< Yohanna 7 >

1 Bayan wannan, sai Yesu ya yi ta zagawa a cikin Galili, da ganga bai yarda yă je Yahudiya ba domin Yahudawa a can suna nema su kashe shi.
And after this Jesus walked in Galilee: for he would not walk in Judea, because the Jews sought to kill him.
2 Amma sa’ad da Bikin Tabanakul na Yahudawa ya yi kusa,
Now the feast of tabernacles, a feast of the Jews, was near.
3 sai’yan’uwan Yesu suka ce masa, “Ya kamata ka bar nan ka tafi Yahudiya, don almajiranka su ga ayyukan banmamaki da kake yi.
Then his brothers said to him: Depart hence, and go into Judea, that your disciples may see your works which you do;
4 Ba wanda yake so a san shi da zai yi abu a ɓoye. Da yake kana yin waɗannan abubuwa, sai ka nuna kanka ga duniya.”
for no one does any thing in secret, while he himself seeks to be before the public. If you do these things, show yourself to the world.
5 Domin ko’yan’uwansa ma ba su gaskata da shi ba.
For neither did his brothers believe on him.
6 Saboda haka Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna; amma a gare ku kowane lokaci daidai ne.
Then Jesus said to them: My time has not yet come; but your time is always ready.
7 Duniya ba za tă iya ƙinku ba, amma ni take ƙi domin ina shaida cewa ayyukanta mugaye ne.
The world can not hate you; but me it hates, because I testify of it, that its works are evil.
8 Ku ku tafi Bikin, ba zan haura zuwa wannan Bikin ba yanzu, domin lokacina bai yi ba tukuna.”
Do you go up to this feast. I go not up now to this feast, because my time has not yet fully come.
9 Da ya faɗa haka, sai ya dakata a Galili.
These things said he to them, and remained in Galilee.
10 Amma fa, bayan’yan’uwansa suka tafi Bikin, shi ma ya tafi, ba a fili ba, amma a ɓoye.
But when his brothers had gone up, then he also went up to the feast, not openly, but, as it were, in secret.
11 A Bikin kuwa, Yahudawa suka yi ta nemansa, suna cewa, “Ina mutumin yake?”
Then the Jews sought for him at the feast, and said: Where is he?
12 A cikin taron kuwa aka yi ta raɗe-raɗe game da shi. Waɗansu suka ce, “Shi mutumin kirki ne.” Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, ai, ruɗin mutane yake.”
And there was much murmuring among the multitudes concerning him. Some said: He is a good man. Others said: No; but he deceives the multitude.
13 Amma ba wanda ya ce kome a fili game da shi don tsoron Yahudawa.
However, no one spoke openly of him, for fear of the Jews.
14 Sai bayan da aka kai tsakiyar Bikin, sa’an nan Yesu ya haura zuwa filin haikali ya fara koyarwa.
Now in the middle of the feast, Jesus went up into the temple, and taught.
15 Yahudawa suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya wannan mutum ya sami wannan sani haka ba tare da ya yi wani karatu ba?”
And the Jews were astonished, and said: How has this man a knowledge of letters, having never been taught?
16 Yesu ya amsa ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni.
Then Jesus answered and said: My teaching is not mine, but his who sent me.
17 Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai gane ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana.
If any one will do his will, he shall know with respect to the teaching, whether it is of God, or I speak of myself.
18 Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi.
He who speaks of himself, seeks his own glory; he who seeks the glory of him that sent him, he is true, and there is no unrighteousness in him.
19 Ashe, ba Musa ba ne ya ba ku Doka? Duk da haka ba ko ɗayanku da yake kiyaye Dokar. Me ya sa kuke nema ku kashe ni?”
Did not Moses give you the law? and not one of you keeps the law. Why do you seek to kill me?
20 Taron suka amsa suka ce, “Kana da aljani, wane ne yake so yă kashe ka?”
The multitude answered and said: You have a demon: who seeks to kill you?
21 Yesu ya ce musu, “Na yi abin banmamaki ɗaya, dukanku kuwa kuka yi mamaki.
Jesus answered and said to them: I have done one work, and you are all astonished on account of this.
22 Duk da haka, domin Musa ya bar muku kaciya (ko da yake a gaskiya, ba daga wurin Musa ne ya fito ba, sai dai daga wurin kakannin kakanninku), ga shi kuna yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci.
Moses gave you circumcision, (not that it is of Moses, but of the fathers, ) and you circumcise a man on the sabbath-day.
23 To, in za a iya yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci don kada a karya dokar Musa, don me kuke fushi da ni saboda na warkar da mutum a ranar Asabbaci?
If a man receives circumcision on the sabbath-day, that the law of Moses may not be broken, are you angry with me, because I have restored the entire man to health on the sabbath-day?
24 Ku daina yin shari’a bisa ga ganin ido, sai dai ku yi shari’a bisa ga adalci.”
Judge not according to appearance, but judge righteous judgment.
25 A nan ne fa waɗansu mutane daga Urushalima suka fara tambaya suna cewa, “Ashe, ba wannan mutum ne suke nema su kashe ba?
Then said some of the men of Jerusalem: Is not this he whom they seek to kill?
26 Ga shi nan yana magana a fili, su kuma ba su ce masa uffam ba. Ko hukumomi sun yarda cewa shi ne Kiristi?
and, lo, he is speaking boldly, and they say nothing to him. Have the rulers really learned that this is the Christ?
27 Mun dai san inda mutumin nan ya fito; amma sa’ad da Kiristi ya zo ba wanda zai san inda ya fito.”
But we know this man, whence he is. But when the Christ comes, no one knows whence he is.
28 Yesu yana cikin koyarwa a filin haikali ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “I, kun san ni, kun kuma san inda na fito. Ban zo don kaina ba, sai dai shi da ya aiko ni mai gaskiya ne. Ba ku san shi ba,
Then Jesus cried out in the temple, as he was teaching, and said: You both know me, and you know whence I am; and I have not come of myself, but he who sent me is true, whom you know not.
29 amma na san shi, domin ni daga wurinsa ne, kuma shi ya aiko ni.”
But I know him, because I am from him, and he has sent me.
30 Da jin haka, sai suka yi ƙoƙari su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna.
Then they sought to take him; yet no one laid his hand on him, because his hour had not yet come.
31 Duk da haka, da yawa a cikin taron suka ba da gaskiya gare shi. Suka ce, “Sa’ad da Kiristi ya zo, zai yi abubuwan banmamaki fiye da na wannan mutum ne?”
And many of the multitude believed on him, and said: When the Christ comes, will he do more signs than these which this man has done?
32 Farisiyawa suka ji taron suna raɗe-raɗen waɗannan abubuwa game da shi. Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki masu gadin haikalin su kama shi.
The Pharisees heard the multitude murmuring such things concerning him; and the Pharisees and chief priests sent attendants to take him.
33 Sai Yesu ya ce, “Ina tare da ku na ɗan ƙanƙanin lokaci ne kawai, sa’an nan zan koma wurin wanda ya aiko ni.
Then Jesus said to them: Yet a little while I am with you, and I go away to him that sent me.
34 Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba; inda nake kuwa, ba za ku iya zuwa ba.”
You will seek me, and shall not find me; and where I am, you can not come.
35 Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina mutumin nan yake niyyar tafiya da ba za mu iya samunsa ba? Zai je wurin mutanenmu da suke zaune warwatse a cikin Hellenawa, yă kuma koya wa Hellenawa ne?
Then the Jews said among themselves: Whither is this man about to go, that we shall not find him? Is he about to go to those who are dispersed among the Greeks, and to teach the Greeks?
36 Me yake nufi da ya ce, ‘Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba,’ da kuma ‘Inda nake, ba za ku iya zuwa ba’?”
What means this saying which he uttered, You will seek me, and will not find me; and, Where I am you can not come?
37 A rana ta ƙarshe kuma mafi girma ta Bikin, Yesu ya tsaya ya yi magana da babbar murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa, yă zo wurina yă sha.
On the last day, the great day of the feast, Jesus stood and cried, saying: If any one thirst, let him come to me and drink.
38 Duk wanda ya gaskata da ni, kamar yadda Nassi ya ce, kogunan ruwa masu rai za su gudana daga cikinsa.”
He that believes on me, as the scripture has said, from his inner self shall flow rivers of living water.
39 Da wannan yana nufin Ruhu ke nan, wanda waɗanda suka gaskata da shi za su karɓa daga baya. Har yă zuwa wannan lokaci ba a ba da Ruhu ba tukuna, da yake ba a riga an ɗaukaka Yesu ba.
But this he spoke of the Spirit, which those who believe on him were about to receive; for the Holy Spirit had not yet been given, because Jesus had not yet been glorified.
40 Da jin kalmominsa, waɗansu mutane suka ce, “Ba shakka, mutumin nan shi ne Annabin.”
Therefore, many of the multitude, when they had heard this word, said: This is, in truth, the prophet.
41 Waɗansu suka ce, “Shi ne Kiristi.” Waɗansu har wa yau suka ce, “Yaya Kiristi zai fito daga Galili?
Others said: This is the Christ. But others said: Does the Christ come out of Galilee?
42 Nassi bai ce Kiristi zai fito daga zuriyar Dawuda, daga kuma Betlehem garin da Dawuda ya zauna ba?”
Has not the scripture said that the Christ comes from the posterity of David, and from Bethlehem, the town where David was?
43 Sai mutanen suka rabu saboda Yesu.
So there was a division among the multitude because of him.
44 Waɗansu suka so su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi.
And some of them desired to take him; but no one laid hands on him.
45 A ƙarshe masu gadin haikali suka koma wurin manyan firistocin da Farisiyawa, waɗanda suka tambaye su cewa, “Don me ba ku kawo shi nan ba?”
Then came the attendants to the chief priests and the Pharisees; and they said to them: Why have you not brought him?
46 Sai masu gadin suka ce, “Kai, babu wanda ya taɓa magana kamar wannan mutum.”
The attendants answered: Never did man speak like this man.
47 Sai Farisiyawa suka amsa cikin fushi suka ce, “Af, kuna nufi har da ku ma ya ruɗe ku ke nan?
Then the Pharisees answered them: Are you also deceived?
48 Akwai wani daga cikin masu mulki ko cikin Farisiyawan da ya gaskata da shi?
Has any one of the rulers, or of the Pharisees believed on him?
49 A’a! Sai dai wannan taron da ba su san kome game da Doka ba, la’anannu ne.”
But this multitude that know not the law are cursed.
50 Nikodimus, wanda ya je wurin Yesu dā, wanda kuma yake ɗayansu ya ce,
Nicodemus said to them (he that came to Jesus by night, being one of them):
51 “Ashe, dokarmu takan hukunta mutum ba tare da an fara ji daga bakinsa game da abin da yake yi ba?”
Does our law condemn a man unless it first hear from him, and know what he does?
52 Sai suka amsa suka ce, “Kai ma daga Galili ne? Bincika ka gani, za ka iske cewa ba annabin da zai fito daga Galili.”
They answered and said to him: Are you also from Galilee? Search, and see that out of Galilee arises no prophet.
53 Sai kowannensu ya koma gidansa.
And every one departed to his own house.

< Yohanna 7 >