< Mahukunta 16 >

1 Wata rana Samson ya tafi Gaza, inda ya ga wata karuwa. Ya shiga wurinta ya kwana.
וילך שמשון עזתה וירא שם אשה זונה ויבא אליה
2 Aka gaya wa mutanen Gaza, “Ai, Samson yana a nan!” Saboda haka suka zo suka kewaye wurin suka yi kwanto dukan dare a bakin ƙofar birni. A daren nan ba su motsa nan da can ba, suna cewa, “Gari yana wayewa za mu kashe shi.”
לעזתים לאמר בא שמשון הנה ויסבו ויארבו לו כל הלילה בשער העיר ויתחרשו כל הלילה לאמר עד אור הבקר והרגנהו
3 Amma Samson ya yi kwanciyarsa har tsakiyar dare. Sa’an nan ya tashi ya kama ƙofofin birnin, tare da madogarai biyunsu, ya tumɓuke, ya aza su a kafaɗarsa, ya kai su kan dutsen da yake a fuskantar Hebron.
וישכב שמשון עד חצי הלילה ויקם בחצי הלילה ויאחז בדלתות שער העיר ובשתי המזזות ויסעם עם הבריח וישם על כתפיו ויעלם אל ראש ההר אשר על פני חברון
4 Bayan ɗan lokaci, sai ya shiga ƙaunar wata mace, mai suna Delila a Kwarin Sorek.
ויהי אחרי כן ויאהב אשה בנחל שרק ושמה דלילה
5 Sai shugabannin Filistiyawa suka tafi wurinta suka ce, “Ki yi ƙoƙari ki ga ko za ki rarrashe shi yă nuna miki asirin ƙarfinsa da yadda za mu iya shan ƙarfinsa don mu ɗaura shi mu yi nasara a kansa. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu ɗari ɗaya na azurfa.”
ויעלו אליה סרני פלשתים ויאמרו לה פתי אותו וראי במה כחו גדול ובמה נוכל לו ואסרנוהו לענותו ואנחנו נתן לך איש אלף ומאה כסף
6 Saboda haka Delila ta ce wa Samson, “Ka faɗa miki asirin ƙarfinka da yadda za a ɗaura ka a yi nasara a kanka.”
ותאמר דלילה אל שמשון הגידה נא לי במה כחך גדול ובמה תאסר לענותך
7 Samson ya ce mata, “In wani ya ɗaura ni da sababbin igiyoyin da ba su bushe ba, zan zama marar ƙarfi kamar kowa.”
ויאמר אליה שמשון אם יאסרני בשבעה יתרים לחים אשר לא חרבו--וחליתי והייתי כאחד האדם
8 Sa’an nan shugabannin Filistiyawa suka kawo mata sababbin igiyoyi guda bakwai da ba su bushe ba, sai ta daure shi da su.
ויעלו לה סרני פלשתים שבעה יתרים לחים--אשר לא חרבו ותאסרהו בהם
9 Da mutane a ɓoye a cikin ɗaki tare da ita, sai ta yi ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka!” Da jin haka sai ya tsintsinke igiyoyin kamar zaren da ya yi kusa da harshen wuta. Saboda haka asirin ƙarfinsa bai tonu ba.
והארב ישב לה בחדר ותאמר אליו פלשתים עליך שמשון וינתק את היתרים כאשר ינתק פתיל הנערת בהריחו אש ולא נודע כחו
10 Sa’an nan Delila ta ce wa Samson, “Ka mai da ni wawiya; ka ruɗe ni. Yanzu, ka gaya mini yadda za a daure ka.”
ותאמר דלילה אל שמשון הנה התלת בי ותדבר אלי כזבים עתה הגידה נא לי במה תאסר
11 Ya ce, “In wani ya ɗaura ni sosai da sababbin igiyoyin da ba a taɓa amfani da su ba, zan zama marar ƙarfi kamar kowa.”
ויאמר אליה--אם אסור יאסרוני בעבתים חדשים אשר לא נעשה בהם מלאכה וחליתי והייתי כאחד האדם
12 Saboda haka Delila ta ɗauki sababbin igiyoyi ta ɗaura shi da su. Sa’an nan, tare da mutane a ɓoye a ɗakin, ta yi ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka!” Amma sai ya tsintsinke su kamar zare.
ותקח דלילה עבתים חדשים ותאסרהו בהם ותאמר אליו פלשתים עליך שמשון והארב ישב בחדר וינתקם מעל זרעתיו כחוט
13 Sa’an nan Delila ta ce, “Har yanzu, ka mai da shashasha, kana mai da ni wawiya kana kuma yin mini ƙarya. Ka gaya mini yadda za a daure ka mana.” Ya ce mata, “In kin yi kitson gashin kaina guda bakwai kika ɗaura su da zare kika buga su da akwasha, zan rasa ƙarfi in zama kamar kowa.” Saboda haka yayinda yake barci, sai Delila ta yi kitson gashin kansa guda bakwai ta ɗinka su da zare,
ותאמר דלילה אל שמשון עד הנה התלת בי ותדבר אלי כזבים--הגידה לי במה תאסר ויאמר אליה--אם תארגי את שבע מחלפות ראשי עם המסכת
14 ta kuma ɗaura su da akwasha. Ta sāke yin ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka.” Ya tashi daga barcinsa ya tumɓuke akwashan tare da zaren da aka ɗaura gashin kansa da su.
ותתקע ביתד ותאמר אליו פלשתים עליך שמשון וייקץ משנתו ויסע את היתד הארג ואת המסכת
15 Sa’an nan ta ce masa, “Yaya kake cewa kana sona alhali ba ka yarda da ni ba? Wannan shi ne sau na uku kana mai da ni wawiya kuma ba ka nuna mini asirin ƙarfinka ba.”
ותאמר אליו איך תאמר אהבתיך ולבך אין אתי זה שלש פעמים התלת בי ולא הגדת לי במה כחך גדול
16 Da irin wannan fitina ta tsokane shi kwana da kwanaki har sai da ya gaji kamar zai mutu.
ויהי כי הציקה לו בדבריה כל הימים--ותאלצהו ותקצר נפשו למות
17 Saboda haka sai ya faɗa mata kome ya ce, “Ba a taɓa sa reza a kaina ba, domin ni Naziri ne keɓaɓɓe ga Allah tun haihuwa. In kuwa an aske kaina, ƙarfina zai rabu da ni, sai in zama kamar kowa.”
ויגד לה את כל לבו ויאמר לה מורה לא עלה על ראשי--כי נזיר אלהים אני מבטן אמי אם גלחתי וסר ממני כחי וחליתי והייתי ככל האדם
18 Da Delila ta gane ya gaya mata kome yanzu, sai ta aika saƙo zuwa ga shugabannin Filistiyawa ta ce, “Ku ƙara zuwa sau ɗayan nan, ai, ya gaya mini kome.” Saboda haka shugabannin Filistiyawa suka dawo tare da azurfa a hannuwansu.
ותרא דלילה כי הגיד לה את כל לבו ותשלח ותקרא לסרני פלשתים לאמר עלו הפעם כי הגיד לה (לי) את כל לבו ועלו אליה סרני פלשתים ויעלו הכסף בידם
19 Bayan ta sa shi ya yi barci a cinyarta, sai ta kira wani ya zo ya aske kitso guda bakwai nan a kansa, aka fara rinjayensa. Ƙarfinsa kuwa ya rabu da shi.
ותישנהו על ברכיה ותקרא לאיש ותגלח את שבע מחלפות ראשו ותחל לענותו ויסר כחו מעליו
20 Sa’an nan ta yi ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka!” Sai ya farka daga barci yana tsammani cewa, “Zan fita kamar dā in miƙe jikina.” Amma bai san cewa Ubangiji ya rabu da shi ba.
ותאמר פלשתים עליך שמשון ויקץ משנתו ויאמר אצא כפעם בפעם ואנער והוא לא ידע כי יהוה סר מעליו
21 Sa’an nan Filistiyawa suka fizge shi, suka ƙwaƙule idanunsa suka gangara da shi zuwa Gaza. Da suka daure shi da sarƙoƙin tagulla, sai aka sa shi yana niƙa a kurkuku.
ויאחזוהו פלשתים וינקרו את עיניו ויורידו אותו עזתה ויאסרוהו בנחשתים ויהי טוחן בבית האסירים (האסורים)
22 Amma gashi kansa ya fara tohuwa kuma bayan an aske shi.
ויחל שער ראשו לצמח כאשר גלח
23 To, sai Filistiyawa suka taru don su miƙa hadaya ga Dagon allahnsu su kuma yi biki cewa, “Allahnmu ya bashe abokin gābanmu Samson a hannuwanmu.”
וסרני פלשתים נאספו לזבח זבח גדול לדגון אלהיהם--ולשמחה ויאמרו--נתן אלהינו בידנו את שמשון אויבנו
24 Sa’ad da mutane suka gan shi, sai suka yabi allahnsu, suna cewa, “Allahnmu ya bashe abokin gābanmu a hannunmu, wanda ya lalace ƙasarmu ya kuma raɓanya kisan mutanenmu.”
ויראו אתו העם ויהללו את אלהיהם כי אמרו נתן אלהינו בידנו את אויבנו ואת מחריב ארצנו ואשר הרבה את חללינו
25 Yayinda suke cikin farin ciki, sai suka yi ihu, suka ce, “Fito mana da Samson yă yi mana wasa.” Saboda haka aka zo da Samson daga kurkuku, shi kuwa ya yi wasa a gabansu. Sa’ad da suka tsai da shi a tsakanin ginshiƙai,
ויהי כי טוב (כטוב) לבם ויאמרו קראו לשמשון וישחק לנו ויקראו לשמשון מבית האסירים (האסורים) ויצחק לפניהם ויעמידו אותו בין העמודים
26 sai Samson ya ce wa bawan da ya riƙe hannunsa, “Ka kai ni inda zan taɓa ginshiƙan da suke ɗauke da wannan haikali, don in jingina a kai.”
ויאמר שמשון אל הנער המחזיק בידו הניחה אותי והימשני (והמישני) את העמדים אשר הבית נכון עליהם ואשען עליהם
27 To, haikalin ya cika da mutane maza da mata; dukan shugabannin Filistiyawa kuwa suna a can, a bisan rufin kuwa akwai mutum wajen dubu uku maza da mata suna kallon Samson yana wasa.
והבית מלא האנשים והנשים ושמה כל סרני פלשתים ועל הגג כשלשת אלפים איש ואשה הראים בשחוק שמשון
28 Sa’an nan Samson ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, ya Allah ka tuna da ni, ka ƙarfafa ni sau ɗaya nan kaɗai, ka bar ni da bugu ɗaya kawai in ɗauki fansa a kan Filistiyawa domin idanuna.”
ויקרא שמשון אל יהוה ויאמר אדני יהוה זכרני נא וחזקני נא אך הפעם הזה האלהים ואנקמה נקם אחת משתי עיני מפלשתים
29 Sa’an nan Samson ya kai hannuwansa ga ginshiƙan waɗanda haikalin yake a kai, ya jingina jikinsa, hannunsa dama yana a ɗaya, hannun hagu kuma na ɗayan,
וילפת שמשון את שני עמודי התוך אשר הבית נכון עליהם ויסמך עליהם--אחד בימינו ואחד בשמאלו
30 Samson ya ce, “Bari in mutu tare da Filistiyawa!” Sa’an nan da dukan ƙarfinsa ya tura haikali ya fāɗa a kan shugabanni da dukan mutanen da suke ciki. Ta haka ya kashe mutane da yawa fiye da yayinda yake da rai.
ויאמר שמשון תמות נפשי עם פלשתים ויט בכח ויפל הבית על הסרנים ועל כל העם אשר בו ויהיו המתים אשר המית במותו רבים מאשר המית בחייו
31 Sa’an nan’yan’uwansa da dukan dangin mahaifinsa suka gangaro don su ɗauke shi. Suka kawo shi suka binne tsakanin Zora da Eshtawol a kabarin Manowa mahaifinsa. Ya yi mulkin Isra’ila shekara ashirin.
וירדו אחיו וכל בית אביהו וישאו אתו ויעלו ויקברו אותו בין צרעה ובין אשתאל בקבר מנוח אביו והוא שפט את ישראל עשרים שנה

< Mahukunta 16 >