< Mahukunta 4 >

1 Bayan rasuwar Ehud, Isra’ilawa suka sāke aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji.
And the children of Israel again did evil in the eyes of the Lord when Ehud was dead.
2 Saboda haka Ubangiji ya sayar da su ga Yabin sarkin Kan’ana wanda yake mulki a Hazor. Shugaban mayaƙansa shi ne Sisera, wanda yake zaune a Haroshet Haggoyim.
And the Lord gave them up into the hands of Jabin, king of Canaan, who was ruling in Hazor; the captain of his army was Sisera, who was living in Harosheth of the Gentiles.
3 Domin Yabin sarkin Kan’ana yana da kekunan yaƙin ƙarfe ɗari tara, ya ji wa Isra’ilawa ƙwarai har shekara ashirin, sai suka yi kuka ga Ubangiji, don taimako.
Then the children of Israel made prayer to the Lord; for he had nine hundred iron war-carriages, and for twenty years he was very cruel to the children of Israel.
4 A lokacin Debora annabiya, matar Laffidot ce take bi da Isra’ila.
Now Deborah, a woman prophet, the wife of Lapidoth, was judge of Israel at that time.
5 Takan yi zaman shari’a a ƙarƙashin Dabinon Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Efraim, Isra’ilawa kuwa sukan zo wurinta don tă yi musu shari’a.
(And she had her seat under the palm-tree of Deborah between Ramah and Beth-el in the hill-country of Ephraim; and the children of Israel came up to her to be judged.)
6 Sai ta aika a kira mata Barak ɗan Abinowam daga Kedesh a Naftali, ta ce masa, “Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce ka, ‘Je ka, ka ɗauki mutane Naftali da na Zebulun dubu goma tare da kai, ka yi jagoransu zuwa Dutse Tabor.
And she sent for Barak, the son of Abinoam, from Kedesh-naphtali, and said to him, Has not the Lord, the God of Israel, given orders saying, Go and get your force into line in Mount Tabor, and take with you ten thousand men of the children of Naphtali and of the children of Zebulun?
7 Zan jawo Sisera, shugaban mayaƙan Yabin, da keken yaƙinsa da mayaƙansa zuwa Kogin Kishon in ba da su a hannunku.’”
And I will make Sisera, the captain of Jabin's army, with his war-carriages and his forces, come against you at the river Kishon, where I will give him into your hands.
8 Barak ya ce, “In kika tafi tare da ni, zan tafi; amma in ba ki zo tare da ni ba, ba zan tafi ba.”
And Barak said to her, If you will go with me then I will go; but if you will not go with me I will not go.
9 Debora ta ce, “To, shi ke nan, zan tafi tare da kai. Amma saboda yadda ka ɗauki wannan batun, darajar ba za tă zama taka ba, gama Ubangiji zai ba da Sisera a hannun mace.” Saboda haka Debora ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh,
And she said, I will certainly go with you: though you will get no honour in your undertaking, for the Lord will give Sisera into the hands of a woman. So Deborah got up and went with Barak to Kedesh.
10 a can Barak ya kira Zebulun da Naftali. Mutum dubu goma suka kuma bi shi, Debora kuma tana tare da shi.
Then Barak sent for Zebulun and Naphtali to come to Kedesh; and ten thousand men went up after him, and Deborah went up with him.
11 To, Heber Bakene ya riga ya bar Keniyawa, zuriyar Hobab, ɗan’uwan matar Musa, ya kafa tentinsa wajen babban itace a Za’anannim kusa da Kedesh.
Now Heber the Kenite, separating himself from the rest of the Kenites, from the children of Hobab, the brother-in-law of Moses, had put up his tent as far away as the oak-tree in Zaanannim, by Kedesh.
12 Sa’ad da aka gaya wa Sisera cewa Barak ɗan Abinowam ya haura zuwa dutsen Tabor,
And word was given to Sisera that Barak, the son of Abinoam, had gone up to Mount Tabor.
13 sai Sisera ya tattara keken yaƙinsa na ƙarfe ɗari tara wuri ɗaya da dukan mutanen da suke tare da shi daga Haroshet Haggoyim zuwa Kogin Kishon.
So Sisera got together all his war-carriages, nine hundred war-carriages of iron, and all the people who were with him, from Harosheth of the Gentiles as far as the river Kishon.
14 Sa’an nan Debora ta ce wa Barak, “Je ka! Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da Sisera a hannunka. Ba Ubangiji ya riga ya sha gabanka?” Saboda haka Barak ya gangara zuwa Dutsen Tabor, da mutum dubu goma biye da shi.
Then Deborah said to Barak, Up! for today the Lord has given Sisera into your hands: has not the Lord gone out before you? So Barak went down from Mount Tabor and ten thousand men after him.
15 Da matsowar Barak, Ubangiji ya murƙushe Sisera da dukan sarakunansa da mayaƙansa da takobi, Sisera kuwa ya gudu da ƙafa ya bar keken yaƙinsa.
And the Lord sent fear on Sisera and all his war-carriages and all his army before Barak; and Sisera got down from his war-carriage and went in flight on foot.
16 Amma Barak ya bi keken yaƙin da mayaƙan har Haroshet Haggoyim. Aka karkashe dukan mayaƙan Sisera ba ko ɗayan da ya tsira.
But Barak went after the war-carriages and the army as far as Harosheth of the Gentiles; and all Sisera's army was put to the sword; not a man got away.
17 Amma Sisera, ya tsere da ƙafa zuwa tentin Yayel, matar Heber Bakene, domin suna da abokantaka da Yabin sarkin Hazor da kuma kabilar Heber Bakene.
But Sisera went in flight on foot to the tent of Jael, the wife of Heber the Kenite; for there was peace between Jabin, king of Hazor, and the family of Heber the Kenite.
18 Yayel ta fito ta taryi Sisera ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ka shigo, ka shigo ciki. Kada ka ji tsoro.” Saboda haka ya shiga cikin tentinta, sai ta rufe shi da bargo.
And Jael went out to Sisera, and said to him, Come in, my lord, come in to me without fear. So he went into her tent, and she put a cover over him.
19 Sai ya ce, “Ina roƙonki, ki ba ni ruwa in sha, ina jin ƙishirwa.” Sai ta buɗe salkar madara, ta ba shi ya sha, sai ta kuma rufe shi.
Then he said to her, Give me now a little water, for I have need of a drink. And opening a skin of milk, she gave him drink, and put the cover over him again.
20 Ya ce mata, “Ki tsaya a ƙofar tenti, in wani ya zo ya tambaye ki, ‘Akwai wani a nan?’ Ki ce masa ‘a’a.’”
And he said to her, Take your place at the door of the tent, and if anyone comes and says to you, Is there any man here, say, No.
21 Amma Yayel, matar Heber, ta ɗauki turken tenti da guduma ta tafi wurinsa da sauri sa’ad da yake barci saboda gajiya. Ta kafa masa turken a gindin kunnensa ta haɗa shi da ƙasa, har ya mutu.
Then Jael, Heber's wife, took a tent-pin and a hammer and went up to him quietly, driving the pin into his head, and it went through his head into the earth, for he was in a deep sleep from weariness; and so he came to his end.
22 Sai ga Barak mai bin sawun Sisera, Yayel kuwa ta fito don marabtarsa, ta ce, “Shigo, zan nuna maka mutumin da kake nema.” Saboda haka ya shiga ciki tare da ita, sai ga Sisera kwance da turken a gindin kunnensa, matacce.
Then Jael went out, and meeting Barak going after Sisera, said to him, Come, and I will let you see the man you are searching for. So he came into her tent and saw, and there was Sisera stretched out dead with the tent-pin in his head.
23 A ranar Allah ya yi kaca-kaca da Yabin, sarkin Kan’ana a gaban Isra’ila.
So that day God overcame Jabin, king of Canaan, before the children of Israel.
24 Isra’ilawa kuwa suka ƙara ƙarfi gāba da Yabin, sarkin Kan’aniyawa, har suka hallaka shi.
And the power of the children of Israel went on increasing against Jabin, king of Canaan, till he was cut off.

< Mahukunta 4 >