka ji zaginsu, da duka mugun shirin da suke yi mini
Thou hearest their reproach, O Jehovah, all their devices against me,
62 Abin da maƙiyana suke yin raɗa a kai game da ni duk yini.
The words of my adversaries, and their machinations against me all the day long!
63 Dube su! A zaune ko a tsaye, suna yi mini ba’a cikin waƙoƙinsu.
Behold their sitting down and their rising up! I am their song.
64 Ka ba su abin da ya dace su samu, ya Ubangiji, domin abin da hannuwansu suka yi.
Render to them a recompense, O Jehovah, according to the work of their hands!
65 Ka sa yana ta rufe zuciyarsu, kuma bari la’anarka ta bi su.
Give them blindness of mind! thy curse be upon them!
66 Ka fafare su cikin fushi ka hallaka su daga cikin duniya ta Ubangiji.
Pursue them in thine anger, and destroy them from under Jehovah's heaven!