< Mahukunta 9 >

1 Abimelek ɗan Yerub-Ba’al ya tafi Shekem wurin’yan’uwan mahaifiyarsa, ya ce musu da kuma dukan dangin mahaifiyarsa,
耶魯巴耳的兒子阿彼默肋客到舍根去見他的母舅們,對他們和他母家的人說:「
2 “Ku tambayi’yan ƙasar Shekem, ‘Wanne ya fi muku, a sa dukan’ya’yan Yerub-Ba’al saba’in maza su yi mulkinku, ko dai mutum guda kawai yă yi mulkinku?’ Ku tuna, ni jininku ne.”
請你們問一問舍根所有的公民:是耶魯巴耳的兒子七十人治理你們好呢﹖還是一個人治理你們好呢﹖你們還要記得:我是你們的骨肉。」
3 Sa’ad da’yan’uwan suka mayar wa’yan ƙasar Shekem wannan, sai suka goyi bayan Abimelek, gama sun ce, “Shi ɗan’uwanmu ne.”
他的母舅們就替他把這些話傳給舍根所有的公民;他們的心都傾向阿彼默肋客,因為他們說:「他確是我們的兄弟! 」
4 Suka ba shi shekel saba’in na azurfa daga haikalin Ba’al-Berit, Abimelek kuwa ya yi amfani da shi ya yi hayar’yan tauri waɗanda suka zama masu binsa.
他們遂從巴耳貝黎特廟裏拿了七十塊銀錢給他,阿彼默肋客就用這些錢僱了一些放蕩無賴之徒跟隨他。
5 Sai ya tafi gidan mahaifinsa a Ofra kuma a dutse guda ya kashe’yan’uwansa,’ya’yan Yerub-Ba’al. Amma Yotam, autan ɗan Yerub-Ba’al ya tsira ta wurin ɓuya.
他回到敖弗辣他父親家裏,在一塊石頭上把自己的兄弟,即耶魯巴耳的兒子七十人都殺了,只剩下耶魯巴耳的幼子約堂,因為他藏了起來。
6 Sa’an nan duka’yan ƙasar Shekem da Bet Millo suka taru kusa da babban itacen wajen ginshiƙi a Shekem don a naɗa Abimelek sarki.
於是舍根所有的公民和貝特米羅人都集合起來,在舍根的紀念碑前那棵橡樹下,立阿彼默肋客為王。約堂講寓言
7 Sa’ad da aka gaya wa Yotam wannan, sai ya hau Dutsen Gerizim ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Ku saurare ni,’yan ƙasar Shekem, don Allah yă saurare ku.
有人將此事告訴了約堂,約堂就上了革黎斤山頂,站在那裏,高聲向他們喊說:「舍根公民,請你們聽我,望天主也聽你們!
8 Wata rana itatuwa suka fita don su naɗa wa kansu sarki. Suka ce wa itacen zaitun, ‘Ka zama sarkinmu.’
有一次,眾樹要去立一樹為他們的君王,就對橄欖樹說:請你作我們的君王!
9 “Amma itacen zaitun ya ce, ‘In bar mai nawa, wanda da shi ake girmama alloli da mutane, don in zo in yi ta fama da itatuwa?’
橄欖樹回答說:人用我的油來敬禮神,尊崇人,難道要我放棄出油,而去搖搖在眾樹之上嗎﹖
10 “Biye da wannan, sai itatuwan suka ce wa itacen ɓaure, ‘Zo ka zama sarkinmu.’
眾樹又對無花果樹說:請你來作我們的君王!
11 “Amma itacen ɓauren ya ce, ‘In bar kyawawan’ya’yana da zaƙinsu, in zo in yi ta fama da itatuwa?’
無花果樹回答說:難道要我捨掉我的甘甜和美果,而去搖搖在眾樹之上嗎﹖
12 “Sa’an nan itatuwan suka ce wa kuringar inabi, ‘Ki zo ki zama sarkinmu.’
眾樹又對葡萄樹說:請你來作我們的君王!
13 “Amma kuringar ta ce, ‘In bar ruwan inabina, wanda yake faranta zuciyar alloli da mutane, in zo in yi fama da itatuwa?’
葡萄樹就回答說:我的新酒悅樂神人,難道要我放棄出產,而去搖搖在眾樹之上嗎﹖
14 “A ƙarshe sai dukan itatuwa suka ce wa itacen ƙaya, ‘Ka zo ka zama sarkinmu.’
於是眾樹對荊棘說:請你來作我們的君王!
15 “Itacen ƙaya ya ce wa itatuwan, ‘In da gaske ne kuke so ku naɗa ni sarkinku, ku zo ku sha inuwana; in ba haka ba, bari wuta ta fito daga itacen ƙaya ta cinye itacen al’ul na Lebanon!’
荊棘對樹木答道:若你們真願立我作你們的君王,來罷! 躲在我的蔭下;否則,火必從荊棘冒出,吞滅黎巴嫩的香柏木。
16 “To, da a ce kun yi abin bangirma da aniya mai kyau sa’ad da kuka naɗa Abimelek sarki, da kun nuna wa Yerub-Ba’al da iyalinsa ladabi, da kuma kun yi masa abin da ya cancanci shi,
現在,你們立阿彼默肋客為王,如果你們認為作的真誠正直,如果你們認為是善待了耶魯巴耳和他的家族,如果你們認為你們這樣行事,對得起他一手所立的功勳,─
17 a yi tunani cewa mahaifina ya yi yaƙi saboda ku, ya yi kasai da ransa don yă cece ku daga hannun Midiyawa
因為原是我父親為你們作戰而捨生,把你們由米德楊手中救出來。
18 (amma ga shi yau kun tayar wa iyalin mahaifina, kuka kashe’ya’yansa saba’in a dutse guda, kuka kuma naɗa Abimelek, ɗan baiwa, sarki a kan’yan ƙasar Shekem domin shi ɗan’uwanku ne)
然而你們今日卻來反對我父親的家族,在一塊石頭上殺了他的兒子七十人,立他婢女的兒子阿彼默肋客為舍根公民的君王,因為他是你們的弟兄。─
19 in har kun aikata wannan cikin bangirma da kuma aminci wajen Yerub-Ba’al da iyalinsa a yau, bari Abimelek yă zama farin cikinku, ku kuma nasa!
今天如果你們認為以真誠正直對待了耶魯巴耳和他的家族,那麼,你們就因阿彼默肋客而喜樂罷! 希望他有因你們而喜樂!
20 Amma in ba haka ba, bari wuta ta fito daga Abimelek ya cinye ku,’yan ƙasar Shekem da Bet Millo, bari wuta kuma daga wurinku’yan ƙasar Shekem da Bet Millo ta cinye Abimelek!”
不然,願火從阿彼默肋客發出,吞滅舍根的公民和貝特米羅! 也願火從舍根的公民和貝特米羅發出,吞滅阿彼默肋客! 」
21 Sa’an nan Yotam ya gudu, ya tsere zuwa Beyer ya zauna a can gama yana tsoron ɗan’uwansa Abimelek.
以後約堂出走,逃到貝爾去了,住在那裏,遠避他的哥哥阿彼默肋客。舍根叛變
22 Bayan Abimelek ya yi shekara uku yana mulki a Isra’ila,
阿彼默肋客治理以色列三年。
23 sai Allah ya aiko da mugun ruhu tsakanin Abimelek da’yan ƙasar Shekem, waɗanda suka ci amanar Abimelek.
天主使惡神降在阿彼默肋客和舍根公民中間,舍根的公民便背叛了阿彼默肋客,
24 Allah ya yi haka saboda kisan’ya’ya saba’in na Yerub-Ba’al, don a ɗauki fansar jininsu a kan Abimelek ɗan’uwansu da kuma’yan ƙasar Shekem, waɗanda suka taimake shi kisan’yan’uwansa.
要報復對耶魯巴耳七十個兒子的罪行,將他們的血歸於他們的兄弟阿彼默肋客,因為是他殺害了他們;也歸於舍根的公民,因為他們曾鼓勵他殺害自己的兄弟。
25 Cikin hamayya da shi waɗannan’yan ƙasar Shekem suka sa mutane a kan tuddai don su yi kwanton ɓauna a kan su yi fashi ga duk wanda ya wuce a can, wannan fa ya kai kunnen Abimelek.
舍根公民為反抗他,就在山頂上設下伏兵,搶掠所有路過他們那裏的人:有人將這事報告給阿彼默肋客。
26 To, Ga’al ɗan Ebed ya tafi tare da’yan’uwansa zuwa Shekem,’yan ƙasarta kuwa suka dogara da shi.
那時厄貝得的兒子加阿耳和他同族的人遷徙到舍根,舍根的居民竟信任了他;
27 Bayan sun tafi gonaki suka tattara inabi suka matse su, sai suka yi biki a haikalin allahnsu. Yayinda suke ci da sha, sai suka la’anci Abimelek.
他們便到田間收葡萄,榨酒,開慶祝會,到他們的神廟裏又吃又喝,也咒罵了阿彼默肋客。
28 Sa’an nan Ga’al ɗan Ebed ya ce, “Wane ne Abimelek, kuma wane ne Shekem, da za mu bauta masa? Shi ba ɗan Yerub-Ba’al ba ne, kuma ba Zebul ne mataimakinsa ba? Ku bauta wa mutanen Hamor, mahaifin Shekem! Me ya sa za mu bauta wa Abimelek?
厄貝得的兒子加阿耳說:「阿彼默肋客是誰,我們舍根人是誰,我們竟該服侍他﹖豈不是耶魯巴耳的兒子和官員則步耳,該服侍舍根的始祖哈摩爾的後人嗎﹖我們為什麼要服侍阿彼默肋客﹖
29 Da a ce waɗannan mutane suna a ƙarƙashina mana! Da zan hamɓarar da shi. In ce wa Abimelek, ‘Ka tara dukan mayaƙanka!’”
恨不得這百姓交於我手中,好把阿彼默肋客除掉。我要對阿彼默肋客說:增派你的軍隊出征罷! 」
30 Sa’ad da Zebul gwamnar birnin ya ji abin da Ga’al ɗan Ebed ya ce, sai ya fusata.
則步耳城尉聽到厄貝得的兒子加阿耳的話,大發忿怒,
31 Asirce sai ya aiki manzanni wajen Abimelek, yana cewa, “Ga’al ɗan Ebed da’yan’uwansa sun zo Shekem suna kuma zuga birnin sun tayar maka.
遂打發使者去見在阿魯瑪的阿彼默肋客說:「看,厄貝得的兒子加阿耳和他的同族人,來到舍根,挑唆全城反叛你。
32 To, in dare ya yi, sai ka zo da mutanenka ku yi kwanto a filaye.
所以現在你和跟隨你的人夜裏要起來,埋伏在田野間,
33 Kashegari da safe, sai ku tashi ku fāɗa wa birnin. Sa’ad da Ga’al da mutanensa suka faɗa maka, sai ka yi abin da ka iya yi da su.”
明天早晨太陽一出來,就攻城。當他和隨從他的人出來抵抗你時,你看看怎樣好,就怎樣對付他。」
34 Saboda haka Abimelek da dukan mutanensa suka tashi da dare suka ɓuya kusa da Shekem a ƙungiyoyi huɗu.
阿彼默肋客遂同所有跟隨他的人夜間起身,分作四隊,對著舍根設下埋伏。
35 To, Ga’al ɗan Ebed ya riga ya fita waje yana tsaye a ƙofar birni daidai Abimelek da mayaƙansa suka fito daga inda suka ɓuya.
當厄貝得的兒子加阿耳出來,站在城門口時,阿彼默肋客便與隨從他的人從埋伏的地方出來,
36 Sa’ad da Ga’al ya gan su, sai ya ce wa Zebul, “Duba, ga mutane suna gangarowa daga kan duwatsu!” Zebul ya ce, “Kana ɗaukan inuwan duwatsu kana ce mutane.”
加阿耳一見這些人就對則步耳說:「看,有人從山頂下來! 」則步耳回答他說:「你看見山影,誤以為是人! 」
37 Amma Ga’al ya sāke magana ya ce, “Duba, mutane suna gangarowa daga tsakiyar filaye, kuma wata ƙungiya tana zuwa daga wajen itacen masu duba.”
加阿耳接著又說:「看,有人從高地出來,又有一隊沿巫士橡樹道上前來。」
38 Sa’an nan Zebul ya ce masa, “Ina bakin da ka yi ɗin, kai da ka ce, ‘Wane ne Abimelek da za mu bauta masa.’ Ba mutanen ne ka yi musu ba’a ba? Fita, ka yaƙe su mana!”
則步耳對他說:「現在你的口在那裏﹖不是你曾說過:阿彼默肋客是誰,要我們服侍他﹖這不是你所輕視的人嗎﹖現在請你出去攻打他罷! 」
39 Saboda haka Ga’al ya fito da’yan ƙasar Shekem suka yaƙi Abimelek.
加阿耳就在舍根公民之前出去,攻打阿彼默肋客;
40 Abimelek ya kore shi, mutane da yawa suka ji ciwo a yaƙin, har zuwa ƙofar birnin.
a可是阿彼默肋客一追擊他,他就在他面前逃跑了;直到城門有許多傷亡的人。
41 Abimelek ya zauna a Aruma, Zebul kuwa ya kori Ga’al da’yan’uwansa daga Shekem.
以後阿彼默肋客回到阿魯瑪;則步耳將加阿耳和他的同族人趕走,禁止他們住在舍根。舍根滅亡
42 Kashegari mutanen Shekem suka tafi gonaki, aka kuwa gaya wa Abimelek.
第二天早晨,人民到田野裏去,有人告訴了阿彼默肋客,
43 Saboda haka ya ɗauki mutanensa, ya raba su ƙungiya uku, sa’an nan ya yi kwanto a gonakin. Sa’ad da ya ga mutanen suna fitowa daga birni, sai ya yi wuf ya fāɗa musu.
他於是把自己的人分作三隊,叫他們埋伏在田間;他自己窺望,當他看見百姓從城裏出來,就衝過去,擊殺了他們;
44 Abimelek da ƙungiyoyin da suke tare da shi suka yi maza suka yi tsaya a ƙofar birnin. Sa’an nan ƙungiyoyi biyu suka ruga suka fāɗa wa waɗanda suke a gonaki suka karkashe su.
當時阿彼默肋客與跟隨他的軍隊衝過去,把住城門口,而另兩隊衝向田間的眾人,殺了他們。
45 Dukan yinin, Abimelek ya matsa yaƙi da birnin sai da ya cinye ta ya kuma kashe mutanenta. Sa’an nan ya hallaka birnin ya barbaza gishiri a kanta.
那一天,阿彼默肋客整天攻打那城,把城攻下,殺了城中的居民,把城拆毀,撒上鹽。
46 Da jin haka, sai’yan ƙasa a hasumiyar Shekem suka shiga wurin mafaka a hankalin El-Berit.
舍根碉堡裏的人聽見此事,就躲到巴耳貝黎特廟裏的地穴裏。
47 Da Abimelek ya ji dukan mutanen hasumiyar Shekem sun taru a can,
有人告訴阿彼默肋客,人民都聚集在舍根碉堡內。
48 sai Abimelek da dukan mutanensa suka haura zuwa Dutsen Zalmon. Sai ya ɗauki gatari ya sassare waɗansu rassa, waɗanda ya sa a kafaɗunsa. Ya umarci mutanen da suke tare da shi ya ce, “Sauri, ku yi abin da kuka ga na yi!”
阿彼默肋客和跟隨他的人就上了匝耳孟山;阿彼默肋客手裏拿著一把斧頭,砍了一根樹枝,拿起來放在肩上,然後向跟隨他的人說:「你們看我作什麼,你們也趕快照樣去作! 」
49 Saboda haka mutanen suka sassare rassan itatuwa suka bi Abimelek. Suka tattara su a jikin mafakar suka kuma cinna mata wuta a kan mutanen da suke a ciki. Ta haka dukan mutanen da suke cikin hasumiyar Shekem, wajen maza da mata dubu ɗaya suka mutu.
於是眾人都各砍了根樹枝,隨著阿彼默肋客把樹枝堆在地穴上,在地穴上點了火,於是舍根碉堡裏所有的人都死了,男女約有一千人。阿彼默肋客的結局
50 Biye da wannan Abimelek ya tafi Tebez, ya kewaye ta ya kuma cinye ta da yaƙi.
此後阿彼默肋客往特貝茲去,安營攻打特貝茲,也佔據了那城。
51 A cikin birnin, akwai wata hasumiya mai ƙarfi, inda dukan maza da mata, dukan mutanen birnin, suka ɓuya. Suka kulle kansu, suka kuma hau rufin hasumiyar.
在那城中有一座堅固的城堡,該城所有的公民,男男女女都跑到那裏躲避,關上門,上到碉堡頂上。
52 Abimelek ya je wajen hasumiya ya kuma auka mata. Amma da ya yi kusa da ƙofar hasumiyar don yă cinna mata wuta,
阿彼默肋客來到碉堡前攻打;當他走近碉堡門口,要放火焚燒時,
53 sai wata mata ta saki ɗan dutsen niƙa a kan Abimelek ta fasa ƙoƙon kansa.
有一個婦人拋下了一塊磨石,正落在阿彼默肋客頭上,打碎了他的頭蓋骨。
54 Da sauri ya kira mai riƙon masa makami ya ce, “Zaro takobinka ka kashe ni, don kada a ce ‘Mace ce ta kashe shi.’” Saboda haka bawansa ya soke shi, ya mutu.
他急忙喊叫替他執戟的少年,向他說:「拔出你的刀殺了我罷! 免得人講論我說:一個女子殺了他! 」那少年就用刀刺死了他。
55 Sa’ad da Isra’ilawa suka ga Abimelek ya mutu, sai suka tafi gida.
以色列人一見阿彼默肋客死了,各回了本家。
56 Ta haka Allah ya sāka muguntar da Abimelek da ya yi wa mahaifinsa ta wurin kisan’yan’uwansa saba’in.
於是天主報復了阿彼默肋客對他父親所行的惡事,因為他殺了自己的七十個兄弟;
57 Allah kuma ya sa muguntar mutanen Shekem suka koma kansu. La’anar Yotam ɗan Yerub-Ba’al kuma ta kama su.
並且天主也把舍根人的一切惡行歸在他們自己的頭上:這樣耶魯巴耳的兒子約堂的詛咒,也應驗在他們身上。

< Mahukunta 9 >