< Yoshuwa 12 >

1 Waɗannan su ne sarakunan ƙasashen da Isra’ilawa suka ci da yaƙi, suka kuma mallaki ƙasarsu a gabashin Urdun, daga kwarin Arnon zuwa Dutsen Hermon haɗe da dukan gefen gabas na Araba.
以色列人在約旦河外向日出之地擊殺二王,得他們的地,就是從亞嫩谷直到黑門山,並東邊的全亞拉巴之地。
2 Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Ya yi mulki daga Arower wadda take iyakar kwarin Arnon, daga tsakiyar kwarin har zuwa, Kogin Yabbok, wanda yake iyakar Ammonawa. Wannan ya haɗa da rabin Gileyad.
這二王,有住希實本、亞摩利人的王西宏。他所管之地是從亞嫩谷邊的亞羅珥和谷中的城,並基列一半,直到亞捫人的境界,雅博河
3 Ya kuma yi mulki a kan gabashin Araba daga tekun Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri), zuwa Bet-Yeshimot da kuma kudu zuwa gangaren dutsen Fisga.
與約旦河東邊的亞拉巴,直到基尼烈海,又到亞拉巴的海,就是鹽海,通伯‧耶西末的路,以及南方,直到毗斯迦的山根。
4 Haka ma suka ci sashen Og sarkin Bashan, ɗaya daga cikin Refahiyawa na ƙarshe da ya yi mulki a Ashtarot da Edireyi.
又有巴珊王噩。他是利乏音人所剩下的,住在亞斯他錄和以得來。
5 Mulkinsa ya taso daga Dutsen Hermon, da Saleka, da dukan Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa haɗe da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar Heshbon ta sarki Sihon.
他所管之地是黑門山、撒迦、巴珊全地,直到基述人和瑪迦人的境界,並基列一半,直到希實本王西宏的境界。
6 Sai Musa, bawan Ubangiji da Isra’ilawa suka ci Sihon da Og da yaƙi. Musa bawan Ubangiji kuwa ya ba da ƙasarsu ga mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse.
這二王是耶和華僕人摩西和以色列人所擊殺的;耶和華僕人摩西將他們的地賜給呂便人、迦得人,和瑪拿西半支派的人為業。
7 Waɗannan su ne sarakuna da kuma ƙasashen da Yoshuwa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi a yammancin Urdun, daga Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa Seyir. Yoshuwa ya raba ƙasarsu ta zama gādo ga Isra’ilawa bisa ga yadda aka raba su kabila-kabila.
約書亞和以色列人在約旦河西擊殺了諸王。他們的地是從黎巴嫩平原的巴力‧迦得,直到上西珥的哈拉山。約書亞就將那地按着以色列支派的宗族分給他們為業,
8 Ƙasar ta haɗa da ƙasar kan tudu, filayen arewanci, Araba, gangaren Dutse, da jejin, da kuma Negeb, wato, ƙasashen Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa, da Yebusiyawa.
就是赫人、亞摩利人、迦南人、比利洗人、希未人、耶布斯人的山地、高原亞拉巴、山坡、曠野,和南地。
9 Sarkin Yeriko, ɗaya sarkin Ai (kusa da Betel), ɗaya
他們的王:一個是耶利哥王,一個是靠近伯特利的艾城王,
10 sarkin Urushalima, ɗaya sarkin Hebron, ɗaya
一個是耶路撒冷王,一個是希伯崙王,
11 sarkin Yarmut, ɗaya sarkin Lakish, ɗaya
一個是耶末王,一個是拉吉王,
12 sarkin Eglon, ɗaya sarkin Gezer, ɗaya
一個是伊磯倫王,一個是基色王,
13 sarkin Debir, ɗaya sarkin Bet-Gader, ɗaya
一個是底璧王,一個是基德王,
14 sarkin Horma, ɗaya sarkin Arad, ɗaya
一個是何珥瑪王,一個是亞拉得王,
15 sarkin Libna, ɗaya sarkin Adullam, ɗaya
一個是立拿王,一個是亞杜蘭王,
16 sarkin Makkeda, ɗaya sarkin Betel, ɗaya
一個是瑪基大王,一個是伯特利王,
17 sarkin Taffuwa, ɗaya sarkin Hefer, ɗaya
一個是他普亞王,一個是希弗王,
18 sarkin Afek, ɗaya sarkin Sharon, ɗaya
一個是亞弗王,一個是拉沙崙王,
19 sarkin Madon, ɗaya sarkin Hazor, ɗaya
一個是瑪頓王,一個是夏瑣王,
20 sarkin Shimron Meron, ɗaya sarkin Akshaf, ɗaya
一個是伸崙‧米崙王,一個是押煞王,
21 sarkin Ta’anak, ɗaya sarkin Megiddo, ɗaya
一個是他納王,一個是米吉多王,
22 sarkin Kedesh, ɗaya sarkin Yokneyam a Karmel, ɗaya
一個是基低斯王,一個是靠近迦密的約念王,
23 sarkin Dor (A Nafot Dor), ɗaya sarkin Goyim a Gilgal, ɗaya
一個是多珥山岡的多珥王,一個是吉甲的戈印王,
24 sarki Tirza, ɗaya. Duka-duka dai sarakuna talatin da ɗaya ne.
一個是得撒王;共計三十一個王。

< Yoshuwa 12 >