< Yoshuwa 2 >
1 Sai Yoshuwa ɗan Nun ya aika’yan leƙen asiri guda biyu a ɓoye daga Shittim ya ce, “Ku je ku duba, ku ga yadda wurin yake, musamman Yeriko.” Sai suka je suka shiga gidan wata karuwa mai suna Rahab, suka sauka a can.
2 Aka gaya wa sarkin Yeriko cewa, “Ji fa, waɗansu Isra’ilawa sun shigo nan da dare don su leƙi asirin ƙasar.”
3 Saboda haka sai sarki ya aika wannan saƙo zuwa ga Rahab, “Ki fito da mutanen da suka zo suka sauka a gidanki, gama sun zo su leƙi asirin ƙasar ne gaba ɗaya.”
4 Amma matar ta ɓoye mutanen nan biyu. Ta ce, “I, mutanen sun zo wurina, amma ban san daga ina suka zo ba,
5 da yamma kuwa, kafin a rufe ƙofar gari sai mutanen suka tafi. Ban san hanyar da suka bi ba, ku yi sauri ku bi su. Mai yiwuwa ku same su.”
6 (Amma ta kai su saman rufin ɗaki ta ɓoye su a ƙarƙashin karan rama da ta baza a rufin ɗaki.)
7 Sai mutanen garin suka kama hanyar Urdun don su nemi’yan leƙen asirin, daga fitar su sai aka rufe ƙofar garin.
8 Kafin’yan leƙen asirin su kwanta, sai ta tafi wurinsu a bisa rufin ɗakin
9 ta ce musu, “Na sani Ubangiji ya riga ya ba ku ƙasan nan, tsoronku kuma ya kama mu har zukatan mazaunan ƙasar duka sun narke saboda ku.
10 Mun ji yadda Ubangiji ya busar da ruwan Jan Teku domin ku lokacin da kuka fito daga ƙasar Masar, da kuma abin da kuka yi wa Sihon da Og, sarakunan nan biyu na Amoriyawa gabas da Urdun, waɗanda kuka hallaka su sarai.
11 Da muka ji labarin, duk sai zuciyar kowa ta narke, kowa ya karaya saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne Allah na sama da ƙasa.
12 Yanzu ina roƙonku ku rantse mini da Ubangiji cewa za ku yi wa iyalina alheri kamar yadda na yi muku alheri. Ku ba ni ƙwaƙƙwarar shaida cewa
13 za ku ceci rayukan mahaifina da mahaifiyata, da’yan’uwana maza da mata, da duk waɗanda suke nasu, za ku cece mu daga mutuwa.”
14 Mutanen suka tabbatar mata suka ce, “Ranmu a bakin ranki! In ba ki faɗa wa kowa abin da ya kawo mu ba, za mu yi miki alheri da aminci lokacin da Ubangiji ya ba mu ƙasar.”
15 Sai ta zura igiya ta taga suka bi, domin gidan da take yana haɗe da katangar birnin.
16 Ta ce musu, “Ku tafi cikin tuddan ƙasar don kada mutanen sarki su same ku. Ku ɓuya a can na kwana uku, har sai masu nemanku su komo, sa’an nan ku kama hanyarku.”
17 Mutanen suka ce mata, “Rantsuwar da kika sa muka yi, ba za tă yi amfani ba
18 sai in kin ɗaura jan ƙyalle a tagar da kika zura mu, kuma sai in kin kawo mahaifinki da mahaifiyarki, da’yan’uwanki, da dukan iyalinki cikin gidanki.
19 In wani ya fita kan hanya, alhakin jininsa yă kasance a kansa; ba ruwanmu. Amma in aka taɓa wani da yake cikin gidanki tare da ke, alhakin jininsa yana kanmu.
20 In kika tone mana asiri, za mu karya alkawarin da kika sa muka yi.”
21 Ta ce, “Na yarda! Bari yă zama yadda kuka ce.” Sai ta sallame su suka tafi. Ta kuwa ɗaura jan ƙyalle a tagar.
22 Sai suka tafi, suka shiga cikin tuddai, suka yi zamansu a can kwana uku har masu nemansu suka koma, gama masu nemansu suka yi ta nema ko’ina a hanyar, amma ba su sami kowa ba.
23 Sa’an nan mutanen nan biyu,’yan leƙen asiri suka sauka daga tuddai suka haye kogi zuwa wurin Yoshuwa ɗan Nun, suka gaya masa duk abin da ya faru da su.
24 Suka ce wa Yoshuwa, “Ba shakka Ubangiji ya ba mu ƙasan nan duka, tana hannunmu, mutane can duk sun narke da tsoro saboda mu.”