< Mahukunta 6 >

1 Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, sai ya ba da su ga Midiyawa shekara bakwai.
ויעשו בני ישראל הרע בעיני יהוה ויתנם יהוה ביד מדין שבע שנים
2 Da Midiyawa suka matsa musu sosai, sai Isra’ilawa suka yi wa kansu mafakai a rammukan duwatsu, kogona da kuma mafaka.
ותעז יד מדין על ישראל מפני מדין עשו להם בני ישראל את המנהרות אשר בהרים ואת המערות ואת המצדות
3 Duk lokacin da Isra’ilawa suka yi shuka sai Midiyawa da Amalekawa da waɗansu mutane daga gabashi sukan kai musu hari.
והיה אם זרע ישראל--ועלה מדין ועמלק ובני קדם ועלו עליו
4 Sukan yi sansani a ƙasar sun lalatar da hatsi har zuwa Gaza kuma ba sa barin wani abu mai rai wa Isra’ila, ko tumaki ko shanu ko jakuna.
ויחנו עליהם וישחיתו את יבול הארץ עד בואך עזה ולא ישאירו מחיה בישראל ושה ושור וחמור
5 Sukan zo da dabbobinsu da tentinsu kamar tarin fāri. Yana da wuya a ƙidaya yawan mutanen da kuma raƙumansu; sukan mamaye ƙasar don su lalatar da ita.
כי הם ומקניהם יעלו ואהליהם יבאו (ובאו) כדי ארבה לרב ולהם ולגמליהם אין מספר ויבאו בארץ לשחתה
6 Midiyawa suka talauce Isra’ilawa ƙwarai, har ya sa suka yi kuka ga Ubangiji don taimako.
וידל ישראל מאד מפני מדין ויזעקו בני ישראל אל יהוה
7 Sa’ad da Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji saboda Midiyawa,
ויהי כי זעקו בני ישראל אל יהוה על אדות מדין
8 sai ya aika musu da annabi, wanda ya ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce na fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta.
וישלח יהוה איש נביא אל בני ישראל ויאמר להם כה אמר יהוה אלהי ישראל אנכי העליתי אתכם ממצרים ואציא אתכם מבית עבדים
9 Na ƙwace ku daga ikon Masarawa da kuma daga dukan hannuwan masu danniya. Na kore su a gabanku na kuma ba ku ƙasarsu.
ואצל אתכם מיד מצרים ומיד כל לחציכם ואגרש אותם מפניכם ואתנה לכם את ארצם
10 Na ce muku, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku; kada ku bauta allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a ƙasarsu.’ Amma ba ku saurare ni ba.”
ואמרה לכם אני יהוה אלהיכם--לא תיראו את אלהי האמרי אשר אתם יושבים בארצם ולא שמעתם בקולי
11 Sai mala’ikan Ubangiji ya zo ya zauna a ƙarƙashin itacen oak a Ofra na Yowash mutumin Abiyezer, inda ɗansa Gideyon yake sussukar alkama a wurin matsin inabi don yă ɓoye daga Midiyawa.
ויבא מלאך יהוה וישב תחת האלה אשר בעפרה אשר ליואש אבי העזרי וגדעון בנו חבט חטים בגת להניס מפני מדין
12 Sa’ad da mala’ikan Ubangiji ya bayyana wa Gideyon, sai ya ce masa, “Ubangiji yana tare da kai, jarumi.”
וירא אליו מלאך יהוה ויאמר אליו יהוה עמך גבור החיל
13 Gideyon ya ce, “Ranka yă daɗe, in Ubangiji yana tare da mu, me ya sa waɗannan abubuwa suka faru da mu? Ina dukan abubuwan al’ajabinsa waɗanda kakanninmu suka gaya mana game su sa’ad da suka ce, ‘Ashe, ba Ubangiji ne ya fitar da mu daga Masar ba?’ Amma yanzu Ubangiji ya rabu da mu ya kuma sa mu hannun Midiyawa.”
ויאמר אליו גדעון בי אדני ויש יהוה עמנו ולמה מצאתנו כל זאת ואיה כל נפלאתיו אשר ספרו לנו אבותינו לאמר הלא ממצרים העלנו יהוה ועתה נטשנו יהוה ויתננו בכף מדין
14 Sai Ubangiji ya juya wajensa ya ce, “Ka je da ƙarfin da kake da shi ka ceci Isra’ila daga hannun Midiyawa. Ba Ni ne nake aikan ka ba?”
ויפן אליו יהוה ויאמר לך בכחך זה והושעת את ישראל מכף מדין הלא שלחתיך
15 Gideyon ya ce, “Amma Ubangiji, yaya zan iya ceci Isra’ila? Kabilata ce marar ƙarfi duka a Manasse, kuma ni ne ƙarami a iyalina.”
ויאמר אליו בי אדני במה אושיע את ישראל הנה אלפי הדל במנשה ואנכי הצעיר בבית אבי
16 Ubangiji ya ce, “Zan kasance tare da kai, za ka kuwa fatattake dukan Midiyawa gaba ɗaya.”
ויאמר אליו יהוה כי אהיה עמך והכית את מדין כאיש אחד
17 Gideyon ya ce, “In lalle na sami tagomashi a gabanka, to, ka ba ni wata alamar da ta nuna lalle kai kake magana da ni.
ויאמר אליו אם נא מצאתי חן בעיניך ועשית לי אות שאתה מדבר עמי
18 Ina roƙonka ka dakata har in komo in kawo maka hadayata in ajiye a gabanka.” Sai Ubangiji ya ce, “Zan jira har ka dawo.”
אל נא תמש מזה עד באי אליך והצאתי את מנחתי והנחתי לפניך ויאמר אנכי אשב עד שובך
19 Sai Gideyon ya shiga ciki, ya gyara’yar akuya ya dafa, da garin efa ya yi burodi marar yisti. Da ya sa naman a kwando, romon kuma a tukunya, sai ya fito da su waje ya miƙa masa su a ƙarƙashin itacen oak.
וגדעון בא ויעש גדי עזים ואיפת קמח מצות הבשר שם בסל והמרק שם בפרור ויוצא אליו אל תחת האלה ויגש
20 Mala’ikan Allah ya ce masa, “Ka ɗauko naman da burodi marar yisti ka sa su a kan wannan dutse, ka zuba romon a kai.” Gideyon kuwa ya yi haka.
ויאמר אליו מלאך האלהים קח את הבשר ואת המצות והנח אל הסלע הלז ואת המרק שפוך ויעש כן
21 Da kan sandan da yake a hannunsa, mala’ikan Ubangiji ya taɓa naman da burodi marar yistin. Sai wuta ta fito daga dutsen ta cinye naman da burodin. Mala’ikan kuwa ya ɓace.
וישלח מלאך יהוה את קצה המשענת אשר בידו ויגע בבשר ובמצות ותעל האש מן הצור ותאכל את הבשר ואת המצות ומלאך יהוה הלך מעיניו
22 Sa’ad da Gideyon ya gane mala’ikan Ubangiji ne, sai ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka! Na ga mala’ikan Ubangiji ido da ido.”
וירא גדעון כי מלאך יהוה הוא ויאמר גדעון אהה אדני יהוה--כי על כן ראיתי מלאך יהוה פנים אל פנים
23 Amma Ubangiji ya ce masa, “Salama! Kada ka ji tsoro, ba za ka mutu ba.”
ויאמר לו יהוה שלום לך אל תירא לא תמות
24 Saboda haka Gideyon ya gina wa Ubangiji bagade a can, ya kuma kira shi, Ubangiji Salama ne. Har wa yau bagaden yana a Ofra ta mutanen Abiyezer.
ויבן שם גדעון מזבח ליהוה ויקרא לו יהוה שלום עד היום הזה--עודנו בעפרת אבי העזרי
25 A wannan dare Ubangiji ya ce masa, “Ka ɗauki bijimi na biyu daga garken mahaifinka, wannan mai shekara bakwai. Ka rushe bagaden mahaifinka na Ba’al ka sare ginshiƙin Ashera kusa da ita.
ויהי בלילה ההוא ויאמר לו יהוה קח את פר השור אשר לאביך ופר השני שבע שנים והרסת את מזבח הבעל אשר לאביך ואת האשרה אשר עליו תכרת
26 Sa’an nan ka gina bagade irin da ya dace wa Ubangiji Allahnka a kan wannan tudu. Ka yi amfani da itacen katakon ginshiƙin Ashera da ka sare, ka miƙa bijiman nan biyu hadaya ta ƙonawa.”
ובנית מזבח ליהוה אלהיך על ראש המעוז הזה--במערכה ולקחת את הפר השני והעלית עולה בעצי האשרה אשר תכרת
27 Saboda haka Gideyon ya ɗebi bayinsa bakwai ya yi yadda Ubangiji ya ce masa. Amma saboda yana tsoron iyalinsa da mutanen gari, ya yi haka da dare a maimako da rana.
ויקח גדעון עשרה אנשים מעבדיו ויעש כאשר דבר אליו יהוה ויהי כאשר ירא את בית אביו ואת אנשי העיר מעשות יומם--ויעש לילה
28 Da safe sa’ad da mutanen garin suka tashi, sai suka tarar an rushe bagaden Ba’al, tare da ginshiƙin Ashera da yake kusa da shi, duk an sare, bijimi na biyu kuma aka miƙa hadaya a kan sabon bagaden!
וישכימו אנשי העיר בבקר והנה נתץ מזבח הבעל והאשרה אשר עליו כרתה ואת הפר השני העלה על המזבח הבנוי
29 Sai suka tambayi junansu, “Wa ya yi wannan?” Sa’ad da suka bincika a hankali, sai aka faɗa musu, “Gideyon ɗan Yowash ne ya yi haka.”
ויאמרו איש אל רעהו מי עשה הדבר הזה וידרשו ויבקשו--ויאמרו גדעון בן יואש עשה הדבר הזה
30 Mutanen garin suka ce wa Yowash, “Ka kawo mana ɗanka. Dole yă mutu, domin ya rushe bagaden Ba’al, ya sare ginshiƙin Asheran da yake tsaye kusa da shi.”
ויאמרו אנשי העיר אל יואש הוצא את בנך וימת כי נתץ את מזבח הבעל וכי כרת האשרה אשר עליו
31 Amma Yowash ya ce wa taron da suka tayar masa, “Za ku yi hamayya domin Ba’al ne? Kuna ƙoƙari ku cece shi ne? Duk wanda ya yi faɗa saboda shi za a kashe shi kafin safe. In lalle Ba’al allah ne, zai kāre kansa sa’ad da wani ya rushe bagadensa.”
ויאמר יואש לכל אשר עמדו עליו האתם תריבון לבעל אם אתם תושיעון אותו אשר יריב לו יומת עד הבקר אם אלהים הוא ירב לו כי נתץ את מזבחו
32 Saboda haka a ranar suka kira Gideyon, “Yerub-Ba’al,” suna cewa, “Bari Ba’al ya yi hamayya da shi,” domin ya rushe bagaden Ba’al.
ויקרא לו ביום ההוא ירבעל לאמר ירב בו הבעל כי נתץ את מזבחו
33 To, dukan Midiyawa, Amalekawa da sauran mutanen gabashi suka haɗa ƙarfi suka ƙetare Urdun suka kafa sansani a Kwarin Yezireyel.
וכל מדין ועמלק ובני קדם נאספו יחדו ויעברו ויחנו בעמק יזרעאל
34 Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko wa Gideyon, ya kuma busa ƙaho, ya kira mutanen Abiyezer su bi shi.
ורוח יהוה לבשה את גדעון ויתקע בשופר ויזעק אביעזר אחריו
35 Ya aika manzanni ko’ina a Manasse, yana kiransu su kintsa, haka ma Asher, Zebulun da Naftali, ta haka su ma suka haura su sadu da su.
ומלאכים שלח בכל מנשה ויזעק גם הוא אחריו ומלאכים שלח באשר ובזבלון ובנפתלי ויעלו לקראתם
36 Gideyon ya cewa Allah, “In za ka ceci Isra’ila ta hannuna yadda ka yi alkawari,
ויאמר גדעון אל האלהים אם ישך מושיע בידי את ישראל--כאשר דברת
37 to, zan shimfiɗa ulu a masussuka, inda safe akwai raɓa a kan ulun kaɗai, ƙasa kuwa a bushe, to, zan san cewa za ka ceci Isra’ila ta hannuna, yadda ka ce.”
הנה אנכי מציג את גזת הצמר--בגרן אם טל יהיה על הגזה לבדה ועל כל הארץ חרב--וידעתי כי תושיע בידי את ישראל כאשר דברת
38 Abin da faru ke nan. Gideyon ya tashi da sassafe kashegari, ya matse ulun ya kakkaɓe raɓar, ruwan ya cika ƙwarya.
ויהי כן--וישכם ממחרת ויזר את הגזה וימץ טל מן הגזה מלוא הספל מים
39 Sa’an nan Gideyon ya ce wa Allah, “Kada ka yi fushi da ni. Bari in ƙara yin wani gwaji kuma da ulun. A wannan lokaci ka sa ulun yă bushe, ƙasar kuma ta rufu da raɓa.”
ויאמר גדעון אל האלהים אל יחר אפך בי ואדברה אך הפעם אנסה נא רק הפעם בגזה--יהי נא חרב אל הגזה לבדה ועל כל הארץ יהיה טל
40 A wannan dare Allah ya yi haka. Ulun ne kaɗai yake a bushe, amma dukan ƙasar ta jiƙe da raɓa.
ויעש אלהים כן בלילה ההוא ויהי חרב אל הגזה לבדה ועל כל הארץ היה טל

< Mahukunta 6 >