< Yoshuwa 14 >

1 Ga wuraren da Isra’ilawa suka sami gādo a ƙasar Kan’ana waɗanda Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun da kuma shugabannin iyalai kabila-kabila na Isra’ila suka raba musu.
And these are the countries which the children of Israel inherited in the land of Canaan, which Eleazar the priest, and Joshua the son of Nun, and the heads of the fathers of the tribes of the children of Israel, distributed for inheritance to them.
2 Ta wurin yin ƙuri’a aka raba wa kabilan nan tara da rabi, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.
By lot was their inheritance, as the LORD commanded by the hand of Moses, for the nine tribes, and for the half tribe.
3 Musa ya ba wa kabilan biyu da rabin nan gādonsu gabashin Urdun, amma bai ba wa Lawiyawa gādo a cikin sauran ba,
For Moses had given the inheritance of two tribes and an half tribe on the other side Jordan: but to the Levites he gave none inheritance among them.
4 gama’ya’yan Yusuf sun zama kabilu biyu, Manasse da Efraim. Ba a ba Lawiyawa gādon ba sai dai garuruwan da aka ba su su zauna a ciki, da wurin kiwo mai kyau domin dabbobinsu.
For the children of Joseph were two tribes, Manasseh and Ephraim: therefore they gave no part to the Levites in the land, save cities to dwell in, with their suburbs for their cattle and for their substance.
5 Haka Isra’ilawa suka raba ƙasar, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
As the LORD commanded Moses, so the children of Israel did, and they divided the land.
6 Mutanen Yahuda kuma suka je wurin Yoshuwa a Gilgal, sai Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze ya ce wa Yoshuwa, “Ka san abin da Ubangiji ya gaya wa Musa, mutumin Allah a Kadesh Barneya game da kai da ni.
Then the children of Judah came to Joshua in Gilgal: and Caleb the son of Jephunneh the Kenezite said to him, You know the thing that the LORD said to Moses the man of God concerning me and you in Kadeshbarnea.
7 Ina da shekara arba’in lokacin da Musa bawan Ubangiji ya aike ni zuwa Kadesh Barneya in leƙi asirin ƙasar. Na kuwa kawo masa rahoto daidai yadda na ga ƙasar,
Forty years old was I when Moses the servant of the LORD sent me from Kadeshbarnea to espy out the land; and I brought him word again as it was in my heart.
8 amma’yan’uwana waɗanda muka je tare su suka ba da rahoton da ya sa zukatan mutane suka narke don tsoro. Ni kam na bi Ubangiji Allah da dukan zuciyata.
Nevertheless my brothers that went up with me made the heart of the people melt: but I wholly followed the LORD my God.
9 Saboda haka a ranan nan Musa ya rantse mini cewa, ‘Ƙasar da ka taka za tă zama ƙasarka ta gādo kai da’ya’yanka har abada, domin ka bi Ubangiji Allahna da dukan zuciyarka.’
And Moses swore on that day, saying, Surely the land where on your feet have trodden shall be your inheritance, and your children’s for ever, because you have wholly followed the LORD my God.
10 “Ga shi, kamar yadda Ubangiji ya yi alkawari, ya bar ni da rai har na ƙara shekaru arba’in da biyar tun daga lokacin da ya gaya wa Musa wannan, a lokacin da Isra’ilawa suke yawo a cikin jeji. Ga ni nan yau shekaruna tamanin da biyar!
And now, behold, the LORD has kept me alive, as he said, these forty and five years, even since the LORD spoke this word to Moses, while the children of Israel wandered in the wilderness: and now, see, I am this day fourscore and five years old.
11 Ina nan da ƙarfina kamar yadda nake da ƙarfi a lokacin da Musa ya aike ni; zan iya fita zuwa yaƙi da ƙwazo yanzu kamar yadda nake zuwa a dā.
As yet I am as strong this day as I was in the day that Moses sent me: as my strength was then, even so is my strength now, for war, both to go out, and to come in.
12 Yanzu sai ka ba ni wannan ƙasar da take kan tudu wadda Ubangiji ya yi alkawari zai ba ni a ranan nan. Kai ma ka ji a lokacin, yadda Anakawa suke a can, biranensu manya ne kuma sun kewaye su sosai, amma na sani Ubangiji zai taimake ni, zan kore su kamar yadda ya faɗa.”
Now therefore give me this mountain, whereof the LORD spoke in that day; for you heard in that day how the Anakims were there, and that the cities were great and fenced: if so be the LORD will be with me, then I shall be able to drive them out, as the LORD said.
13 Sai Yoshuwa ya sa wa Kaleb ɗan Yefunne albarka, ya ba shi Hebron.
And Joshua blessed him, and gave to Caleb the son of Jephunneh Hebron for an inheritance.
14 Saboda haka Hebron ta zama ƙasar Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze tun daga lokacin nan, domin ya bi Ubangiji, Allah na Isra’ila da dukan zuciyarsa.
Hebron therefore became the inheritance of Caleb the son of Jephunneh the Kenezite to this day, because that he wholly followed the LORD God of Israel.
15 (Dā a kan kira wannan Hebron, Kiriyat Arba. Wannan Arba kuwa shi ne wani katon mutum a cikin Anakawa.) Sa’an nan ƙasar ta huta daga yaƙi.
And the name of Hebron before was Kirjatharba; which Arba was a great man among the Anakims. And the land had rest from war.

< Yoshuwa 14 >