< Yohanna 6 >
1 Ɗan lokaci bayan wannan, sai Yesu ya ƙetare zuwa gaɓar mai nesa na Tekun Galili (wato, Tekun Tibariya),
After this Jesus went away across the Lake of Galilee (that is, the Lake of Tiberias).
2 sai taro mai yawa na mutane suka bi shi domin sun ga abubuwan banmamakin da ya yi ga marasa lafiya.
A vast multitude followed Him, because they witnessed the miracles on the sick which He was constantly performing.
3 Sa’an nan Yesu ya hau gefen dutse ya zauna tare da almajiransa.
Then Jesus went up the hill, and sat there with His disciples.
4 Bikin Ƙetarewan Yahudawa ya yi kusa.
The Jewish Festival, the Passover, was at hand.
5 Sa’ad da Yesu ya ɗaga kai ya ga taro mai yawa suna zuwa wajensa, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayi burodi saboda mutanen nan su ci?”
And when He looked round and saw an immense crowd coming towards Him, He said to Philip, "Where shall we buy bread for all these people to eat?"
6 Ya yi wannan tambayar don yă gwada shi ne kawai, gama ya riga ya san abin da zai yi.
He said this to put Philip to the test, for He Himself knew what He was going to do.
7 Sai Filibus ya amsa ya ce, “Kai, ko albashin wata takwas ba zai iya sayan isashen burodin da kowa zai ɗan samu kaɗan ba!”
"Seven pounds' worth of bread," replied Philip, "is not enough for them all to get even a scanty meal."
8 Sai wani daga cikin almajiransa Andarawus, ɗan’uwan Bitrus, ya yi magana,
One of His disciples, Andrew, Simon Peter's brother, said to Him,
9 “Ga wani yaro da ƙananan burodin sha’ir guda biyar da ƙananan kifi biyu, amma me wannan zai yi wa yawan mutanen nan.”
"There is a boy here with five barley loaves and a couple of fish: but what is that among so many?"
10 Yesu ya ce, “Ku sa mutanen su zauna.” Wurin kuwa akwai ciyawa da sosai, sai maza suka zazzauna, sun kai wajen dubu biyar.
"Make the people sit down," said Jesus. The ground was covered with thick grass; so they sat down, the adult men numbering about 5,000.
11 Sa’an nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.
Then Jesus took the loaves, and after giving thanks He distributed them to those who were resting on the ground; and also the fish in like manner--as much as they desired.
12 Sa’ad da duk suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka rage. Kada kome yă lalace.”
When all were fully satisfied, He said to His disciples, "Gather up the broken portions that remain over, so that nothing be lost."
13 Saboda haka suka tattara su suka kuma cika kwanduna goma sha biyu na gutsattsarin burodin sha’ir biyar nan da suka ragu bayan kowa ya ci.
Accordingly they gathered them up; and with the fragments of the five barley loaves--the broken portions that remained over after they had done eating--they filled twelve baskets.
14 Bayan mutanen suka ga abin banmamakin da Yesu ya yi, sai suka fara cewa, “Lalle, wannan shi ne Annabin nan mai zuwa duniya.”
Thereupon the people, having seen the miracle He had performed, said, "This is indeed the Prophet who was to come into the world."
15 Da Yesu ya gane suna shirin su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.
Perceiving, however, that they were about to come and carry Him off by force to make Him a king, Jesus withdrew again up the hill alone by Himself.
16 Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara zuwa tafki,
When evening came on, His disciples went down to the Lake.
17 inda suka shiga jirgin ruwa suka tasar wa haye tafkin zuwa Kafarnahum. A lokacin kuwa duhu ya yi, Yesu kuma bai riga ya zo wurinsu ba tukuna.
There they got on board a boat, and pushed off to cross the Lake to Capernaum. By this time it had become dark, and Jesus had not yet joined them.
18 Iska mai ƙarfi kuwa tana bugowa, ruwaye kuma suka fara hauka.
The Lake also was getting rough, because a strong wind was blowing.
19 Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko uku da rabi, sai suka ga Yesu ya kusato jirgin ruwan, yana takawa a kan ruwan; sai suka tsorata.
When, however, they had rowed three or four miles, they saw Jesus walking on the water and coming near the boat.
20 Amma ya ce musu, “Ni ne; kada ku ji tsoro.”
They were terrified; but He called to them. "It is I," He said, "do not be afraid."
21 Sa’an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin ruwan, nan da nan kuwa jirgin ya kai gaɓar da za su.
Then they were willing to take Him on board; and in a moment the boat reached the shore at the point to which they were going.
22 Kashegari taron da suka tsaya a wancan ƙetaren tafkin suka lura cewa jirgin ruwa ɗaya ne yake a can dā ma, kuma sun lura cewa Yesu bai shiga ciki tare da almajiransa ba, gama sun tashi su kaɗai.
Next morning the crowd who were still standing about on the other side of the Lake found that there had been but one small boat there, and they had seen that Jesus did not go on board with His disciples, but that His disciples went away without Him.
23 Sai ga waɗansu jiragen ruwa daga Tibariya suka iso kusa da wurin da mutanen suka ci burodi bayan Ubangiji ya yi godiya.
Yet a number of small boats came from Tiberias to the neighbourhood of the place where they had eaten the bread after the Lord had given thanks.
24 Da taron suka lura cewa Yesu da almajiransa ba sa can, sai suka shiga jiragen ruwa suka tafi Kafarnahum neman Yesu.
When however the crowd saw that neither Jesus nor His disciples were there, they themselves also took boats and came to Capernaum to look for Jesus.
25 Da suka same shi a wancan ƙetaren tafkin, sai suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, yaushe ka kai nan?”
So when they had crossed the Lake and had found Him, they asked Him, "Rabbi, when did you come here?"
26 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga abubuwan banmamaki ba, sai dai domin kun ci burodi kun ƙoshi.
"In most solemn truth I tell you," replied Jesus, "that you are searching for me not because you have seen miracles, but because you ate the loaves and had a hearty meal.
27 Kada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har yă zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa.” (aiōnios )
Bestow your pains not on the food which perishes, but on the food that remains unto the Life of the Ages--that food which will be the Son of Man's gift to you; for on Him the Father, God, has set His seal." (aiōnios )
28 Sai suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi don mu aikata ayyukan da Allah yake so?”
"What are we to do," they asked, "in order to carry out the things that God requires?"
29 Yesu ya amsa, “Aikin Allah shi ne, a gaskata da wanda ya aiko.”
"This," replied Jesus, "is above all the thing that God requires--that you should be believers in Him whom He has sent."
30 Sai suka tambaye shi, “Wace abin banmamaki ce za ka yi don mu gani mu kuwa gaskata ka? Me za ka yi?
"What miracle then," they asked, "do you perform for us to see and become believers in you? What do you do?
31 Kakannin-kakanninmu sun ci Manna a hamada; kamar yadda yake a rubuce, ‘Ya ba su burodi daga sama su ci.’”
Our forefathers ate the manna in the Desert, as it is written, 'He gave them bread out of Heaven to eat'."
32 Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba Musa ne ya ba ku burodi daga sama ba, sai dai Ubana ne yake ba ku burodi na gaskiya daga sama.
"In most solemn truth I tell you," replied Jesus, "that Moses did not give you the bread out of Heaven, but my Father is giving you the bread--the true bread--out of Heaven.
33 Gama burodin Allah shi ne wanda yake saukowa daga sama, yana kuma ba wa duniya rai.”
For God's bread is that which comes down out of Heaven and gives Life to the world."
34 Sai suka ce, “Ranka yă daɗe, daga yanzu ka dinga ba mu wannan burodi.”
"Sir," they said, "always give us that bread."
35 Sa’an nan Yesu ya furta cewa, “Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.
"I am the bread of Life," replied Jesus; "he who comes to me shall never hunger, and he who believes in me shall never, never thirst.
36 Amma kamar yadda na faɗa muku, kun gan ni duk da haka ba ku gaskata ba.
But it is as I have said to you: you have seen me and yet you do not believe.
37 Duk waɗanda Uba ya ba ni za su zo wurina, kuma duk wanda ya zo wurina ba zan kore shi ba ko kaɗan.
Every one whom the Father gives me will come to me, and him who comes to me I will never on any account drive away.
38 Gama na sauko daga sama ba don in cika nufin kaina ba sai dai don in cika nufin shi wanda ya aiko ni.
For I have left Heaven and have come down to earth not to seek my own pleasure, but to do the will of Him who sent me.
39 Nufin wanda ya aiko ni kuwa shi ne, kada in yar da ko ɗaya daga cikin duk waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a rana ta ƙarshe.
And this is the will of Him who sent me, that of all that He has given me I should lose nothing, but should raise it to life on the last day.
40 Gama nufin Ubana shi ne, duk wanda yake duban Ɗan, ya kuma gaskata shi zai sami rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.” (aiōnios )
For this is my Father's will, that every one who fixes his gaze on the Son of God and believes in Him should have the Life of the Ages, and I will raise him to life on the last day." (aiōnios )
41 Da jin haka, Yahudawa suka fara gunaguni a kansa, domin ya ce, “Ni ne burodin da ya sauka daga sama.”
Now the Jews began to find fault about Him because of His claiming to be the bread which came down out of Heaven.
42 Suka ce, “Kai, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusuf, wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa duk mun san su? Yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko daga sama?’”
They kept asking, "Is not this man Joseph's son? Is he not Jesus, whose father and mother we know? What does he mean by now saying, 'I have come down out of Heaven'?"
43 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ku daina gunaguni a junanku.
"Do not thus find fault among yourselves," replied Jesus;
44 Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uban da ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.
"no one can come to me unless the Father who sent me draws him; then I will raise him to life on the last day.
45 A rubuce yake a cikin Annabawa cewa, ‘Allah zai koyar da dukansu.’Duk wanda ya saurari Uba, ya kuma koyi daga wurinsa, zai zo wurina.
It stands written in the Prophets, 'And they shall all of them be taught by God'. Every one who listens to the Father and learns from Him comes to me.
46 Ba wanda ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda ya zo daga Allah; shi ne kaɗai ya taɓa ganin Uban.
No one has ever seen the Father--except Him who is from God. He has seen the Father.
47 Gaskiya nake gaya muku, wanda ya gaskata yana da rai madawwami. (aiōnios )
"In most solemn truth I tell you that he who believes has the Life of the Ages. (aiōnios )
49 Kakannin-kakanninku sun ci Manna a hamada, duk da haka suka mutu.
Your forefathers ate the manna in the Desert, and they died.
50 Amma ga burodin da ya sauko daga sama, wanda mutum zai iya ci, ba zai kuma mutu ba.
Here is the bread that comes down out of Heaven that a man may eat it and not die.
51 Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.” (aiōn )
I am the living bread come down out of Heaven. If a man eats this bread, he shall live for ever. Moreover the bread which I will give is my flesh given for the life of the world." (aiōn )
52 Sai Yahudawa suka fara gardama mai tsanani a junansu suna cewa, “Yaya wannan mutum zai ba mu naman jikinsa mu ci?”
This led to an angry debate among the Jews. "How can this man," they argued, "give us his flesh to eat?"
53 Sai Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba.
"In most solemn truth I tell you," said Jesus, "that unless you eat the flesh of the Son of Man and drink His blood, you have no Life in you.
54 Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe. (aiōnios )
He who eats my flesh and drinks my blood has the Life of the Ages, and I will raise him up on the last day. (aiōnios )
55 Gama naman jikina abinci ne na gaskiya jinina kuma abin sha ne na gaskiya.
For my flesh is true food, and my blood is true drink.
56 Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana cikina, ni kuma ina cikinsa.
He who eats my flesh and drinks my blood remains in union with me, and I remain in union with him.
57 Kamar dai yadda Uba mai rai ya aiko ni, ina kuma rayuwa ta saboda shi, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni.
As the ever-living Father has sent me, and I live because of the Father, so also he who eats me will live because of me.
58 Wannan shi ne burodin da ya sauko daga sama. Kakannin-kakanninku sun ci Manna suka kuma mutu, amma duk wanda yake cin wannan burodi zai rayu har abada.” (aiōn )
This is the bread which came down out of Heaven; it is unlike that which your forefathers ate--for they ate and yet died. He who eats this bread shall live for ever." (aiōn )
59 Ya faɗi wannan ne lokacin da yake koyarwa a cikin majami’a a Kafarnahum.
Jesus said all this in the synagogue while teaching at Capernaum.
60 Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan koyarwa tana da wuya. Wa zai iya yarda da ita?”
Many therefore of His disciples, when they heard it, said, "This is hard to accept. Who can listen to such teaching?"
61 Da yake ya san almajiransa suna gunaguni game da wannan, sai Yesu ya ce musu, “Wannan ya ɓata muku rai ne?
But, knowing in Himself that His disciples were dissatisfied about it, Jesus asked them,
62 Me za ku ce ke nan, in kuka gan Ɗan Mutum yana hawa zuwa inda yake dā!
"Does this seem incredible to you? What then if you were to see the Son of Man ascending again where He was before?
63 Ruhu ne yake ba da rai; jikin kam, ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku, Ruhu ne, da kuma rai.
It is the spirit which gives Life. The flesh confers no benefit whatever. The words I have spoken to you are spirit and are Life.
64 Duk da haka akwai waɗansunku da ba su gaskata ba.” Gama Yesu ya sani tun farko, waɗanda ba su gaskata ba, da kuma wanda zai bashe shi.
But there are some of you who do not believe." For Jesus knew from the beginning who those were that did not believe, and who it was that would betray Him.
65 Ya ci gaba da cewa, “Shi ya sa na faɗa muku cewa ba mai iya zuwa wurina, sai dai Uba ya yardar masa.”
So He added, "That is why I told you that no one can come to me unless it be granted him by the Father."
66 Daga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina bin sa.
Thereupon many of His disciples left Him and went away, and no longer associated with Him.
67 Sai Yesu ya tambayi Sha Biyun, “Ku ma za ku tafi ne?”
Jesus therefore appealed to the Twelve. "Will you go also?" He asked.
68 Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami. (aiōnios )
"Master," replied Simon Peter, "to whom shall we go? Your teachings tell us of the Life of the Ages. (aiōnios )
69 Mun gaskata mun kuma san cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”
And we have come to believe and know that you are indeed the Holy One of God."
70 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ba ni na zaɓe ku Sha Biyu ba? Amma ɗayanku Iblis ne!”
"Did not I choose you--the Twelve?" said Jesus, "and even of you one is a devil."
71 (Yana nufin Yahuda, ɗan Siman Iskariyot, wanda, ko da yake ɗaya ne cikin Sha Biyun, zai bashe shi daga baya.)
He alluded to Judas, the son of Simon the Iscariot. For he it was who, though one of the Twelve, was afterwards to betray Him.