< Yoshuwa 3 >
1 Kashegari Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Shittim suka nufi Urdun inda suka sauka kafin su haye.
여호수아가 아침에 일찌기 일어나서 이스라엘 사람들로 더불어 싯딤에서 떠나 요단에 이르러서는 건너지 아니하고 거기서 유숙하니라
2 Bayan kwana uku sai shugabannin suka zazzaga sansani, suna
삼일 후에 유사들이 진중으로 두루 다니며
3 ba da umarni ga mutane, suna cewa, “Lokacin da kuka ga akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku, da firistoci waɗanda su ne Lawiyawa, suna ɗauke da shi, sai ku tashi daga inda kuke, ku bi shi.
백성에게 명하여 가로되 `너희는 레위 사람 제사장들이 너희 하나님 여호와의 언약궤 메는 것을 보거든 너희 곳을 떠나 그 뒤를 좇으라
4 A ta haka za ku san inda za ku bi, gama ba ku taɓa bin hanyar ba. Sai dai ku ɗan ba da rata wajen yadi ɗari tara tsakaninku da akwatin alkawari, kada ku kusace shi.”
그러나 너희와 그 사이 상거가 이천 규빗쯤 되게 하고 그것에 가까이 하지는 말라 그리하면 너희 행할 길을 알리니 너희가 이전에 이 길을 지나보지 못하였음이니라'
5 Yoshuwa ya ce wa mutane, “Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubangiji zai yi abubuwan al’ajabi a cikinku.”
여호수아가 또 백성에게 이르되 `너희는 스스로 성결케 하라! 여호와께서 내일 너희 가운데 기사를 행하시리라'
6 Yoshuwa ya ce wa firistoci, “Ku ɗauki akwatin alkawari ku sha gaba.” Sai suka ɗauki akwatin alkawari suka wuce gaban sauran jama’a.
여호수아가 또 제사장들에게 일러 가로되 `언약궤를 메고 백성 앞서 건너라' 하매 곧 언약궤를 메고 백성 앞서 나아가니라
7 Ubangiji kuwa ya ce wa Yoshuwa, “Yau, zan fara ɗaukaka ka a gaban Isra’ilawa duka don su sani cewa ina tare da kai kamar yadda na kasance tare da Musa.
여호와께서 여호수아에게 이르시되 내가 오늘부터 시작하여 너를 온 이스라엘의 목전에서 크게 하여 내가 모세와 함께 있던 것 같이 너와 함께 있는 것을 그들로 알게 하리라
8 Ka ce wa firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari, ‘Sa’ad da kuka kai bakin Urdun, ku shiga cikin ruwan ku tsaya.’”
너는 언약궤를 멘 제사장들에게 명하여 이르기를 너희가 요단 물가에 이르거든 요단에 들어서라 하라
9 Yoshuwa ya ce wa Isra’ilawa, “Ku zo nan ku ji maganar Ubangiji Allahnku.
여호수아가 이스라엘 자손에게 이르되 `이리 와서 너희 하나님 여호와의 말씀을 들으라' 하고
10 Ta haka ne za ku san cewa Allah mai rai yana tare da ku, kuma ba shakka a gabanku za ku gani zai kore Kan’aniyawa, Hittiyawa, Hiwiyawa, Ferizziyawa, Girgashiyawa, Amoriyawa da Yebusiyawa.
또 말하되 `사시는 하나님이 너희 가운데 계시사 가나안 족속과, 헷 족속과, 히위 족속과, 브리스 족속과, 기르가스 족속과, 아모리 족속과, 여부스 족속을 너희 앞에서 정녕히 쫓아내실 줄을 이 일로 너희가 알리라
11 Ku duba, akwatin alkawarin Ubangiji na dukan duniya zai yi gaba cikin Urdun kafin ku.
보라, 온 땅의 주의 언약궤가 너희 앞서 요단으로 들어가나니
12 Yanzu sai ku zaɓi mutum goma sha biyu daga kabilan Isra’ila, ɗaya daga kowace kabila.
이제 이스라엘 지파 중에서 매 지파에 한 사람씩 십 이명을 택하라
13 Kuma da firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji, Ubangiji dukan duniya, sun sa ƙafa cikin ruwan kogin Urdun, ruwan da yake gudu a rafin zai tsaya cik yă taru a wuri ɗaya.”
온 땅의 주 여호와의 궤를 멘 제사장들의 발바닥이 요단 물을 밟고 멈추면 요단 물 곧 위에서부터 흘러 내리던 물이 끊어지고 쌓여 서리라'
14 Saboda haka sa’ad da mutanen suka tashi don su ƙetare Urdun, firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin suka sha gaba.
백성이 요단을 건너려고 자기들의 장막을 떠날때에 제사장들은 언약궤를 메고 백성 앞에서 행하니라
15 Da kaka Urdun yakan cika makil da ruwa. Duk da haka da zarar firistoci masu ɗauke da akwatin alkawari suka tsoma ƙafafunsu a gefen ruwa,
(요단이 모맥 거두는 시기에는 항상 언덕에 넘치더라) 궤를 멘 자들이 요단에 이르며 궤를 멘 제사장들의 발이 물가에 잠기자
16 sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru a wuri ɗaya ya yi tudu daga nan har zuwa wani garin da ake kira Adam kusa da Zaretan, ruwan da yake gangarowa zuwa Tekun Araba (Tekun Gishiri) kuma ya yanke gaba ɗaya. Sai mutane suka ƙetare kusa da Yeriko.
곧 위에서부터 흘러 내리던 물이 그쳐서 심히 멀리 사르단에 가까운 아담 읍 변방에 일어나 쌓이고 아라바의 바다 염해로 향하여 흘러가는 물은 온전히 끊어지매 백성이 여리고 앞으로 바로 건널새
17 Firistocin kuwa da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya daram a kan busasshiyar ƙasa a tsakiyar Urdun a lokacin da Isra’ilawa suka ƙetarewa, har sai da dukan mutane suka gama ƙetarewa.
여호와의 언약궤를 멘 제사장들은 요단 가운데 마른 땅에 굳게 섰고 온 이스라엘 백성은 마른 땅으로 행하여 요단을 건너니라