< Mahukunta 7 >

1 Kashegari da sassafe, Yerub-Ba’al (wato, Gideyon) da dukan mutanensa suka kafa sansani a maɓulɓulan Harod. Sansanin Midiyawa kuma yana arewa da su a kwari kusa da tudu na More.
וישכם ירבעל הוא גדעון וכל העם אשר אתו ויחנו על עין חרד ומחנה מדין היה לו מצפון מגבעת המורה בעמק
2 Sai Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Mutanen da kake da su sun yi mini yawa da zan ba da Midiyawa a hannunsu. Don kada Isra’ila tă yi mini fahariya cewa ƙarfinta ne ya cece su,
ויאמר יהוה אל גדעון רב העם אשר אתך מתתי את מדין בידם פן יתפאר עלי ישראל לאמר ידי הושיעה לי
3 ka yi shela ga mutane yanzu cewa, ‘Duk wanda ya yi rawan jiki don tsoro, sai yă juya yă bar Dutsen Gileyad.’” Saboda haka mutum dubu ashirin da biyu suka koma, sai mutum dubu goma suka rage.
ועתה קרא נא באזני העם לאמר מי ירא וחרד ישב ויצפר מהר הגלעד וישב מן העם עשרים ושנים אלף ועשרת אלפים נשארו
4 Amma Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Har yanzu mutanen sun yi yawa. Ka kai cikin ruwa, in kuma tankaɗe maka su a can. In na ce, ‘Wannan zai tafi da kai,’ to, zai tafi; amma in na ce, ‘Wannan ba zai tafi da kai ba,’ to, ba zai tafi ba.”
ויאמר יהוה אל גדעון עוד העם רב הורד אותם אל המים ואצרפנו לך שם והיה אשר אמר אליך זה ילך אתך הוא ילך אתך וכל אשר אמר אליך זה לא ילך עמך הוא לא ילך
5 Saboda haka Gideyon ya kai mutanen cikin ruwa. A can Ubangiji ya ce masa, “Ka ware waɗanda suka tanɗi ruwa kamar kare daga waɗanda suka durƙusa suka sha ruwan.”
ויורד את העם אל המים ויאמר יהוה אל גדעון כל אשר ילק בלשונו מן המים כאשר ילק הכלב תציג אותו לבד וכל אשר יכרע על ברכיו לשתות
6 Mutum ɗari uku sun tanɗi ruwa, dukan sauran kuwa suka durƙusa suka sha ruwan.
ויהי מספר המלקקים בידם אל פיהם--שלש מאות איש וכל יתר העם כרעו על ברכיהם לשתות מים
7 Sai Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Da mutum ɗari uku ɗin nan da suka tanɗi ruwa, zan cece ka in kuma ba da Midiyawa a hannuwanku. Ka bar sauran mutane su tafi kowa zuwa wurinsa.”
ויאמר יהוה אל גדעון בשלש מאות האיש המלקקים אושיע אתכם ונתתי את מדין בידך וכל העם--ילכו איש למקמו
8 Saboda haka Gideyon ya mai da sauran Isra’ilawa zuwa tentinsu amma ya riƙe mutum ɗari uku waɗanda suka karɓi guzuri da ƙahonin sauran. To, sansanin Midiyawa yana ƙasa da su a kwarin.
ויקחו את צדה העם בידם ואת שופרתיהם ואת כל איש ישראל שלח איש לאהליו ובשלש מאות האיש החזיק ומחנה מדין היה לו מתחת בעמק
9 A daren nan Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Tashi ka tafi sansaninsu domin zan ba da su a hannuwanka.
ויהי בלילה ההוא ויאמר אליו יהוה קום רד במחנה כי נתתיו בידך
10 In kana tsoron fāɗa musu, sai ka tafi da bawanka Fura
ואם ירא אתה לרדת--רד אתה ופרה נערך אל המחנה
11 ka kuma saurari abin da suke faɗi. Bayan haka za ka sami ƙarfin hali ka auka musu.” Saboda haka sai ya tafi tare da Fura bawansa zuwa sansanin.
ושמעת מה ידברו ואחר תחזקנה ידיך וירדת במחנה וירד הוא ופרה נערו אל קצה החמשים אשר במחנה
12 Midiyawa, Amalekawa da dukan sauran mutane gabashi suka yi sansani a kwari, kamar fāra. Raƙumansu kuma kamar yashi a bakin teku don sun wuce ƙirge.
ומדין ועמלק וכל בני קדם נפלים בעמק כארבה לרב ולגמליהם אין מספר כחול שעל שפת הים לרב
13 Gideyon ya iso daidai wani yana faɗa wa wani aboki mafarkinsa, yana cewa, “Na yi mafarki, na ga dunƙule burodin sha’ir ya fāɗo a tsakiyar sansanin Midiyawa. Ya bugi tentin da ƙarfin da ya sa tenti ta kife a ƙasa.”
ויבא גדעון--והנה איש מספר לרעהו חלום ויאמר הנה חלום חלמתי והנה צליל לחם שערים מתהפך במחנה מדין ויבא עד האהל ויכהו ויפל ויהפכהו למעלה ונפל האהל
14 Abokinsa ya ce, “Ai wannan ba wani abu ba ne fiye da takobin Gideyon ɗan Yowash, mutumin Isra’ila. Allah ya ba da Midiyawa da dukan sansani a hannuwansa.”
ויען רעהו ויאמר אין זאת בלתי אם חרב גדעון בן יואש איש ישראל נתן האלהים בידו את מדין ואת כל המחנה
15 Da Gideyon ya ji mafarkin da fassararsa, sai ya yi wa Allah sujada. Ya koma sansanin Isra’ila ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Ku tashi! Ubangiji ya ba da sansanin Midiyawa a hannuwanku.”
ויהי כשמע גדעון את מספר החלום ואת שברו--וישתחו וישב אל מחנה ישראל ויאמר קומו כי נתן יהוה בידכם את מחנה מדין
16 Ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho da tulu da acibalbal a ciki.
ויחץ את שלש מאות האיש שלשה ראשים ויתן שופרות ביד כלם וכדים ריקים ולפדים בתוך הכדים
17 Ya ce musu, “Ku dube ni, ku bi abin da na yi. Sa’ad da na kai sansanin, ku yi daidai abin da na yi.
ויאמר אליהם ממני תראו וכן תעשו והנה אנכי בא בקצה המחנה והיה כאשר אעשה כן תעשון
18 Sa’ad da ni da dukan waɗanda suke tare da ni muka busa ƙahoninmu, to, ko’ina a kewayen sansanin sai ku busa naku ku kuma yi ihu, ku ce, ‘Don Ubangiji da kuma domin Gideyon.’”
ותקעתי בשופר--אנכי וכל אשר אתי ותקעתם בשופרות גם אתם סביבות כל המחנה ואמרתם ליהוה ולגדעון
19 Gideyon da mutum ɗari da suke tare da shi suka kai sansanin da tsakar dare bayan an sauya matsara. Suka busa ƙahoninsu, suka farfashe tulunansu da suke hannuwansu.
ויבא גדעון ומאה איש אשר אתו בקצה המחנה ראש האשמרת התיכונה--אך הקם הקימו את השמרים ויתקעו בשופרות ונפוץ הכדים אשר בידם
20 Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka ɗauki acibalbal a hannuwansu na hagu da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama, sai suka yi ihu, “Takobi don Ubangiji da kuma don Gideyon!”
ויתקעו שלשת הראשים בשופרות וישברו הכדים ויחזיקו ביד שמאולם בלפדים וביד ימינם השופרות לתקוע ויקראו חרב ליהוה ולגדעון
21 Yayinda kowannensu ya tsaya a inda yake kewaye da sansanin, dukan Midiyawa suka fito da gudu, suna kuka yayinda suke gudu.
ויעמדו איש תחתיו סביב למחנה וירץ כל המחנה ויריעו ויניסו (וינוסו)
22 Sa’ad da aka busa ƙahonin nan ɗari uku sai Ubangiji ya sa Midiyawa suka yi ta saran juna. Mayaƙan suka gudu zuwa Bet-Shitta wajen Zerera har zuwa yankin Abel-Mehola kusa da Tabbat.
ויתקעו שלש מאות השופרות וישם יהוה את חרב איש ברעהו ובכל המחנה וינס המחנה עד בית השטה צררתה--עד שפת אבל מחולה על טבת
23 Aka kira dukan Isra’ilawa daga Naftali, Asher da dukan Manasse, suka kuwa fatattaki Midiyawa.
ויצעק איש ישראל מנפתלי ומן אשר ומן כל מנשה וירדפו אחרי מדין
24 Gideyon ya aiki manzanni zuwa dukan ƙasar tudu ta Efraim cewa, “Ku gangaro ku yaƙi Midiyawa ku ƙwace ruwan Urdun gaba da su har zuwa Bet-Bara.” Saboda haka aka kira dukan mutanen Efraim suka ƙwace ruwan Urdun har zuwa Bet-Bara.
ומלאכים שלח גדעון בכל הר אפרים לאמר רדו לקראת מדין ולכדו להם את המים עד בית ברה ואת הירדן ויצעק כל איש אפרים וילכדו את המים עד בית ברה ואת הירדן
25 Suka kuma kama shugabannin biyu na Midiyawa, Oreb da Zeyib suka kashe Oreb a dutsen Oreb, Zeyib kuma a wurin matsin ruwa inabin Zeyib. Suka fatattaki Midiyawa suka kawo kawunan Oreb da Zeba wurin Gideyon, wanda yake kusa da Urdun.
וילכדו שני שרי מדין את ערב ואת זאב ויהרגו את עורב בצור עורב ואת זאב הרגו ביקב זאב וירדפו אל מדין וראש ערב וזאב--הביאו אל גדעון מעבר לירדן

< Mahukunta 7 >