< Yoshuwa 15 >
1 An raba wa kabilar Yahuda gādonsu ta wurin yin ƙuri’a, bisa ga iyalansu, rabon ya kai har zuwa sashen Edom, zuwa Jejin Zin can kurewar kudu.
2 Iyakarsu a kudanci ta tashi tun daga kurewar kudu na Tekun Gishiri,
3 zuwa kudancin Hanyar Kunama, ta ci gaba har zuwa Zin, zuwa kudancin Kadesh Barneya. Sa’an nan ta kurɗa zuwa Hezron har zuwa Addar, ta kuma karkata zuwa Karka.
4 Sai ta wuce zuwa Azmon ta haɗu da Rafin Masar, ta ƙarasa a Bahar Rum. Wannan shi ne iyakarsu ta kudu.
5 Iyakarsu ta gabas kuwa ita ce Tekun Gishiri wadda ta zarce har zuwa gaɓar Urdun. Iyakarsu ta arewa ta fara ne daga Tekun Gishiri a bakin Urdun,
6 wajen Bet-Hogla ta wuce har zuwa arewancin Bet-Araba, zuwa Dutsen Bohan ɗan Ruben.
7 Sai iyakar ta haura zuwa Debir daga Kwarin Akor ta juya arewa da Gilgal, wadda take fuskantar hawan Adummim a kudancin kwari, ta ci gaba zuwa ruwan En Shemesh, ta ɓullo ta En Rogel.
8 Sai kuma ta gangara zuwa Kwarin Ben Hinnom a gangaren kudancin birnin Yebusiyawa (wato, Urushalima). Daga can ta haura zuwa kan tudun a yammancin Kwarin Hinnom, a arewancin ƙarshen Kwarin Refayim.
9 Daga kan tudun, iyakar ta nufi maɓulɓular ruwa na Neftowa, ta ɓullo a garuruwan da suke a Dutsen Efron, ta gangara zuwa Ba’ala (wato, Kiriyat Yeyarim).
10 Sa’an nan ta karkata yamma daga Ba’ala zuwa Dutsen Seyir, ta wuce ta gangaren Dutsen Yeyarim (wato, Kesalon), ta ci gaba zuwa Bet-Shemesh, ta bi zuwa Timna.
11 Ta wuce zuwa gangaren arewancin Ekron, ta juya zuwa Shikkeron, ta wuce zuwa Dutsen Ba’ala, ta kai Yabneyel, iyakarta ta ƙare a teku.
12 Bakin Bahar Rum nan ne iyakar yammanci. Wannan ita ce iyakar da ta kewaye jama’ar Yahuda bisa ga iyalansu.
13 Yoshuwa ya ba Kaleb ɗan Yefunne wuri a Yahuda, Kiriyat Arba, wato, Hebron, bisa ga umarnin Ubangiji. (Arba shi ne mahaifin Anak.)
14 Daga can sai Kaleb ya kori’ya’yan Anak, maza su uku daga Hebron, wato, Sheshai, Ahiman da Talmai.
15 Daga can ya nufi Debir ya yi yaƙi da mutanen da suke zama a can (Dā sunan Debir, Kiriyat Sefer ne).
16 Kaleb ya ce, “Zan ba da’yata Aksa aure ga wanda zai ci Kiriyat Sefer da yaƙi.”
17 Otniyel ɗan Kenaz, ɗan’uwan Kaleb, ya ci Kiriyat Sefer da yaƙi; saboda haka Kaleb ya ba wa Aksa’yarsa, ya kuwa aure ta.
18 Wata rana da ta zo wurin Otniyel, sai ya zuga ta ta roƙi mahaifinta fili. Da ta sauka daga kan jakinta sai Kaleb ya tambaye ta ya ce, “Me kike so in yi miki?”
19 Ta amsa ta ce, “Ka yi mini alheri na musamman, tun da ka ba ni wuri a Negeb, ina roƙonka, ka ba ni maɓulɓulan ruwa.” Kaleb kuwa ya ba ta maɓulɓulan ruwa na tuddai da na kwari.
20 Wannan shi ne gādon kabilar Yahuda bisa ga iyalansu.
21 Garuruwan kabilar Yahuda da suke kudu cikin Negeb zuwa iyakar Edom su ne. Kabzeyel, Eder, Yagur,
22 Kina, Dimona, Adada,
23 Kedesh, Hazor, Itnan,
24 Zif, Telem, Beyalot,
25 Hazor-Hadatta, Keriyot Hezron (wato, Hazor),
26 Amam, Shema, Molada,
27 Hazar Gadda, Heshmon, Bet-Felet,
28 Hazar Shuwal, Beyersheba, Biziyotiya,
29 Ba’ala, Iyim, Ezem,
30 Eltolad, Kesil, Horma,
31 Ziklag, Madmanna, Sansanna,
32 Lebayot, Shilhim, Ayin, Rimmon, jimillarsu, garuruwa da ƙauyukansu duka ashirin da tara ne.
33 Biranen da suke a filayen kwari su ne, Eshtawol, Zora; Ashna,
34 Zanowa, En Gannim, Taffuwa, Enam,
35 Yarmut, Adullam, Soko, Azeka,
36 Sha’arayim, Aditayim, Gedera (Gederotayim ke nan). Garuruwa goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu.
37 Zenan, Hadasha, Migdal Gad,
38 Dileyan, Mizfa, Yokteyel,
39 Lakish, Bozkat, Eglon,
40 Kabbon, Lahman, Kitlish,
41 Gederot, Bet-Dagon, Na’ama, Makkeda, garuruwa goma sha shida ke nan da ƙauyukansu.
42 Libna, Eter, Ashan,
43 Yefta, Ashna, Nezib,
44 Keyila, Akzib, Maresha, garuruwa tara ke nan da ƙauyukansu.
45 Ekron da ƙauyukan da suke kewaye da ita;
46 yammancin Ekron da dukan garuruwa da ƙauyukan da suke kusa da Ashdod.
47 Ashdod da garuruwa da kuma ƙauyukan da suke kewaye da ita, Gaza da garuruwanta da ƙauyukanta har zuwa Rafin Masar da kuma Bahar Rum.
48 Birane na cikin ƙasar tuddai kuwa, su ne, Shamir, Yattir, Soko,
49 Danna, Kiriyat Sanna (wato, Debir),
50 Anab, Eshtemo, Anim,
51 Goshen, Holon, Gilo, garuruwa goma sha ɗaya ke nan da ƙauyukansu.
52 Arab, Duma, Eshan,
53 Yanum, Bet-Taffuwa, Afeka,
54 Humta, Kiriyat Arba (wato, Hebron) da Ziyor, garuruwa tara ke nan da ƙauyukansu.
55 Mawon, Karmel, Zif, Yutta
56 Yezireyel, Yokdeyam, Zanowa,
57 Kayin, Gibeya, Timna, garuruwa goma ke nan da ƙauyukansu.
58 Halhul, Bet-Zur, Gedor,
59 Ma’arat, Bet-Anot, Eltekon, garuruwa shida ke nan da ƙauyukansu.
60 Kiriyat Ba’al (wato, Kiriyat Yeyarim) da Rabba, garuruwa biyu ke nan da ƙauyukansu.
61 Biranen da suke a jeji kuwa su ne, Bet-Araba, Middin, Sekaka,
62 Nibshan, Birnin gishiri da En Gedi, garuruwa shida ke nan da ƙauyukansu.
63 Kabilar Yahuda kuwa ba su iya korar Yebusiyawa waɗanda suke zama cikin Urushalima ba; har wa yau Yebusiyawa suna nan zaune tare da mutanen Yahuda.