< Yunana 2 >

1 Daga ciki cikin kifi, Yunana ya yi addu’a ga Ubangiji Allahnsa.
And Jonas prayed to the Lord his God out of the belly of the fish.
2 Ya ce, “A cikin damuwata na yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini. Daga cikin zurfi kabari na yi kiran neman taimako, ka kuwa saurari kukata. (Sheol h7585)
And he said: I cried out of my affliction to the Lord, and he heard me: I cried out of the belly of hell, and thou hast heard my voice. (Sheol h7585)
3 Cikin tashin hankali, ka jefa ni cikin zurfafa, a tsakiyar teku, ka kuma jujjuya ni a cikin ruwa; dukan raƙuman ruwanka da ambaliyarka sun bi ta kaina.
And thou hast cast me forth into the deep in the heart of the sea, and a flood hath compassed me: all thy billows, and thy waves have passed over me.
4 Sai na ce, ‘An kore ni daga fuskarka; duk da haka zan sāke duba wajen haikalinka mai tsarki.’
And I said: I am cast away out of the sight of thy eyes: but yet I shall see thy holy temple again.
5 Ruwayen da suke kewaye da ni sun yi mini barazana, zurfi kuma ya kewaye ni, ciyayin ruwa suna nannaɗe kewaye da ni.
The waters compassed me about even to the soul: the deep hath closed me round about, the sea hath covered my head.
6 Na nutsa har ƙarƙashin tuddai; a ƙarƙashin duniya, ka rufe ni har abada. Amma ka dawo da raina daga rami, Ya Ubangiji Allahna.
I went down to the lowest parts of the mountains: the bars of the earth have shut me up for ever: and thou wilt bring up my life from corruption, O Lord my God.
7 “Sa’ad da na ji raina yana rabuwa da ni, na tuna da kai ya Ubangiji, addu’ata kuma ta kai gare ka, a haikalinka mai tsarki.
When my soul was in distress within me, I remembered the Lord: that my prayer may come to thee, unto thy holy temple.
8 “Waɗanda suka maƙale wa gumaka marasa amfani, sukan ƙyale alherin da zai kasance nasu.
They that are vain observe vanities, forsake their own mercy.
9 Amma ni, da waƙar godiya, zan miƙa tawa hadaya gare ka. Abin da na yi alkawari, shi ne zan yi. Ceto yakan zo ne kawai daga wurin Ubangiji.”
But I with the voice of praise will sacrifice to thee: I will pay whatsoever I have vowed for my salvation to the Lord.
10 Sai Ubangiji ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunana a gaɓan teku.
And the Lord spoke to the fish: and it vomited out Jonas upon the dry land.

< Yunana 2 >