< Mahukunta 12 >

1 Mutanen Efraim suka tattaro mayaƙansu, suka haye zuwa Zafon suka cewa Yefta, “Don me ka tafi ka yaƙi Ammonawa ba ka gayyace mu ba? Za mu ƙone gidanka a kanka.”
以法蓮人聚集,到了北方,對耶弗他說:「你去與亞捫人爭戰,為甚麼沒有招我們同去呢?我們必用火燒你和你的房屋。」
2 Yefta ya ce, “Ni da mutanena mun yi ta jayayya sosai da Ammonawa, ko da yake na kira ku, amma ba ku cece ni daga hannuwansu ba.
耶弗他對他們說:「我和我的民與亞捫人大大爭戰;我招你們來,你們竟沒有來救我脫離他們的手。
3 Da na ga ba za ku taimake ni ba, sai na yi kasai da raina na kuwa haye don in yaƙi Ammonawa, Ubangiji kuwa ya ba ni nasara a kansu. To, don me kuka zo yau don ku yaƙe ni?”
我見你們不來救我,我就拚命前去攻擊亞捫人,耶和華將他們交在我手中。你們今日為甚麼上我這裏來攻打我呢?」
4 Sa’an nan Yefta ya tara mutanen Gileyad wuri guda ya kuma yaƙi Efraim. Mutanen Gileyad suka fatattake su domin mutanen Efraim sun ce, “Ku Mutanen Gileyad masu neman mafaka ne cikin Efraim da Manasse.”
於是耶弗他招聚基列人,與以法蓮人爭戰。基列人擊殺以法蓮人,是因他們說:「你們基列人在以法蓮、瑪拿西中間,不過是以法蓮逃亡的人。」
5 Mutanen Gileyad suka ƙwace mashigan Urdun masu zuwa Efraim, duk sa’ad da wani daga Efraim da ya tsira ya ce, “Bari in haye,” sai mutane Gileyad su ce “Kai mutumin Efraim ne?” In ya ce, “A’a,”
基列人把守約旦河的渡口,不容以法蓮人過去。以法蓮逃走的人若說:「容我過去。」基列人就問他說:「你是以法蓮人不是?」他若說:「不是」,
6 sai su ce, “To, ka ce, ‘Shibbolet.’” In ya ce, “Sibbolet,” saboda ba sa iya faɗin kalmar daidai, sai su kama shi su kashe a mashigan Urdun. Aka kashe mutanen Efraim dubu arba’in da biyu a ta haka.
就對他說:「你說『示播列』。」以法蓮人因為咬不真字音,便說「西播列」。基列人就將他拿住,殺在約旦河的渡口。那時以法蓮人被殺的有四萬二千人。
7 Yefta ya shugabanci Isra’ila shekara shida. Sa’an nan Yefta mutumin Gileyad ya mutu, aka kuwa binne shi wani gari a Gileyad.
耶弗他作以色列的士師六年。基列人耶弗他死了,葬在基列的一座城裏。
8 Bayansa, Ibzan mutumin Betlehem, ya shugabanci Isra’ila.
耶弗他以後,有伯利恆人以比讚作以色列的士師。
9 Yana’ya’ya maza talatin da’ya’ya mata talatin. Ya ba da auren’ya’yansa mata ga waɗanda ba daga dangi ba, ga’ya’yansa maza kuwa ya kawo’yan mata talatin su zama matansu waje da danginsa. Ibzan ya shugabanci Isra’ila shekara bakwai.
他有三十個兒子,三十個女兒;女兒都嫁出去了。他給眾子從外鄉娶了三十個媳婦。他作以色列的士師七年。
10 Sa’an nan Ibzan ya mutu, aka kuwa binne shi Betlehem.
以比讚死了,葬在伯利恆。
11 Bayansa, Elon mutumin Zebulun, ya shugabanci Isra’ila shekara goma.
以比讚之後,有西布倫人以倫,作以色列的士師十年。
12 Sa’an nan Elon ya mutu, aka kuwa binne shi a Aiyalon a ƙasar Zebulun.
西布倫人以倫死了,葬在西布倫地的亞雅崙。
13 Bayansa, Abdon ɗan Hillel, daga Firaton, ya shugabanci Isra’ila.
以倫之後,有比拉頓人希列的兒子押頓作以色列的士師。
14 Yana da’ya’ya maza arba’in da’yan taɓa kunne talatin, waɗanda suka hau jakuna saba’in. Ya shugabanci Isra’ila shekara takwas.
他有四十個兒子,三十個孫子,騎着七十匹驢駒。押頓作以色列的士師八年。
15 Sa’an nan Abdon ɗan Hillel ya mutu, aka kuwa binne shi a Firaton a Efraim, a ƙasar tudu ta Amalekawa.
比拉頓人希列的兒子押頓死了,葬在以法蓮地的比拉頓,在亞瑪力人的山地。

< Mahukunta 12 >