< Yoshuwa 13 >

1 Sa’ad da Yoshuwa ya tsufa, Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi kuma akwai sauran ƙasa mai fāɗi da ba ku riga kun mallaka ba.
ויהושע זקן בא בימים ויאמר יהוה אליו אתה זקנתה באת בימים והארץ נשארה הרבה מאד לרשתה
2 “Ga ƙasar da ta rage, “dukan yankunan Filistiyawa da na Geshurawa.
זאת הארץ הנשארת כל גלילות הפלשתים וכל הגשורי
3 Daga Kogin Shihor a gabashin Masar zuwa sashen Ekron a arewa, dukan wannan ƙasa ana lissafta ta a cikin ƙasar Kan’aniyawa, ko da yake tana a sashen da sarakuna biyar na Filistiyawa na Gaza, Ashdod, Ashkeloniyawa, Gat da Ekron; na Awwiyawa.
מן השיחור אשר על פני מצרים ועד גבול עקרון צפונה--לכנעני תחשב חמשת סרני פלשתים העזתי והאשדודי האשקלוני הגתי והעקרוני והעוים
4 Daga wajen kudu kuma, dukan ƙasar Kan’aniyawa ce. Iyakarta a arewa ta fara daga Ara ta Sidoniyawa har zuwa Afek, ta zarce har zuwa iyakar Amoriyawa;
מתימן כל ארץ הכנעני ומערה אשר לצידנים--עד אפקה עד גבול האמרי
5 da ƙasar Gebaliyawa; da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba’al-Gad a gindin Dutsen Hermon zuwa Lebo Hamat.
והארץ הגבלי וכל הלבנון מזרח השמש מבעל גד תחת הר חרמון--עד לבוא חמת
6 “Dukan mazauna kan yankunan tuddai daga Lebanon zuwa Misrefot Mayim, wato, dukan Sidoniyawa, ni da kaina zan kore su a gaban Isra’ilawa. Ka tabbata ka raba wa Isra’ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka,
כל ישבי ההר מן הלבנון עד משרפת מים כל צידנים--אנכי אורישם מפני בני ישראל רק הפלה לישראל בנחלה כאשר צויתיך
7 ka raba ta tă zama gādo wa kabilu tara da kuma rabin kabilar Manasse.”
ועתה חלק את הארץ הזאת בנחלה--לתשעת השבטים וחצי השבט המנשה
8 Rabin kabilar Manasse, mutanen Ruben da mutanen Gad suka karɓi rabonsu na gādo wanda Musa ya ba su a gabashin Urdun. Abin da Musa bawan Ubangiji ya ba su ke nan.
עמו הראובני והגדי לקחו נחלתם--אשר נתן להם משה בעבר הירדן מזרחה כאשר נתן להם משה עבד יהוה
9 Wannan ya tashi daga Arower a gefen kwarin Arnon, da kuma daga garin da yake tsakiyar kwarin, ya kuma haɗa da ƙasar da take tudun Medeba har zuwa Dibon,
מערוער אשר על שפת נחל ארנון והעיר אשר בתוך הנחל וכל המישר מידבא--עד דיבון
10 da dukan garuruwan Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulkin Heshbon, har zuwa iyakar Ammonawa.
וכל ערי סיחון מלך האמרי אשר מלך בחשבון--עד גבול בני עמון
11 Haɗe da Gileyad, inda mutanen Geshur da Ma’aka suke. Dukan Dutsen Hermon, da dukan Bashan har zuwa Saleka,
והגלעד וגבול הגשורי והמעכתי וכל הר חרמון וכל הבשן--עד סלכה
12 wato, dukan masarautar Og a Bashan, wanda ya yi mulkin Ashtarot da Edireyi, yana cikin waɗanda suke na ƙarshe da ba a kashe ba a cikin Refahiyawa. Musa ya ci su da yaƙi, ya ƙwace ƙasarsu.
כל ממלכות עוג בבשן אשר מלך בעשתרות ובאדרעי הוא נשאר מיתר הרפאים ויכם משה וירשם
13 Amma Isra’ilawa ba su kori mutanen Geshur da Ma’aka ba, saboda haka suka ci gaba da zama cikin Isra’ilawa har wa yau.
ולא הורישו בני ישראל את הגשורי ואת המעכתי וישב גשור ומעכת בקרב ישראל עד היום הזה
14 Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa da ake miƙa wa Ubangiji, Allah na Isra’ila ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari.
רק לשבט הלוי לא נתן נחלה אשי יהוה אלהי ישראל הוא נחלתו כאשר דבר לו
15 Ga abin da Musa ya ba kabilar Ruben bisa ga iyalansu.
ויתן משה למטה בני ראובן למשפחתם
16 Abin da ya kama daga Arower a gefen kwarin Arnon, da kuma daga garin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu kusa da Medeba
ויהי להם הגבול מערוער אשר על שפת נחל ארנון והעיר אשר בתוך הנחל וכל המישר--על מידבא
17 zuwa Heshbon, da dukan garuruwan kan tudu, haɗe da Dibon, Bamot Ba’al, Bet-Ba’al-Meyon,
חשבון וכל עריה אשר במישר דיבן ובמות בעל ובית בעל מעון
18 Yahza, Kedemot, Mefa’at,
ויהצה וקדמת ומפעת
19 Kiriyatayim, Sibma, Zeret Shahar kan tudu cikin kwari,
וקריתים ושבמה וצרת השחר בהר העמק
20 Bet-Feyor, gangaren Fisga da Bet-Yeshimot,
ובית פעור ואשדות הפסגה ובית הישמות
21 dukan garuruwan da suke kan tudu da dukan masarautar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Musa ya yi nasara da shi, da shugabannin Midiyawa, wato, Ewi, Rekem, Zur, Hur, da Reba, sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar.
וכל ערי המישר וכל ממלכות סיחון מלך האמרי אשר מלך בחשבון אשר הכה משה אתו ואת נשיאי מדין את אוי ואת רקם ואת צור ואת חור ואת רבע נסיכי סיחון ישבי הארץ
22 Ƙari a kan waɗanda aka kashe a yaƙi, Isra’ilawa suka kashe Bala’am ɗan Beyor da takobi don yana duba.
ואת בלעם בן בעור הקוסם--הרגו בני ישראל בחרב אל חלליהם
23 Gefen Urdun shi ne iyakar mutanen Ruben. Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon mutanen Ruben, bisa ga iyalansu.
ויהי גבול בני ראובן--הירדן וגבול זאת נחלת בני ראובן למשפחותם הערים וחצריהן
24 Ga abin da Musa ya ba kabilar Gad, bisa ga iyalansu.
ויתן משה למטה גד לבני גד למשפחתם
25 Yankin ƙasarsu ya ƙunshi Yazer, da dukan garuruwan Gileyad, da rabin ƙasar Ammonawa har zuwa Arower kusa da Rabba,
ויהי להם הגבול--יעזר וכל ערי הגלעד וחצי ארץ בני עמון עד ערוער אשר על פני רבה
26 da kuma daga Heshbon zuwa Ramat Mizfa da Betonim, da kuma daga Mahanayim zuwa sashen Debir,
ומחשבון עד רמת המצפה ובטנים וממחנים עד גבול לדבר
27 kuma a cikin kwari, Bet-Haram, Bet-Nimra, Sukkot da Zafon da kuma sauran masarautar Sihon sarkin Heshbon (gabashin Urdun, abin da ya kama har zuwa ƙarshen Tekun Kinneret).
ובעמק בית הרם ובית נמרה וסכות וצפון יתר ממלכות סיחון מלך חשבון הירדן וגבל--עד קצה ים כנרת עבר הירדן מזרחה
28 Waɗannan garuruwan da ƙauyukansu duka, gādon mutanen Gad ne, bisa ga iyalansu.
זאת נחלת בני גד למשפחתם הערים וחצריהם
29 Ga abin da Musa ya ba rabin kabilar Manasse, wato, wa rabin zuriyar Manasse, bisa ga iyalansu.
ויתן משה לחצי שבט מנשה ויהי לחצי מטה בני מנשה--למשפחותם
30 Abin da ya miƙe daga Mahanayim haɗe da dukan Bashan, da gefen masarautar Og sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan,
ויהי גבולם ממחנים כל הבשן כל ממלכות עוג מלך הבשן וכל חות יאיר אשר בבשן--ששים עיר
31 da rabin Gileyad, da Ashtarot, Edireyi (biranen sarki Og a Bashan). Wannan shi ne rabon da zuriyar Makir ɗan Manasse suka samu, domin rabin’ya’yan Makir maza, bisa ga iyalansu.
וחצי הגלעד ועשתרות ואדרעי ערי ממלכות עוג בבשן לבני מכיר בן מנשה לחצי בני מכיר למשפחותם
32 Waɗannan su ne rabon gādon da Musa ya yi lokacin da suke cikin filayen Mowab a hayin gabashin Urdun kusa da Yeriko.
אלה אשר נחל משה בערבות מואב מעבר לירדן יריחו מזרחה
33 Amma Musa bai ba kabilar Lawiyawa gādo ba; Ubangiji, Allah na Isra’ila, shi ne gādonsu kamar yadda ya yi musu alkawari.
ולשבט הלוי--לא נתן משה נחלה יהוה אלהי ישראל הוא נחלתם כאשר דבר להם

< Yoshuwa 13 >