< Yohanna 5 >

1 Bayan an ɗan jima, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima don wani bikin Yahudawa.
Afterward there was a Jewish festival, and Jesus went to Jerusalem.
2 To, a Urushalima akwai wani tafki kusa da Ƙofar Tumaki, wanda a yaren Arameyik ake kira Betesda an kuma kewaye shi da shirayi biyar.
Now there is at Jerusalem, nigh the sheep gate, a bath, called, in Hebrew, Bethesda, which has five covered walks.
3 A nan naƙasassu da yawa sukan kwanta, makafi, guragu, shanyayyu.
In these lay a great number of sick, blind, lame, and palsied people, waiting for the moving of the water,
4
(for a messenger at times descended into the bath, and agitated the water; and the first that stepped in, after the agitation of the water, was cured of whatever disease he had.)
5 Akwai wani da yake nan ba shi da amfani shekara talatin da takwas.
Now, there was one there, who had been diseased thirty-eight years.
6 Da Yesu ya gan shi kwance a can ya kuma sami labari cewa ya daɗe a wannan hali, sai ya tambaye shi, “Kana so ka warke?”
Jesus, who saw him lying, and knew that he had been long ill, said to him, Do you desire to be healed?
7 Marar amfanin nan ya ce, “Ranka yă daɗe, ba ni da wanda zai taimaka yă sa ni a cikin tafkin sa’ad da aka motsa ruwan. Yayinda nake ƙoƙarin shiga, sai wani yă riga ni.”
The diseased man answered, Sir, I have no person to put me into the bath, when the water is agitated; but while I am going, another gets down before me.
8 Sai Yesu ya ce masa, “Tashi! Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.”
Jesus said to him, Arise, take up your couch and walk.
9 Nan take mutumin ya warke; ya ɗauki tabarmarsa ya yi tafiya. A ranar da wannan ya faru ranar Asabbaci ce,
Instantly the man was healed, and took up his couch and walked.
10 saboda haka kuwa Yahudawa suka ce wa mutumin da aka warkar, “Yau Asabbaci ne; doka ta hana ka ɗauki tabarmarka.”
Now, that day was the Sabbath. The Jews, therefore, said to him that was cured, This is the Sabbath. It is now lawful for you to carry the couch.
11 Amma ya amsa ya ce, “Mutumin da ya warkar da ni shi ya ce mini, ‘Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.’”
He answered, He who healed me, said to me, Take up your couch and walk.
12 Sai suka tambaye shi suka ce, “Wane ne wannan da ya ce maka ka ɗauke ta ka yi tafiya?”
They asked him then, Who is the man that said to you, Take up your couch and walk?
13 Mutumin da aka warkar kuwa bai ma san ko wane ne ba ne, gama Yesu ya ɓace cikin taron da yake can.
But he that had been healed, knew who it was; for Jesus had slipped away, there being a crowd in the place.
14 Daga baya Yesu ya same shi a haikali ya ce masa, “Ga shi, ka warke. Ka daina yin zunubi, in ba haka ba wani abin da ya fi wannan muni zai iya samunka.”
Jesus, afterward, finding him in the temple, said to him, Behold, you are cured; sin no more, lest something worse befall you.
15 Sai mutumin ya je ya gaya wa Yahudawa cewa Yesu ne ya warkar da shi.
The man went, and told the Jews that it was Jesus who had cured him.
16 To, domin Yesu yana yin waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci, sai Yahudawa suka tsananta masa.
Therefore, the Jews persecuted Jesus, because he had done this on the Sabbath.
17 Yesu ya ce musu, “Ubana yana cikin aikinsa kullum har yă zuwa wannan rana, haka ni ma, ina kan aiki.”
But Jesus answered them, My Father works until now; I also work.
18 Don haka Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi; ba don yă karya Asabbaci kawai ba, har ma yana ce Allah Ubansa ne, yana mai da kansa daidai da Allah.
For this reason the Jews were the more intent to kill him; because he had not only broken the Sabbath, but, by calling God his real Father, had equaled himself to God.
19 Sai Yesu ya ba su wannan amsa cewa, “Gaskiya nake gaya muku, Ɗan ba ya iya yin kome da kansa; yana yin abin da ya ga Ubansa yake yi ne kawai, gama duk abin da Uban yake yi shi ne Ɗan ma yake yi.
Then Jesus addressed them, saying, Most assuredly, I say to you, the Son can do nothing of himself, but as he sees the Father do: for what things soever he does, such does the Son, likewise.
20 Gama Uban yana ƙaunar Ɗan yana kuma nuna masa duk abin da yake yi. I, za ku kuwa yi mamaki, gama zai nuna masa abubuwan da suka fi waɗannan girma.
For the Father loves the Son, and shows him all that he himself does: nay, and will show him greater works than these, which will astonish you.
21 Gama kamar yadda Uban yake tā da matattu yake kuma ba su rai, haka ma Ɗan yake ba da rai ga wanda ya ga dama.
For as the Father raises and quickens the dead, the Son also quickens whom he will:
22 Bugu da ƙari, Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya danƙa dukan hukunci a hannun Ɗan,
for the Father judges no person, having committed the power of judging entirely to the Son,
23 don kowa yă girmama Ɗan kamar yadda yake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan ba ya girmama Uban, da ya aiko shi ke nan.
that all might honor the Son; as they honor the Father. He that honors not the Son, honors not the Father, who sent him.
24 “Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai. (aiōnios g166)
Most assuredly, I say to you, he who hears my doctrine, and believes him who sent me, has eternal life; and shall not suffer condemnation, having passed from death to life. (aiōnios g166)
25 Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu.
Most assuredly, I say to you, the time comes; or, rather, is come, when the dead shall hear the voice of the Son of God; and hearing, they shall live.
26 Gama kamar yadda Uban yana da rai a cikinsa, haka ya sa Ɗan yă kasance da rai a cikin kansa.
For, as the Father has life in himself, so has he given to the Son, to have life in himself;
27 Ya kuma ba shi iko yă hukunta domin shi Ɗan Mutum ne.
and has given him even the judicial authority, because he is a Son of Man.
28 “Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa
Wonder not at this: for the time comes when all that are in their graves shall hear his voice,
29 su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci.
and shall come forth. They who have done good, shall arise to enjoy life; they who have done evil, shall arise to suffer punishment.
30 Ni kaɗai dai ba na iya yin kome, ina shari’a ne bisa ga abin da na ji. Shari’ata kuwa mai adalci ce. Gama ba na neman gamsar da kaina, sai dai in gamshi shi wanda ya aiko ni.
I can do nothing of myself; as I hear, I judge; and my judgment is just, because I seek not to please myself, but to please him who sent me.
31 “In na ba da shaida a kaina, shaidata ba gaskiya ba ce.
If I alone testify concerning myself, my testimony is not to be regarded:
32 Akwai wani mai ba da shaida mai kyau a kaina, na kuma san cewa shaidarsa game da ni gaskiya ce.
there is another who testifies concerning me; and I know that his testimony of me ought to be regarded.
33 “Kun aika wajen Yohanna ya kuma yi shaida a kan gaskiya.
You, yourselves, sent to John, and he bore testimony of the truth.
34 Ba cewa ina neman shaidar mutum ba ne; sai dai na faɗi haka ne domin ku sami ceto.
As for me, I need no human testimony; I can only urge this for your salvation.
35 Yohanna fitila ne da ya ci ya kuma ba da haske, kun kuwa zaɓa ku ji daɗin haskensa na ɗan lokaci.
He was the blazing and shining lamp; and for awhile, you were glad to enjoy his light.
36 “Ina da shaidar da ta fi ta Yohanna ƙarfi. Gama aikin nan da Uba ya ba ni in kammala, wanda kuwa nake yi, yana ba da shaida cewa Uba ne ya aiko ni.
But I have greater testimony than John's: for the works which the Father has empowered me to perform, the works themselves, which I do, testify for me, that the Father has sent me.
37 Uba da ya aiko ni kuwa kansa ya yi shaida game da ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ko ganin siffarsa ba,
Nay, the Father, who sent me, has himself attested me. Did you never hear his voice, or see his form?
38 maganarsa kuwa ba ta zama a cikinku, gama ba ku gaskata da wanda ya aiko ni ba.
Or, have you forgotten his declaration, that you believe not him whom he has sent forth?
39 Kuna ta nazarin Nassosi da himma don kuna tsammani ta wurinsu ne kuna samun rai madawwami. Nassosin nan ne suke ba da shaida a kaina, (aiōnios g166)
You search the scriptures because you think to obtain by them eternal life. Now these, also, are witnesses for me; (aiōnios g166)
40 duk da haka kun ƙi zuwa wurina domin ku sami rai.
yet you will not come to me, that you may obtain life.
41 “Ni ba na neman yabon mutane,
I desire not honor from men;
42 na fa san ku. Na san cewa ba ku da ƙaunar Allah a cikin zukatanku.
but I know you, that you are strangers to the love of God.
43 Na zo a cikin sunan Ubana, ba ku kuwa karɓe ni ba; amma a ce wani dabam ya zo a cikin sunan kansa, za ku karɓe shi.
I am come in my Father's name, and you did not receive me; if another come, in his own name, you will receive him.
44 Ta yaya za ku gaskata in kuna neman yabon junanku, ba kwa kuwa yin ƙoƙarin neman yabon da yake zuwa daga Allah Makaɗaici?
How can you believe, while you court honor one from another, regardless of the honor which comes from God alone?
45 “Kada fa ku yi tsammani zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi.
Do not think that I am he who will accuse you to the Father. Your accuser is Moses, in whom you confide.
46 Da a ce kun gaskata da Musa, da kun gaskata ni, domin ya rubuta game da ni.
For if you believed Moses, you would believe me: for he wrote concerning me.
47 Amma da yake ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, yaya za ku gaskata maganata?”
But if you believe not his writings, how shall you believe my words?

< Yohanna 5 >