< Yoshuwa 19 >

1 Ƙuri’a ta biyu ta fāɗa a kan kabilar Simeyon, bisa ga iyalansu. Ƙasarsu ta gādo tana cikin yankin Yahuda.
為西緬支派的人,按着宗族,拈出第二鬮。他們所得的地業是在猶大人地業中間。
2 Waɗannan su ne wuraren da suka gāda. Beyersheba (ko Sheba), Molada,
他們所得為業之地就是:別是巴(或名示巴)、摩拉大、
3 Hazar Shuwal, Bilha, Ezem,
哈薩‧書亞、巴拉、以森、
4 Eltolad, Betul, Horma,
伊利多拉、比土力、何珥瑪、
5 Ziklag, Bet-Markabot, Hazar-Susa,
洗革拉、伯‧瑪加博、哈薩‧蘇撒、
6 Bet-Lebayot da Sharuhen, garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu.
伯‧利巴勿、沙魯險,共十三座城,還有屬城的村莊;
7 Akwai kuma Ayin, Rimmon, Eter da Ashan, garuruwa huɗu ke nan da ƙauyukansu,
又有亞因、利門、以帖、亞珊,共四座城,還有屬城的村莊;
8 da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da garuruwan nan har zuwa Rama na Negeb (wato, Ba’alat-Beyer). Wannan shi ne gādon kabilar Simeyon bisa ga iyalansu.
並有這些城邑四圍一切的村莊,直到巴拉‧比珥,就是南地的拉瑪。這是西緬支派按着宗族所得的地業。
9 Daga cikin gādon mutanen Yahuda ne aka fitar da gādon kabilar Simeyon, bisa ga iyalansu, domin rabon da kabilar Yahuda suka samu ya fi ƙarfin abin da suke bukata. Saboda haka kabilar gādon Simeyon yana cikin harabar Yahuda.
西緬人的地業是從猶大人地業中得來的;因為猶大人的分過多,所以西緬人在他們的地業中得了地業。
10 Ƙuri’a ta uku ta fāɗa a kan Zebulun bisa ga iyalansu. Iyakar ƙasarsu ta gādo ta kai har Sarid.
為西布倫人,按着宗族,拈出第三鬮。他們地業的境界是到撒立;
11 Ta nufi yamma zuwa Marala, ta taɓa Dabbeshet, ta wuce zuwa rafin da yake kusa da Yokneyam.
往西上到瑪拉拉,達到大巴設,又達到約念前的河;
12 Daga Sarid, ta juya gabas zuwa harabar Kislot Tabor, ta kuma wuce zuwa Daberat har zuwa Yafiya.
又從撒立往東轉向日出之地,到吉斯綠‧他泊的境界,又通到大比拉,上到雅非亞;
13 Sa’an nan ta ci gaba, ta yi gabas zuwa Gat-Hefer da Et Kazin; ta ɓulla a Rimmon, ta juya zuwa Neya.
從那裏往東,接連到迦特‧希弗,至以特‧加汛,通到臨門,臨門延到尼亞;
14 A can ne iyakar ta kewaya zuwa Hannaton, sa’an nan ta ƙarasa a Kwarin Ifta El.
又繞過尼亞的北邊,轉到哈拿頓,通到伊弗他‧伊勒谷。
15 Zebulun ta ƙunshi garuruwa goma sha biyu da ƙauyukansu. Garuruwan sun haɗa da Kattat, Nahalal, Shimron, Idala da Betlehem.
還有加他、拿哈拉、伸崙、以大拉、伯利恆,共十二座城,還有屬城的村莊。
16 Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Zebulun ta samu, bisa ga iyalansu.
這些城並屬城的村莊就是西布倫人按着宗族所得的地業。
17 Ƙuri’a ta huɗu ta fāɗa a kan kabilar Issakar, bisa ga iyalansu.
為以薩迦人,按着宗族,拈出第四鬮。
18 Ƙasarsu gādonsu ta haɗa da, Yezireyel, Kessulot, Shunem,
他們的境界是到耶斯列、基蘇律、書念、
19 Hafarayim, Anaharat,
哈弗連、示按、亞拿哈拉、
20 Rabbat, Kishiyon, Ebez,
拉璧、基善、亞別、
21 Remet, En Gannim, En Hadda da Bet-Fazez.
利篾、隱‧干寧、隱‧哈大、伯‧帕薛;
22 Iyakar ta taɓa Tabor Shahazuma da Bet-Shemesh ta kuma ƙarasa a Urdun. Duka-duka garuruwa goma sha shida ke nan da ƙauyukansu.
又達到他泊、沙哈洗瑪、伯‧示麥,直通到約旦河為止,共十六座城,還有屬城的村莊。
23 Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon da kabilar Issakar ta samu, bisa ga iyalansu.
這些城並屬城的村莊就是以薩迦支派按着宗族所得的地業。
24 Ƙuri’a ta biyar ta fāɗa a kan kabilar Asher, bisa ga iyalansu.
為亞設支派,按着宗族,拈出第五鬮。
25 Ƙasarsu gādonsu ta haɗa da, Helkat, Hali, Beten, Akshaf,
他們的境界是黑甲、哈利、比田、押煞、
26 Allammelek, Amad da Mishal. A arewanci kuma iyakar ta taɓa Karmel da Shihor Libnat.
亞拉米勒、亞末、米沙勒;往西達到迦密,又到希曷‧立納,
27 Sai ta yi gabas zuwa Bet-Dagon, ta taɓa Zebulun da kuma Kwarin Ifta El, ta wuce arewa zuwa Bet-Emek da Neyiyel, ta wuce Kabul a hagu,
轉向日出之地,到伯‧大袞,達到細步綸;往北到伊弗他‧伊勒谷,到伯‧以墨和尼業,也通到迦步勒的左邊;
28 ta kai Abdon, Rehob, Hammon da Kana, har zuwa Sidon Babba.
又到義伯崙、利合、哈們、加拿,直到西頓大城;
29 Daga nan iyakar ta juya baya zuwa Rama, ta bi ta birnin nan mai katanga na Taya, ta juya ta nufi Hosa, sa’an nan ta ɓulla ta Bahar Rum cikin yankin Akzib,
轉到拉瑪和堅固城泰爾;又轉到何薩,靠近亞革悉一帶地方,直通到海;
30 Umma, Afek da Rehob. Garuruwa ashirin da biyu ke nan da ƙauyukansu.
又有烏瑪、亞弗、利合,共二十二座城,還有屬城的村莊。
31 Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Asher ta samu bisa ga iyalansu.
這些城並屬城的村莊就是亞設支派按着宗族所得的地業。
32 Ƙuri’a ta shida ta fāɗa a kan kabilar Naftali, bisa ga iyalansu.
為拿弗他利人,按着宗族,拈出第六鬮。
33 Iyakarsu ta kama daga Helef, daga babban itacen Mamre nan da yake a Za’anannim, ta wuce Adami Nekeb da Yabneyel zuwa Lakkum, ta kuma ƙarasa a Urdun.
他們的境界是從希利弗從撒拿音的橡樹,從亞大米‧尼吉和雅比聶,直到拉共,通到約旦河;
34 Iyakar kuma ta juya yamma ta cikin Aznot-Tabo ta ɓulla a Hukkok. Ta taɓa Zebulun a kudu, Asher a yamma, da kuma Urdun a gabas.
又轉向西到亞斯納‧他泊,從那裏通到戶割,南邊到西布倫,西邊到亞設,又向日出之地,達到約旦河那裏的猶大。
35 Biranen da suke da katanga su ne Ziddim, Zer, Hammat, Rakkat, Kinneret,
堅固的城就是:西丁、側耳、哈末、拉甲、基尼烈、
36 Adama, Rama, Hazor,
亞大瑪、拉瑪、夏瑣、
37 Kedesh, Edireyi, En Hazor,
基低斯、以得來、隱‧夏瑣、
38 Yiron, Migdal El, Horem, Bet-Anat da Bet-Shemesh. Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu.
以利穩、密大‧伊勒、和璉、伯‧亞納、伯‧示麥,共十九座城,還有屬城的村莊。
39 Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon da kabilar Naftali ta samu, bisa ga iyalansu.
這些城並屬城的村莊就是拿弗他利支派按着宗族所得的地業。
40 Ƙuri’a ta bakwai ta fāɗa a kan kabilar Dan, bisa ga iyalansu.
為但支派,按着宗族,拈出第七鬮。
41 Ƙasarsu ta gādo ta haɗa da, Zora, Eshtawol, Ir Shemesh,
他們地業的境界是瑣拉、以實陶、伊珥‧示麥、
42 Shalim, Aiyalon, Itla,
沙拉賓、亞雅崙、伊提拉、
43 Elon, Timna, Ekron,
以倫、亭拿他、以革倫、
44 Elteke, Gibbeton, Ba’alat,
伊利提基、基比頓、巴拉、
45 Yehud, Bene-Berak, Gat-Rimmon,
伊胡得、比尼‧比拉、迦特‧臨門、
46 Me Yarkon da Rakkon tare da sashen da yake fuskantar Yaffa.
美‧耶昆、拉昆,並約帕對面的地界。
47 (Amma ya zama wa mutanen kabilar Dan da wahala su mallaki ƙasar da aka ba su gādo, saboda haka sai suka nufi Leshem suka ci su da yaƙi, suka karkashe mutanen wurin, suka mallake ta, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato, Dan.)
但人的地界越過原得的地界;因為但人上去攻取利善,用刀擊殺城中的人,得了那城,住在其中,以他們先祖但的名將利善改名為但。
48 Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon kabilar Dan, bisa ga iyalansu.
這些城並屬城的村莊就是但支派按着宗族所得的地業。
49 Sa’ad da aka gama raba gādon ƙasar bisa ga ƙuri’a. Sai Isra’ilawa suka ba Yoshuwa ɗan Nun nasa rabo a cikinsu,
以色列人按着境界分完了地業,就在他們中間將地給嫩的兒子約書亞為業,
50 yadda Ubangiji ya umarta, suka ba shi garin da ya ce a ba shi, Timnat Serad a ƙasar tudu ta Efraim. Ya kuma gina garin ya zauna a can.
是照耶和華的吩咐,將約書亞所求的城,就是以法蓮山地的亭拿‧西拉城,給了他。他就修那城,住在其中。
51 Waɗannan su ne rabe-raben gādon da Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin kabilan iyalan Isra’ila suka rarraba ta hanyar jefa ƙuri’a a Shilo a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada. Da haka suka yi suka gama rarraba ƙasar.
這就是祭司以利亞撒和嫩的兒子約書亞,並以色列各支派的族長,在示羅會幕門口,耶和華面前,拈鬮所分的地業。這樣,他們把地分完了。

< Yoshuwa 19 >