< Yahuda 1 >

1 Yahuda, bawan Yesu Kiristi, ɗan’uwan Yaƙub, Zuwa ga waɗanda aka kira, waɗanda Allah Uba yake ƙauna, waɗanda kuma Yesu Kiristi ya kiyaye.
イエス・キリストの僕またヤコブの兄弟であるユダから、父なる神に愛され、イエス・キリストに守られている召された人々へ。
2 Jinƙai, salama da kuma ƙauna, su kasance tare da ku a yalwace.
あわれみと平安と愛とが、あなたがたに豊かに加わるように。
3 Abokaina ƙaunatattu, ko da yake na yi marmari ƙwarai in rubuta muku game da ceton nan namu, sai na ga ya dace in rubuta, in gargaɗe ku ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya wadda aka danƙa wa mutane masu tsarki na Allah sau ɗaya tak.
愛する者たちよ。わたしたちが共にあずかっている救について、あなたがたに書きおくりたいと心から願っていたので、聖徒たちによって、ひとたび伝えられた信仰のために戦うことを勧めるように、手紙をおくる必要を感じるに至った。
4 Na faɗa haka ne domin waɗansu mutanen da aka rubuta hukuncinsu tun dā sun shiga cikinku a ɓoye. Su fa marasa tsoron Allah ne. Su ne waɗanda suka mai da alherin Allahnmu ya zama dalilin yin fasikanci, suna kuma mūsun Yesu Kiristi wanda shi ne Makaɗaici Mai Iko Duka da kuma Ubangijinmu.
そのわけは、不信仰な人々がしのび込んできて、わたしたちの神の恵みを放縦な生活に変え、唯一の君であり、わたしたちの主であるイエス・キリストを否定しているからである。彼らは、このようなさばきを受けることに、昔から予告されているのである。
5 Ko da yake kun riga kun san duk wannan, ina so in tuna muku cewa Ubangiji ya ceci mutanensa daga Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba.
あなたがたはみな、じゅうぶんに知っていることではあるが、主が民をエジプトの地から救い出して後、不信仰な者を滅ぼされたことを、思い起してもらいたい。
6 Haka ma mala’ikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba, waɗanda suka bar ainihin mazauninsu, su ne ya tsare a duhu daure da dawwammamun sarƙoƙi don hukunci ta babbar Ranan nan. (aïdios g126)
主は、自分たちの地位を守ろうとはせず、そのおるべき所を捨て去った御使たちを、大いなる日のさばきのために、永久にしばりつけたまま、暗やみの中に閉じ込めておかれた。 (aïdios g126)
7 Haka ma Sodom da Gomorra da garuruwan da suke kewaye da su, waɗanda su ma suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar sha’awar jiki, sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta. (aiōnios g166)
ソドム、ゴモラも、まわりの町々も、同様であって、同じように淫行にふけり、不自然な肉欲に走ったので、永遠の火の刑罰を受け、人々の見せしめにされている。 (aiōnios g166)
8 Haka yake da masu mafarke-mafarken nan, gama sun ƙazantar da jikunansu, suka ƙi bin masu mulki, suna ɓata sunan talikan sararin sama.
しかし、これと同じように、これらの人々は、夢に迷わされて肉を汚し、権威ある者たちを軽んじ、栄光ある者たちをそしっている。
9 Kai, ko Mika’ilu babban shugaban mala’iku ma, sa’ad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka!”
御使のかしらミカエルは、モーセの死体について悪魔と論じ争った時、相手をののしりさばくことはあえてせず、ただ、「主がおまえを戒めて下さるように」と言っただけであった。
10 Duk da haka mutanen nan suna maganar banza a kan kome da ba su gane ba; kuma abubuwan da suka fahimta bisa ga jiki, kamar dabbobi marasa hankali, waɗannan abubuwa ne suke hallaka su.
しかし、この人々は自分が知りもしないことをそしり、また、分別のない動物のように、ただ本能的な知識にあやまられて、自らの滅亡を招いている。
11 Kaitonsu! Gama sun kama hanyar Kayinu; sun ruga a guje garin neman riba cikin kuskure kamar Bala’am; aka kuma hallaka su cikin tawayen Kora.
彼らはわざわいである。彼らはカインの道を行き、利のためにバラムの惑わしに迷い入り、コラのような反逆をして滅んでしまうのである。
12 Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus.
彼らは、あなたがたの愛餐に加わるが、それを汚し、無遠慮に宴会に同席して、自分の腹を肥やしている。彼らは、いわば、風に吹きまわされる水なき雲、実らない枯れ果てて、抜き捨てられた秋の木、
13 Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada. (aiōn g165)
自分の恥をあわにして出す海の荒波、さまよう星である。彼らには、まっくらなやみが永久に用意されている。 (aiōn g165)
14 Enok ma, wanda yake na bakwai daga Adamu, ya yi annabci game da waɗannan mutane cewa, “Duba, Ubangiji yana zuwa da dubu dubban tsarkakansa
アダムから七代目にあたるエノクも彼らについて預言して言った、「見よ、主は無数の聖徒たちを率いてこられた。
15 don yă yi wa kowa shari’a, yă kuma hukunta duk marasa tsoron Allah game da dukan ayyukansu na rashin tsoron Allah da suka aikata ta hanyar rashin tsoron Allah, da kuma dukan baƙaƙen kalmomin da masu zunubi marasa tsoron Allah suka faɗa game da shi.”
それは、すべての者にさばきを行うためであり、また、不信心な者が、信仰を無視して犯したすべての不信心なしわざと、さらに、不信心な罪人が主にそむいて語ったすべての暴言とを責めるためである」。
16 Waɗannan mutane dai, gunaguni gare su, kullum ganin laifin waɗansu suke yi. Muguwar sha’awa ce kaɗai tunaninsu. Sun cika da banzar magana ta yabon kansu. Suna ruɗin mutane da zaƙin baki don samun ribar kansu.
彼らは不平をならべ、不満を鳴らす者であり、自分の欲のままに生活し、その口は大言を吐き、利のために人にへつらう者である。
17 Amma ku abokaina ƙaunatattu, ku tuna da abin da manzannin Ubangijinmu Yesu Kiristi suka faɗa a dā.
愛する者たちよ。わたしたちの主イエス・キリストの使徒たちが予告した言葉を思い出しなさい。
18 Sun ce muku, “A kwanakin ƙarshe za a kasance da masu ba’a waɗanda za su bi sha’awace-sha’awacensu na rashin tsoron Allah.”
彼らはあなたがたにこう言った、「終りの時に、あざける者たちがあらわれて、自分の不信心な欲のままに生活するであろう」。
19 Waɗannan mutanen ne, suke kawo rabe-rabe, masu bin abin da jiki yake so, marasa Ruhu.
彼らは分派をつくる者、肉に属する者、御霊を持たない者たちである。
20 Amma ku, abokaina ƙaunatattu, ku gina kanku cikin bangaskiyarku mafi tsarki, ku kuma yi addu’a cikin Ruhu Mai Tsarki.
しかし、愛する者たちよ。あなたがたは、最も神聖な信仰の上に自らを築き上げ、聖霊によって祈り、
21 Ku zauna cikin ƙaunar Allah yayinda kuke jira jinƙan Ubangijinmu Yesu Kiristi don yă kawo ku ga rai madawwami. (aiōnios g166)
神の愛の中に自らを保ち、永遠のいのちを目あてとして、わたしたちの主イエス・キリストのあわれみを待ち望みなさい。 (aiōnios g166)
22 Ku ji tausayin waɗanda suke shakka;
疑いをいだく人々があれば、彼らをあわれみ、
23 ku cece waɗansu ta wurin fizge su daga wuta. Ga waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro, har ma ku yi ƙyamar tufafin da suka ɓata da ayyukansu na jiki.
火の中から引き出して救ってやりなさい。また、そのほかの人たちを、おそれの心をもってあわれみなさい。しかし、肉に汚れた者に対しては、その下着さえも忌みきらいなさい。
24 To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki.
あなたがたを守ってつまずかない者とし、また、その栄光のまえに傷なき者として、喜びのうちに立たせて下さるかた、
25 Gare shi kuma, shi da yake kaɗai Allah Mai Cetonmu, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, tun farkon zamanai, yanzu, da har abada abadin! Amin. (aiōn g165)
すなわち、わたしたちの救主なる唯一の神に、栄光、大能、力、権威が、わたしたちの主イエス・キリストによって、世々の初めにも、今も、また、世々限りなく、あるように、アァメン。 (aiōn g165)

< Yahuda 1 >