< Mahukunta 10 >
1 Bayan zamanin Abimelek, sai Tola ɗan Fuwa ɗan Dodo daga Issakar ya tashi don yă ceci Isra’ila. Yana zama a Shamir a ƙasar tudu ta Efraim.
阿彼默肋客之後,有依撒加爾人多多的孫子,普阿的兒子托拉起來整救以色列。他住在厄弗辣因山地的沙米爾,
2 Ya shugabanci Isra’ila shekara ashirin da uku sa’an nan ya mutu, aka kuma binne shi a Shamir.
做以色列民長有二十三年之久,死後葬在紗米爾。雅依爾民長
3 Bayansa kuma sai Yayir daga Gileyad, wanda ya shugabanci Isra’ila shekara ashirin da biyu.
在他以後,有基肋阿得人雅依爾興起,作以色列民長二十二年之久。
4 Yana’ya’ya talatin, waɗanda suke hawan jakuna talatin. Sun shugabanci birane talatin a Gileyad, har wa yau ana ce da biranen Hawwot Yayir.
他有三十個兒子,騎著三十四驢駒;他們有三十座城,這些城稱作哈沃特雅依爾,直到今日,都在基肋阿得地。
5 Sa’ad da Yayir ya mutu, sai aka binne shi a Kamon.
雅依爾死後埋葬在卡孟。以民犯罪受罰
6 Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji. Suka shiga bautar Ba’al da Ashtarot, da kuma allolin Aram, allolin Sidon, allolin Mowab, Ammonawa da kuma allolin Filistiyawa. Kuma domin Isra’ilawa sun bar Ubangiji ba su ƙara bauta masa ba,
那時以色列子民又行了上主視為惡的事,事奉巴耳和阿市托勒特眾神,以及阿蘭的神,漆冬的神,摩阿布的神,阿孟子民的神,培肋舍特人的神;他們背棄上主,不事奉他。
7 sai ya fusata da su. Ya sayar da su ga hannun Filistiyawa da Ammonawa,
上主向以色列發怒,把他們交在培肋舍特人和阿孟子民手中。
8 waɗanda suka fatattake su a shekarar suka kuma ragargaza su. Shekara goma sha takwas suka yi ta danne dukan Isra’ilawan da suke gabashin Urdun a Gileyad, ƙasar Amoriyawa.
從那一年起,他們迫害壓制以色列子民,即所有住在約但河對岸,在阿摩黎人境內基肋阿得地方的以色列子民,一連十八年。
9 Ammonawa su ma suka haye Urdun domin su yi yaƙi da Yahuda, Benyamin da kuma gidan Efraim; Isra’ila kuwa suka kasance cikin wahala ƙwarai da gaske.
阿孟子民也過約但河來攻擊猷大、本雅明和厄弗辣因家族;因此以色列人很是困苦。
10 Sa’an nan Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, suka ce, “Mun yi maka zunubi, mun bar Allahnmu muka shiga bautar Ba’al.”
以色列子民遂向上主呼籲說:「我們得罪了你,因為我們背棄了我們的天主,事奉了巴耳諸神! 」
11 Ubangiji ya ce, “Sa’ad da Masarawa, Amoriyawa, Ammonawa, Filistiyawa,
上主對以色列子民說:「當埃及人、阿摩黎人、阿孟子民、培肋舍特人、
12 Sidoniyawa, Amalekawa da kuma mutanen Mawon suka wulaƙanta ku kuka kuwa yi mini kuka, ban cece ku daga hannunsu ba?
漆冬人、阿瑪肋人、米德楊人難為你們的時後,你們向我哀號,我豈沒有從他們手中拯救了你們﹖
13 Amma kuka bar ni kuka bauta wa waɗansu alloli, saboda haka ni ma ba zan ƙara cece ku ba.
但是你們背棄了我,事奉了別的神,因此我不再拯救你們,
14 Ku tafi ku yi wa allolin da kuka zaɓa. Bari su cece ku sa’ad da kuke cikin wahala!”
去呼籲你們所選擇的神罷! 讓他們在你們遭難時來拯救你們! 」
15 Amma Isra’ilawa suka ce wa Ubangiji, “Mu dai mun yi zunubi. Ka yi da mu abin da ka ga dama, amma muna roƙonka ka cece mu a yanzu.”
以色列子民對上主說:「我們犯了罪,你任意對待我們,只求你今日援救我們! 」
16 Sa’an nan suka zubar da allolin nan daga cikinsu suka bauta wa Ubangiji. Ubangiji kuwa bai ƙara daure da azabar da Isra’ila suke sha ba.
以色列子民遂從他們中間除去外邦的神,而事奉上主;上主再不能容忍以色列受苦。
17 Sa’ad da aka kira Ammonawa su yi ɗamarar yaƙi, sai su kuma kafa sansani a Gileyad, Isra’ilawa kuwa suka tattaru suka kafa sansani Mizfa.
那時阿孟子民集合在基肋阿得紮營,以色列子民也集合在米茲帕安營。
18 Shugabannin mutanen Gileyad suka cewa juna, “Duk wanda zai fara fāɗa wa Ammonawa shi zai zama shugaban duk waɗanda suke zama a Gileyad.”
基肋阿得人民的首領彼此說:「誰開始攻打阿孟子民,誰就作全基肋阿得居民的首領。」