< Makoki 1 >

1 Yanzu birnin ya zama babu kowa a ciki, birnin da a dā yake cike da mutane! Yanzu birnin ya zama kamar gwauruwa, wadda a dā babba ce ita a cikin ƙasashe! Ita da take sarauniya a cikin larduna yanzu ta zama baiwa.
איכה ישבה בדד העיר רבתי עם--היתה כאלמנה רבתי בגוים שרתי במדינות--היתה למס
2 Tana yin kuka mai zafi da dare, hawaye na gangara a kan kumatunta. A cikin masoyanta duka babu wanda ya yi mata ta’aziyya. Duk abokanta sun yashe ta; sun zama abokan gābanta.
בכו תבכה בלילה ודמעתה על לחיה--אין לה מנחם מכל אהביה כל רעיה בגדו בה היו לה לאיבים
3 Bayan wahala da baƙin ciki, Yahuda ta tafi bauta. Ta zauna a cikin ƙasashe, ba tă samu wurin hutawa ba. Duk masu fafararta sun same ta sa’ad da take cikin matuƙar ɓacin rai.
גלתה יהודה מעני ומרב עבדה--היא ישבה בגוים לא מצאה מנוח כל רדפיה השיגוה בין המצרים
4 Hanyoyin zuwa Sihiyona suna makoki, gama ba wanda ya zo bikin da ta shirya. Ba kowa a hanyoyin shiganta. Firistocinta suna gurnani,’yan matana kuma suna wahala, kuma tana cikin shan wahala ƙwarai.
דרכי ציון אבלות מבלי באי מועד--כל שעריה שוממין כהניה נאנחים בתולתיה נוגות והיא מר לה
5 Maƙiyanta sun zama shugabanninta; Abokan gābanta suna da kwanciyar rai. Ubangiji ya kawo mata ɓacin rai domin yawan zunubanta.’Ya’yanta sun tafi bauta, a ƙarƙashin maƙiyanta.
היו צריה לראש איביה שלו כי יהוה הוגה על רב פשעיה עולליה הלכו שבי לפני צר
6 Diyar Sihiyona ba ta da sauran daraja.’Ya’yan sarakunanta sun zama kamar bareyi waɗanda suka rasa wurin kiwo; cikin rashin ƙarfi suka guje wa masu fafararsu.
ויצא מן בת (מבת) ציון כל הדרה היו שריה כאילים לא מצאו מרעה וילכו בלא כח לפני רודף
7 A cikin kwanakin da take shan wahala take kuma yawo Urushalima ta tuna da dukan dukiyar da take da ita a kwanakin dā can. Sa’ad da mutanenta suka faɗa cikin hannun abokan gābanta, ba wanda ya taimake ta. Maƙiyanta suka dube ta suka yi mata dariya don hallakar da ta auko mata.
זכרה ירושלם ימי עניה ומרודיה--כל מחמדיה אשר היו מימי קדם בנפל עמה ביד צר ואין עוזר לה--ראוה צרים שחקו על משבתה
8 Urushalima ta yi zunubi ƙwarai saboda haka ta zama marar tsarki. Dukan masu martaba ta sun raina ta, gama sun ga tsiraicinta; ita ma da kanta tana nishi da ƙyar ta kuma juya baya.
חטא חטאה ירושלם על כן לנידה היתה כל מכבדיה הזילוה כי ראו ערותה גם היא נאנחה ותשב אחור
9 Ƙazantarta ta manne wa rigunanta; ba tă kula da nan gaba ba, fāɗuwarta kuwa babban abu ne; babu wanda zai yi mata ta’aziyya. “Duba, ya Ubangiji, ka ga wahalata, gama maƙiyi ya yi nasara.”
טמאתה בשוליה לא זכרה אחריתה ותרד פלאים אין מנחם לה ראה יהוה את עניי כי הגדיל אויב
10 Maƙiya ya kwashe dukiyarta duka; ta ga mutanen da ba su san Allah ba sun shiga wuri mai tsarkinta waɗanda ka hana su shiga taron jama’arka.
ידו פרש צר על כל מחמדיה כי ראתה גוים באו מקדשה--אשר צויתה לא יבאו בקהל לך
11 Dukan mutanenta suna nishi da ƙyar suna neman burodi; sun sayar da dukiyarsu don su samu abinci don kada su mutu da yunwa. “Ubangiji, ka duba ka gani, gama an yashe ni.”
כל עמה נאנחים מבקשים לחם נתנו מחמודיהם (מחמדיהם) באכל להשיב נפש ראה יהוה והביטה כי הייתי זוללה
12 “Ko wannan ba wani abu ba ne a wurinku, dukanku masu wucewa? Ku duba ku gani. Ko akwai wata wahala kamar irin wadda nake sha, wadda Ubangiji ya auko mini a cikin zafin fushinsa?
לוא אליכם כל עברי דרך--הביטו וראו אם יש מכאוב כמכאבי אשר עולל לי אשר הוגה יהוה ביום חרון אפו
13 “Daga sama ya aiko da wuta, ya aiko ta cikin ƙasusuwana. Ya shimfiɗa raga a ƙafafuna ya juyo da ni. Ya bar ni ni kaɗai, sumamme dukan yini.
ממרום שלח אש בעצמתי וירדנה פרש רשת לרגלי השיבני אחור--נתנני שממה כל היום דוה
14 “Ya ɗaura zunubaina a wuyana; aka naɗe su a hannuwansa. Aka rataye su a wuyana Ubangiji ya kwashe ƙarfina. Ya bashe ni ga waɗanda suka fi ni ƙarfi.
נשקד על פשעי בידו ישתרגו עלו על צוארי--הכשיל כחי נתנני אדני בידי לא אוכל קום
15 “Ubangiji ya ƙi duk mayaƙan da suke tare da ni; ya sa wata runduna ta tayar mini ta kuma tattake samarina. Ubangiji ya tattake budurwa Diyar Yahuda kamar’ya’yan inabi a wurin matsewa.
סלה כל אבירי אדני בקרבי קרא עלי מועד לשבר בחורי גת דרך אדני לבתולת בת יהודה
16 “Dalilin da ya sa nake kuka ke nan idanuna kuma suna ta zubar da hawaye. Babu wani a kusa da zai yi mini ta’aziyya, ba wanda zai sabunta ruhuna.’Ya’yana sun zama fakirai domin maƙiyina ya yi nasara.”
על אלה אני בוכיה עיני עיני ירדה מים--כי רחק ממני מנחם משיב נפשי היו בני שוממים כי גבר אויב
17 Sihiyona ta miƙa hannunta, amma ba wani da zai yi mata ta’aziyya. Ubangiji ya umarta cewa maƙwabtansa za su zama maƙiyansa; Urushalima ta zama abar ƙyama a cikinsu.
פרשה ציון בידיה אין מנחם לה--צוה יהוה ליעקב סביביו צריו היתה ירושלם לנדה ביניהם
18 “Ubangiji mai adalci ne, duk da haka na yi tawaye da umarninsa. Ku saurara, jama’a duka; ku dubi wahalar da nake sha. Samarina da’yan matana duka sun tafi bauta.
צדיק הוא יהוה כי פיהו מריתי שמעו נא כל עמים (העמים) וראו מכאבי--בתולתי ובחורי הלכו בשבי
19 “Na kira abokaina amma sun yashe ni. Firistocina da dattawana sun hallaka a cikin birnin yayinda suke neman abinci don kada su mutu da yunwa.
קראתי למאהבי המה רמוני כהני וזקני בעיר גועו כי בקשו אכל למו וישיבו את נפשם
20 “Duba, Ubangiji, ka ga ƙuncin da nake ciki! Ina shan azaba a raina, ba ni da kwanciyar rai a cikin zuciyata, domin na yi tawaye sosai. A waje takobi na kisa; a ciki kuma akwai mutuwa.
ראה יהוה כי צר לי מעי חמרמרו--נהפך לבי בקרבי כי מרו מריתי מחוץ שכלה חרב בבית כמות
21 “Mutane suna ji ina nishi da ƙyar, amma ba wanda zai yi mini ta’aziyya. Dukan maƙiyana sun ji wahalar da nake ciki; suna farin ciki da abin da ka yi. Ka kawo ranan nan da ka sanar domin su ma su zama kamar ni.
שמעו כי נאנחה אני אין מנחם לי--כל איבי שמעו רעתי ששו כי אתה עשית הבאת יום קראת ויהיו כמני
22 “Bari ka ga muguntarsu duka; ka yi musu yadda ka yi mini domin dukan zunubansu. Nishina da yawa kuma zuciyata ta gaji.”
תבא כל רעתם לפניך ועולל למו כאשר עוללת לי על כל פשעי כי רבות אנחתי ולבי דוי

< Makoki 1 >