< Yoshuwa 9 >

1 To, sa’ad da dukan sarakunan yammancin Urdun suka ji waɗannan abubuwa, sai waɗanda suke kan tudu, da na cikin kwari a yammanci, da dukan waɗanda suke gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon (sarakunan Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa)
ויהי כשמע כל המלכים אשר בעבר הירדן בהר ובשפלה ובכל חוף הים הגדול אל מול הלבנון--החתי והאמרי הכנעני הפרזי החוי והיבוסי
2 suka haɗa kansu don su yaƙi Yoshuwa da Isra’ila.
ויתקבצו יחדו להלחם עם יהושע ועם ישראל--פה אחד
3 Amma da mutanen Gibeyon suka ji abin da Yoshuwa ya yi wa Yeriko da Ai,
וישבי גבעון שמעו את אשר עשה יהושע ליריחו--ולעי
4 sai suka shirya wata dabara ta ruɗu, suka shirya ɗan abinci don tafiya, suka ɗauki tsofaffin buhuna a kan jakunansu da tsofaffin salkuna na ruwan inabi, yagaggu da suka sha ɗinki.
ויעשו גם המה בערמה וילכו ויצטירו ויקחו שקים בלים לחמוריהם ונאדות יין בלים ומבקעים ומצררים
5 Suka sa tsofaffin takalman da suka sha gyara, suka sa tsofaffin tufafi. Dukan abincinsu na tafiya ya bushe ya yi fumfuna.
ונעלות בלות ומטלאות ברגליהם ושלמות בלות עליהם וכל לחם צידם יבש היה נקדים
6 Sai suka je wurin Yoshuwa a sansanin Gilgal suka ce masa da mutanen Isra’ila, “Daga ƙasa mai nisa muka fito, yanzu fa, sai ku yi alkawari da mu.”
וילכו אל יהושע אל המחנה הגלגל ויאמרו אליו ואל איש ישראל מארץ רחוקה באנו ועתה כרתו לנו ברית
7 Mutanen Isra’ila kuwa suka ce wa Hiwiyawa, “Wataƙila kuna kusa da mu, ta yaya za mu yi alkawari da ku?”
ויאמרו (ויאמר) איש ישראל אל החוי אולי בקרבי אתה יושב ואיך אכרות (אכרת) לך ברית
8 Suka ce wa Yoshuwa, “Mu bayinku ne.” Amma Yoshuwa ya tambaye su ya ce, “Ku wane ne, kuma daga ina kuka zo?”
ויאמרו אל יהושע עבדיך אנחנו ויאמר אליהם יהושע מי אתם ומאין תבאו
9 Suka amsa suka ce, “Bayinka sun zo ne daga ƙasa mai nisa gama Ubangiji Allahnka ya yi suna sosai. Gama mun ji labarin abubuwan da ya yi. Dukan abubuwan da ya yi a Masar
ויאמרו אליו מארץ רחוקה מאד באו עבדיך לשם יהוה אלהיך כי שמענו שמעו ואת כל אשר עשה במצרים
10 da kuma duk abubuwan da ya yi wa sarakuna biyu na Amoriyawa gabas da Urdun, Sihon sarkin Heshbon, da Og sarkin Bashan wanda ya yi mulki a Ashtarot.
ואת כל אשר עשה לשני מלכי האמרי אשר בעבר הירדן--לסיחון מלך חשבון ולעוג מלך הבשן אשר בעשתרות
11 Dattawanmu da duk mazaunan ƙasar, suka ce mana, ‘Ku ɗauki abincin tafiyar da za ku riƙe; ku je ku same su ku ce musu, “Mu bayinku ne, ku yi alkawari da mu.”’
ויאמרו אלינו זקינינו וכל ישבי ארצנו לאמר קחו בידכם צידה לדרך ולכו לקראתם ואמרתם אליהם עבדיכם אנחנו ועתה כרתו לנו ברית
12 Abincin tafiyan nan namu yana da ɗumi lokacin da muka kintsa tashi daga gida a ranar da za mu kama hanya zuwa wurinku. Amma yanzu duba yadda ya bushe, ya yi fumfuna.
זה לחמנו חם הצטידנו אתו מבתינו ביום צאתנו ללכת אליכם ועתה הנה יבש והיה נקדים
13 Waɗannan salkuna kuma da muka cika ruwan inabi, sababbi ne amma duba yadda suka yayyage. Tufafinmu da takalmanmu duk sun yayyage don doguwar tafiya.”
ואלה נאדות היין אשר מלאנו חדשים והנה התבקעו ואלה שלמותינו ונעלינו בלו מרב הדרך מאד
14 Mutanen Isra’ila suka ɗiba daga cikin abincin tafiyar amma ba su nemi nufin Ubangiji ba.
ויקחו האנשים מצידם ואת פי יהוה לא שאלו
15 Sa’an nan Yoshuwa ya yi alkawari zaman salama da su, cewa ba zai kashe su ba, sai shugabannin mutanen Isra’ila kuwa suka tabbatar musu da haka ta wurin yin rantsuwa.
ויעש להם יהושע שלום ויכרת להם ברית לחיותם וישבעו להם נשיאי העדה
16 Kwana uku bayan sun yi alkawari da Gibeyonawa, sai Isra’ilawa suka ji cewa Gibeyonawa maƙwabtansu ne, waɗanda suke zaune kurkusa da su.
ויהי מקצה שלשת ימים אחרי אשר כרתו להם ברית וישמעו כי קרבים הם אליו ובקרבו הם ישבים
17 Saboda haka Isra’ilawa suka tashi a rana ta uku suke je biranen mutanen, wato, Gibeyon, Kefira, Beyerot da Kiriyat Yeyarim.
ויסעו בני ישראל ויבאו אל עריהם--ביום השלישי ועריהם גבעון והכפירה ובארות וקרית יערים
18 Amma Isra’ilawa ba su kai musu hari ba domin shugabanninsu sun rantse musu da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila. Mutane Isra’ila duka kuwa suka yi gunaguni a kan shugabannin.
ולא הכום בני ישראל כי נשבעו להם נשיאי העדה ביהוה אלהי ישראל וילנו כל העדה על הנשיאים
19 Amma shugabanni suka amsa musu suka ce, “Mun rantse musu da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, saboda haka ba za mu taɓa su ba yanzu.
ויאמרו כל הנשיאים אל כל העדה אנחנו נשבענו להם ביהוה אלהי ישראל ועתה לא נוכל לנגע בהם
20 Ga abin da za mu yi musu, za mu bar su da rai don kada fushin Allah yă sauka a kanmu gama mun riga mun rantse musu.”
זאת נעשה להם והחיה אותם ולא יהיה עלינו קצף על השבועה אשר נשבענו להם
21 Suka ƙara da cewa, “Mu bar su da rai, amma bari su zama masu yankan itace da masu ɗibo mana ruwa.” Haka shugabannin suka cika alkawarinsu.
ויאמרו אליהם הנשיאים יחיו ויהיו חטבי עצים ושאבי מים לכל העדה כאשר דברו להם הנשיאים
22 Yoshuwa kuwa ya aika aka kira Gibeyonawa ya ce musu, “Don me kuka ruɗe mu kuka ce, ‘Mun zo ne daga wuri mai nisa,’ bayan kuwa kuna nan kurkusa da mu?
ויקרא להם יהושע וידבר אליהם לאמר למה רמיתם אתנו לאמר רחוקים אנחנו מכם מאד ואתם בקרבנו ישבים
23 Yanzu ku la’anannu ne. Ba za ku daina zama mana masu yankan itace da kuma masu ɗebo ruwa domin haikalin Allahnmu ba.”
ועתה ארורים אתם ולא יכרת מכם עבד וחטבי עצים ושאבי מים--לבית אלהי
24 Suka amsa wa Yoshuwa suka ce, “An gaya wa bayinka dalla-dalla yadda Ubangiji Allahnka ya umarci bawansa Musa yă ba ka ƙasar duka, ka kuma kashe duk masu zama a cikinta, muka ji tsoro cewa za ka kashe mu shi ya sa muka yi haka.
ויענו את יהושע ויאמרו כי הגד הגד לעבדיך את אשר צוה יהוה אלהיך את משה עבדו לתת לכם את כל הארץ ולהשמיד את כל ישבי הארץ מפניכם ונירא מאד לנפשתינו מפניכם ונעשה את הדבר הזה
25 Yanzu, a hannunka muke, ka yi duk abin da ka ga ya yi maka kyau.”
ועתה הננו בידך כטוב וכישר בעיניך לעשות לנו עשה
26 Yoshuwa kuwa ya cece su daga hannun Isra’ilawa, har ba su kashe su ba.
ויעש להם כן ויצל אותם מיד בני ישראל ולא הרגום
27 A ranar Yoshuwa ya sa Gibeyonawa suka zama masu yankan itace da ɗebo ruwa wa jama’ar Isra’ila da kuma domin haikalin Ubangiji a inda Ubangiji zai zaɓa. Abin da suke ke nan har wa yau.
ויתנם יהושע ביום ההוא חטבי עצים ושאבי מים--לעדה ולמזבח יהוה עד היום הזה אל המקום אשר יבחר

< Yoshuwa 9 >