< Yohanna 6 >

1 Ɗan lokaci bayan wannan, sai Yesu ya ƙetare zuwa gaɓar mai nesa na Tekun Galili (wato, Tekun Tibariya),
這些事以後,耶穌往加里肋亞海,即提庇黎雅海的對岸去了。
2 sai taro mai yawa na mutane suka bi shi domin sun ga abubuwan banmamakin da ya yi ga marasa lafiya.
大批群眾,因為看見他在患病者身上所行的神跡,都跟隨著他。
3 Sa’an nan Yesu ya hau gefen dutse ya zauna tare da almajiransa.
耶穌上了山,和他的門徒一起坐在那裡。
4 Bikin Ƙetarewan Yahudawa ya yi kusa.
那時,猶太人的慶節,即逾越節,已臨近了。
5 Sa’ad da Yesu ya ɗaga kai ya ga taro mai yawa suna zuwa wajensa, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayi burodi saboda mutanen nan su ci?”
耶穌舉目看見大批群眾來到他前,就對斐理伯說:「我們從那裏買餅給這些人吃呢?」
6 Ya yi wannan tambayar don yă gwada shi ne kawai, gama ya riga ya san abin da zai yi.
他說這話,是為試探斐理伯;他自己原知道要做什麼。
7 Sai Filibus ya amsa ya ce, “Kai, ko albashin wata takwas ba zai iya sayan isashen burodin da kowa zai ɗan samu kaɗan ba!”
斐理伯回答說: 「就是二百塊「德納」的餅,也不夠每人分得一小塊。」
8 Sai wani daga cikin almajiransa Andarawus, ɗan’uwan Bitrus, ya yi magana,
有一個門徒,即西滿伯多祿的哥哥安德肋說:「
9 “Ga wani yaro da ƙananan burodin sha’ir guda biyar da ƙananan kifi biyu, amma me wannan zai yi wa yawan mutanen nan.”
這裏有一個兒童,他有五個大麥餅和兩條魚;但是為這麼多的人,這算得什麼?」
10 Yesu ya ce, “Ku sa mutanen su zauna.” Wurin kuwa akwai ciyawa da sosai, sai maza suka zazzauna, sun kai wajen dubu biyar.
耶穌說: 「你們叫眾人坐下罷! 」在那地方有許多青草,於是人們便坐下,男人約有五千。
11 Sa’an nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.
耶穌就拿起餅,祝謝後,分給坐下的人;對於魚也照樣作了;讓眾人任意吃。
12 Sa’ad da duk suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka rage. Kada kome yă lalace.”
他們吃飽以後,耶穌向門徒說: 「把剩下的碎塊收集起來,免得糟蹋了。」
13 Saboda haka suka tattara su suka kuma cika kwanduna goma sha biyu na gutsattsarin burodin sha’ir biyar nan da suka ragu bayan kowa ya ci.
他們就把人吃後所剩的五個大麥餅的碎塊,收集起來,裝滿了十二筐。
14 Bayan mutanen suka ga abin banmamakin da Yesu ya yi, sai suka fara cewa, “Lalle, wannan shi ne Annabin nan mai zuwa duniya.”
眾人見了耶穌所行的神跡,就說: 「這人確實是那要來到世界上的先知。」
15 Da Yesu ya gane suna shirin su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.
耶穌看出他們要來強迫他,立他為王,就獨自又退避到山裏去了。
16 Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara zuwa tafki,
到了晚上,他的門徒下到海邊,
17 inda suka shiga jirgin ruwa suka tasar wa haye tafkin zuwa Kafarnahum. A lokacin kuwa duhu ya yi, Yesu kuma bai riga ya zo wurinsu ba tukuna.
上船要到對岸的葛法翁去。天已黑了,耶穌還沒有有來到他們那裡。
18 Iska mai ƙarfi kuwa tana bugowa, ruwaye kuma suka fara hauka.
海上因起了大風,便翻騰起來。
19 Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko uku da rabi, sai suka ga Yesu ya kusato jirgin ruwan, yana takawa a kan ruwan; sai suka tsorata.
當他們搖櫓大約過了二十五或三十「斯塔狄」時,看見耶穌在海面行走,臨近了船,便害怕起來。
20 Amma ya ce musu, “Ni ne; kada ku ji tsoro.”
但他卻向他們說: 「是我,不要害怕!」
21 Sa’an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin ruwan, nan da nan kuwa jirgin ya kai gaɓar da za su.
他們便欣然接他上船,船就立時到了他們所要去的地方。
22 Kashegari taron da suka tsaya a wancan ƙetaren tafkin suka lura cewa jirgin ruwa ɗaya ne yake a can dā ma, kuma sun lura cewa Yesu bai shiga ciki tare da almajiransa ba, gama sun tashi su kaɗai.
第二天,留在海對岸的群眾,看見只有一隻小船留在那裡也知道耶穌沒有同他的門徒一起上船,只有他的門徒走了──
23 Sai ga waɗansu jiragen ruwa daga Tibariya suka iso kusa da wurin da mutanen suka ci burodi bayan Ubangiji ya yi godiya.
然而從提庇黎雅有別的小船來到了,靠近吾主祝謝後,人們吃餅的地方──
24 Da taron suka lura cewa Yesu da almajiransa ba sa can, sai suka shiga jiragen ruwa suka tafi Kafarnahum neman Yesu.
當群眾一發覺耶穌和他的門徒都不在那裡時,他們便上了那些小船,往葛法翁找耶穌去了。
25 Da suka same shi a wancan ƙetaren tafkin, sai suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, yaushe ka kai nan?”
當群眾在海對岸找著他時,就對他說: 「辣彼,你什麼時候到了這裏?」
26 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga abubuwan banmamaki ba, sai dai domin kun ci burodi kun ƙoshi.
耶穌回答說: 「我實實在在告訴你們: 你們尋找我,並不是因為看到了神跡,而是因為吃餅吃飽了。
27 Kada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har yă zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa.” (aiōnios g166)
你們不要為那可損壞的食糧勞碌,而要為那存留到永生的食糧勞碌,即人子所要賜給你們的,因為他是天主聖父所印證的。」 (aiōnios g166)
28 Sai suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi don mu aikata ayyukan da Allah yake so?”
他們問說: 「我們該做什麼,才算做天主的事業呢?」
29 Yesu ya amsa, “Aikin Allah shi ne, a gaskata da wanda ya aiko.”
耶穌回答說: 「天主要你們所做的事業,就是要你們信任他所派遣來的。」
30 Sai suka tambaye shi, “Wace abin banmamaki ce za ka yi don mu gani mu kuwa gaskata ka? Me za ka yi?
他們又說: 「那麼,你行什麼神跡給我們看,好叫我們信服你呢?你要行什麼事呢?
31 Kakannin-kakanninmu sun ci Manna a hamada; kamar yadda yake a rubuce, ‘Ya ba su burodi daga sama su ci.’”
我們的祖先在曠野裏吃過「瑪納」,正如經上所記載的:「他從天上賜給了他們食物吃。』
32 Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba Musa ne ya ba ku burodi daga sama ba, sai dai Ubana ne yake ba ku burodi na gaskiya daga sama.
於是耶穌向他們說: 「我實實在在告訴你們: 並不是梅瑟賜給了你們那從天上來的食糧,而是我父現今賜給你們從天上來的真正的食糧,
33 Gama burodin Allah shi ne wanda yake saukowa daga sama, yana kuma ba wa duniya rai.”
因為天主的食糧,是那由天降下,並賜給世界生命的。」
34 Sai suka ce, “Ranka yă daɗe, daga yanzu ka dinga ba mu wannan burodi.”
他們便說: 「主! 你就把這樣的食糧常常賜給我們罷! 」
35 Sa’an nan Yesu ya furta cewa, “Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.
耶穌回答說:「我就是生命的食糧,到我這裏來的,永不會饑餓;信從我的,總不會渴。
36 Amma kamar yadda na faɗa muku, kun gan ni duk da haka ba ku gaskata ba.
但是我向你們說過: 你們看見了我,仍然不信。
37 Duk waɗanda Uba ya ba ni za su zo wurina, kuma duk wanda ya zo wurina ba zan kore shi ba ko kaɗan.
凡父交給我的,必到我這裏來;而到我這裏來的,我必不把他拋棄於外,
38 Gama na sauko daga sama ba don in cika nufin kaina ba sai dai don in cika nufin shi wanda ya aiko ni.
因為我從天降下,不是為執行我的旨意。
39 Nufin wanda ya aiko ni kuwa shi ne, kada in yar da ko ɗaya daga cikin duk waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a rana ta ƙarshe.
派遣我來者的旨意就是:凡他交給我的,叫我連一個也不失掉,而且在末日還要使他復活,
40 Gama nufin Ubana shi ne, duk wanda yake duban Ɗan, ya kuma gaskata shi zai sami rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.” (aiōnios g166)
因為這是我父的旨意: 凡看見子,並信從子的,必獲得永生;並且在末日,我要使他復活。」 (aiōnios g166)
41 Da jin haka, Yahudawa suka fara gunaguni a kansa, domin ya ce, “Ni ne burodin da ya sauka daga sama.”
猶太人遂對耶穌竊竊私議,因為他說: 我是從天上降下來的食糧。
42 Suka ce, “Kai, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusuf, wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa duk mun san su? Yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko daga sama?’”
他們說:「這人不是若瑟的兒子耶穌麼? 他的父親和母親,我們豈不是都認識麼? 怎麼他竟說: 我是從天上降下來的呢?」
43 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ku daina gunaguni a junanku.
耶穌回答說: 「你們不要彼此竊竊私議!
44 Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uban da ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.
凡不是派遣我的父所吸引的人,誰也不能到我這裏來,而我在末日要叫他復活。
45 A rubuce yake a cikin Annabawa cewa, ‘Allah zai koyar da dukansu.’Duk wanda ya saurari Uba, ya kuma koyi daga wurinsa, zai zo wurina.
在先知書上記載: 『眾人都要蒙天主的訓誨。』凡由父聽教而學習的,必到我這裏來。
46 Ba wanda ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda ya zo daga Allah; shi ne kaɗai ya taɓa ganin Uban.
這不是說有人看見過父,只有那從天主來的,才看見過父。
47 Gaskiya nake gaya muku, wanda ya gaskata yana da rai madawwami. (aiōnios g166)
我實實在在告訴你們: 信從的人必得永生。 (aiōnios g166)
48 Ni ne burodin rai.
我是生命的食糧。
49 Kakannin-kakanninku sun ci Manna a hamada, duk da haka suka mutu.
你們的祖先在曠野中吃過「瑪納」,卻死了;
50 Amma ga burodin da ya sauko daga sama, wanda mutum zai iya ci, ba zai kuma mutu ba.
這是從天上降下來的食糧,誰吃了,就不死。
51 Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.” (aiōn g165)
我是從天上降下的生活的食糧;誰若吃了這食糧,必要生活直到永遠。」「我所要賜給的食糧,就是我的肉,是為世界的生命而賜給的。」 (aiōn g165)
52 Sai Yahudawa suka fara gardama mai tsanani a junansu suna cewa, “Yaya wannan mutum zai ba mu naman jikinsa mu ci?”
因此,猶太人彼此爭論說: 「這人怎能把他的肉,賜給我們吃呢?」
53 Sai Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba.
耶穌向他們說:「我實實在在告訴你們:你們若不吃人子的肉,不喝他的血,在你們內便沒有生命。
54 Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe. (aiōnios g166)
誰吃我的肉,並喝我的血,必得永生,在末日,我且要叫他復活, (aiōnios g166)
55 Gama naman jikina abinci ne na gaskiya jinina kuma abin sha ne na gaskiya.
因為我的肉,是真實的食品;我的血,是真實的飲料。
56 Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana cikina, ni kuma ina cikinsa.
誰吃我的肉,並喝我的血,便住在我內,我也住在他內。
57 Kamar dai yadda Uba mai rai ya aiko ni, ina kuma rayuwa ta saboda shi, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni.
就如那生活的父派遣了我,我因父而生活;照樣,那吃我的人,也要因我而生活。
58 Wannan shi ne burodin da ya sauko daga sama. Kakannin-kakanninku sun ci Manna suka kuma mutu, amma duk wanda yake cin wannan burodi zai rayu har abada.” (aiōn g165)
這是從天上降下來的食糧,不像祖先吃了「瑪納」仍然死了;誰吃這食糧,必要生活直到永遠。」 (aiōn g165)
59 Ya faɗi wannan ne lokacin da yake koyarwa a cikin majami’a a Kafarnahum.
這些話是耶穌在葛法翁會堂教訓人時說的。
60 Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan koyarwa tana da wuya. Wa zai iya yarda da ita?”
他的門徒中有許多聽了,便說: 「這話生硬,有誰能聽得下去呢?」
61 Da yake ya san almajiransa suna gunaguni game da wannan, sai Yesu ya ce musu, “Wannan ya ɓata muku rai ne?
耶穌自佑他的門徒對這話竊竊私議,便向他們說: 「這話使你們起反感嗎?
62 Me za ku ce ke nan, in kuka gan Ɗan Mutum yana hawa zuwa inda yake dā!
那麼,如果你們看到人子昇到他先前所在的地方去,將怎樣呢?
63 Ruhu ne yake ba da rai; jikin kam, ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku, Ruhu ne, da kuma rai.
使生活的是神,肉一無所用;我給你們所講論的話,就是神,就生命。
64 Duk da haka akwai waɗansunku da ba su gaskata ba.” Gama Yesu ya sani tun farko, waɗanda ba su gaskata ba, da kuma wanda zai bashe shi.
但你們中間有些人,卻不相信。」原來,耶穌從起頭就知道那些人不信,和誰要出賣他。
65 Ya ci gaba da cewa, “Shi ya sa na faɗa muku cewa ba mai iya zuwa wurina, sai dai Uba ya yardar masa.”
所以他又說: 「為此,我對你們說過: 除非蒙父恩賜的,誰也不能到我這裏來。」
66 Daga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina bin sa.
從此,他的門徒中有許多人退去了,不再同他往來。
67 Sai Yesu ya tambayi Sha Biyun, “Ku ma za ku tafi ne?”
於是耶穌向那十二人說: 「難道你們也願走嗎?」
68 Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami. (aiōnios g166)
西滿伯多祿回答說: 「主! 惟有你有永生的話,我們去投奔誰呢? (aiōnios g166)
69 Mun gaskata mun kuma san cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”
我們相信,而且己知道你是天主的聖者。」
70 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ba ni na zaɓe ku Sha Biyu ba? Amma ɗayanku Iblis ne!”
耶穌對他們說: 「我不是揀選了你們十二個人嗎?你們中卻有一個是魔鬼。」
71 (Yana nufin Yahuda, ɗan Siman Iskariyot, wanda, ko da yake ɗaya ne cikin Sha Biyun, zai bashe shi daga baya.)
他是指依斯加略人西滿的兒子猶達斯說的;因為就是這人,十二人中的一個,將要出賣耶穌。

< Yohanna 6 >