< Mahukunta 14 >

1 Samson ya gangara zuwa Timna a can ya ga wata daga cikin’yan mata Filistiyawa.
那時三松下到提默納;在那裏見了一個女子,她是培肋舍特人的女兒。
2 Da ya komo, sai ya gaya wa mahaifinsa da mahaifiyarsa ya ce, “Na ga wata mace a Timna; ku auro mini ita ta zama matata.”
三松上去稟告他的父母說:「我在提默納見了一個女子,她是培肋舍特人的女兒,願你們現今把她給我娶來為妻! 」
3 Mahaifinsa da mahaifiyarsa suka ce, “Babu wata karɓaɓɓiyar yarinya a cikin zuriyarku ko cikin dukan mutanenmu ne? Dole ne ka tafi wajen Filistiyawa marasa kaciya ka nemi aure?” Amma Samson ya ce wa mahaifinsa, “A auro mini ita dai. Ita ta dace da ni.”
他的父母對他說:「難道在你兄弟的女兒中,在我們民族間沒有女子嗎﹖為什麼你要去從那些未受割損的培肋舍特人中間娶妻呢﹖」三松向他的父親說:「請給我娶了她! 因為我實在喜歡她。」
4 (Iyayensa ba su san cewa wannan daga wurin Ubangiji ne ba, wanda yake neman hanyar da za a kai wa Filistiyawa hari; gama a lokacin suna mulkin Isra’ila.)
他的父母原不知道這事是出於上主,使他找機會攻擊培肋舍特,因為那時培肋舍特正統治以色列。
5 Sai Samson ya gangara zuwa Timna tare da mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa. Da suka yi kusa da gonar inabin Timna, nan da nan sai ga ɗan zaki ya taso ya nufe shi yana ruri.
三松往提默納去,來到提默納的葡萄園時,看,有一隻小獅子向他咆哮;
6 Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa da ƙarfi, ya sa ya yaga zakin kashi biyu da hannu kamar yadda akan yayyage ɗan akuya. Sai dai bai gaya wa iyayensa abin da ya yi ba.
上主的神突然降在他身上,他當時雖赤手空拳,竟將那獅子撕裂,好像撕裂小山羊;他沒有把所作的這事告訴他的父母。
7 Sa’an nan ya gangara ya yi magana da yarinyar, yana kuwa sonsa.
此後他下去向那女子談情,三松很喜愛她。
8 Daga baya, da ya koma don yă aure ta, sai ya ratse don yă ga gawar zakin. Sai ga taron ƙudan zuma da zuma a ciki,
過了不久,回去娶她,繞路去看那隻死獅子。看,在獅子屍體內有一窩蜜蜂作了蜜。
9 wanda ya sa hannu ya ɗebo yana tafiya yana sha. Sa’ad da ya iso wurin iyayensa, ya ba su zuman, su ma suka sha. Sai dai bai gaya musu cewa ya ɗebo zuman daga gawar zaki ba.
他取了些蜜放在手中,繼續前行,一面走一面吃;來到他父母那裏,也給他們一些,他們也吃了,但他沒有告訴他們這蜜是從獅子屍體內取來的。
10 To, mahaifinsa ya gangara don yă ga yarinyar. Samson kuwa ya shirya wata liyafa a can, yadda yake bisa ga al’adar angwaye.
三松又來到那女子那裏,有人為他設了婚筵,因為青年人們慣常這樣做。
11 Sa’ad da ya bayyana, sai aka haɗa shi abokai talatin.
但有人害怕他,便請來三十個同伴陪伴他。
12 Sai Samson ya ce, “Bari in yi muku kacici-kacici, in kun ba ni amsa cikin kwana bakwai na wannan biki, zan ba ku riguna lilin talatin da kuma tufafi talatin.
三松對他們說:「讓我給你們說個謎語,如果你們能在這七天婚筵期內,給我猜出來,我就給你們三十件襯衫和三十套禮服。
13 In kuma ba ku iya ba ni amsar ba, dole ku ba ni rigunan lilin talatin da tufafi talatin.” Suka ce, “Ka gaya mana kacici-kacicin.”
若是你們不能給我解說,你們就得給我三十件襯衫和三十套禮服。」他們對他說:「請你把謎語講給我們聽。」
14 Sai ya ce, “Daga mai ci, abinci ya fito; daga mai ƙarfi, abu mai zaki ya fito.” Har kwana uku ba su iya ba da amsa ba.
他向他們說:「食者生出食品,強者生出甘甜。」他們三天之久不能解這謎語。
15 A rana ta huɗu suka ce wa matar Samson “Ki rarrashi mijinki yă bayyana mana kacici-kacicin, ko kuwa mu ƙone ki da gidan mahaifinki duka da wuta. Kun kira mu domin ku yi mana fashi ne?”
到了第四天,他們對三松的妻子說:「請引誘你的丈夫,把謎語說給你,以免我們放火燒你和你的父家。難道你請了我們來,是為了奪取我們的東西嗎﹖」
16 Sa’an nan matar Samson ta kwanta masa a jiki tana kuka tana cewa, “Kai maƙiyina ne, lalle ba ka ƙaunata, ka yi wa mutanena kacici-kacici, amma ba ka gaya mini amsar ba.” Ya amsa ya ce, “Ban ma bayyana wa mahaifina ko mahaifiyata ba, to, don me zan bayyana miki?”
三松的妻子就在他眼前哭哭啼啼說:「你是恨我,而不是愛我! 你給我的同胞說謎語,都不解給我聽。」三松對她說:「你看,我都沒有告訴我的父母,怎能告訴你﹖」
17 Ta yi ta kuka har kwana bakwai na bikin. Saboda haka a rana ta bakwai sai ya gaya mata, don ta dame shi. Ita kuwa ta bayyana kacici-kacicin wa mutanenta.
那七天婚筵期內,她常在他跟前哭哭啼啼;到了第七天,由於她不斷的催逼,三松便將謎底告訴了她;她就把謎底告訴自己的同胞。
18 Kafin rana ta fāɗi a rana ta bakwai mutane garin suka ce masa, “Me ya fi zuma zaki? Me ya fi zaki ƙarfi?” Samson ya ce musu, “Da ba don kun haɗa baki da matata ba, da ba za ku san amsar kacici-kacici ba.”
到了第七天,在他進洞房之前,本城的人給他說:「有什麼比蜜還甜﹖有什麼比獅子還強﹖」他向他們說:「你們若不是用我的小母牛耕田,你們決不會猜出我的謎底。」
19 Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko masa da iko. Sai ya fita ya gangara zuwa Ashkelon, ya kashe mutanensu talatin, ya kwashe kayansu ya kuma ba da rigunarsu ga waɗanda suka bayyana kacici-kacicin. Cike da fushi, ya haura zuwa gidan mahaifinsa.
上主的神又突然降在他身上,他就下到阿市刻隆,擊殺了三十個人,拿了所劫奪的東西,把三十套禮服送給猜中謎語的人;以後憤怒的回到父親家裏。
20 Aka kuma ɗauki matar Samson aka ba wa ɗaya daga cikin waɗanda suka yi masa hidima a bikin.
三松的妻子以後卻跟了作他伴郎的一個同伴。

< Mahukunta 14 >