< Mahukunta 17 >
1 To, wani mutum mai suna Mika daga ƙasar tudu ta Efraim
2 ya ce wa mahaifiyarsa, “Shekel dubu ɗaya da ɗari ɗaya na azurfa da aka ɗauka daga gare ki wanda kuma ji kin furta la’ana a kai, azurfan yana wurina; ni ne na ɗauka.” Sa’an nan mahaifiyarsa ta ce, “Ubangiji yă albarkace ka ɗana!”
3 Sa’ad da ya mayar da azurfa dubu ɗaya da ɗari ɗaya na shekel wa mahaifiyarsa, sai ta ce, “Na ba da azurfata ga Ubangiji don ɗana yă sassaƙa sura yă kuma yi zubin gunki. Zan mayar maka.”
4 Saboda haka ya mayar da azurfan wa mahaifiyarsa, ita kuwa ta ɗauki azurfa ɗari biyu na shekel ta ba wa maƙeri, wanda ya mai da su sura da kuma gunki. Aka kuwa sa su a gidan Mika.
5 To, wannan mutum Mika yana da ɗakin gumaka, ya yi efod da waɗansu gumaka, ya kuma naɗa ɗaya daga cikin’ya’yansa firist nasa.
6 A kwanakin Isra’ila ba ta da sarki; kowa yana yin abin da ya ga dama.
7 Wani saurayi Balawe daga Betlehem a Yahuda, wanda yake zama cikin zuriyar Yahuda,
8 ya bar garin ya tafi neman inda zai zauna. A hanyarsa ya zo gidan Mika a ƙasar tudu ta Efraim.
9 Mika ya ce masa, “Daga ina kake?” Ya ce, “Ni Balawe ne daga Betlehem a Yahuda, ina kuwa neman wurin zauna ne.”
10 Sa’an nan Mika ya ce masa, “Ka zauna tare da ni ka zama mini mahaifi da firist, zan kuwa ba ka azurfa goma na shekel a shekara, tufafinka da kuma abincinka.” Sai Balawen ya tafi.
11 Saboda haka Balawen ya yarda ya zauna tare da shi, ɗan saurayin kuwa ya zama kamar ɗaya daga cikin’ya’yansa.
12 Sa’an nan Mika ya naɗa Balawen, saurayin kuwa ya zama masa firist ya kuma zauna a gidansa.
13 Mika ya ce, “Yanzu na san cewa Ubangiji zai yi mini alheri, da yake Balawen nan ya zama firist nawa.”