< Yohanna 3 >

1 Akwai wani Bafarisiye mai suna Nikodimus, wani ɗan majalisar Yahudawa.
Now there was a Pharisee called Nicodemus, a ruler of the Jews,
2 Ya zo wurin Yesu da dad dare ya ce, “Rabbi, mun sani kai malami ne daga Allah. Gama ba wanda zai iya yin waɗannan abubuwan banmamaki da kake yi in Allah ba ya tare da shi.”
who came to Jesus by night, and said to him, Rabbi, we know that you are a teacher come from God; for no man can do these miracles which you do, unless God be with him.
3 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”
Jesus answering, said to him, Most assuredly, I say to you, unless a man be born again, he can not discern the Reign of God.
4 Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!”
Nicodemus replied, How can a grown man be born? Can he enter his mother's womb anew, and be born?
5 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu.
Jesus answered, Most assuredly, I say to you, unless a man be born of water and Spirit, he can not enter the kingdom of God.
6 Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu.
That which is born of the flesh is flesh; that which is born of the Spirit is Spirit.
7 Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’
Wonder not, then, that I have said to you, You must be born again.
8 Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu.”
The Spirit breathes where he pleases, and you hear the report of him, but know not whence he comes, or whither he goes; so is every one who is born of the spirit.
9 Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya wannan zai yiwu?”
Nicodemus answered, How can these things be?
10 Yesu ya ce, “Kai ma da kake malami na Isra’ila, ba ka fahimci waɗannan abubuwa ba?
Jesus replied, Are you the teacher of Israel, and know not these things?
11 Gaskiya nake faɗa maka, muna magana a kan abin da muka sani, muka kuma shaida abin da muka gani ne, amma har yanzu kun ƙi ku karɓi shaidarmu.
Most assuredly, I say to you, we speak what we know, and testify what we have seen; yet you receive not our testimony.
12 Na yi muku magana a kan abubuwan duniya amma ba ku gaskata ba; to, yaya za ku gaskata in na yi magana a kan abubuwan sama?
If you understood not, when I told you earthly things, how will you understand when I tell you heavenly things?
13 Ba wanda ya taɓa hawa zuwa sama sai wanda ya sauka daga sama, wato, Ɗan Mutum.
For none has ascended into heaven, but he who descended from heaven; the Son of Man, whose abode is heaven.
14 Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,
As Moses placed on high the serpent in the wilderness, so must the Son of Man be placed on high;
15 don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.” (aiōnios g166)
that whosoever believes on him may not perish, but obtain eternal life: (aiōnios g166)
16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. (aiōnios g166)
for God has so loved the world, as to give his own begotten Son, that whosoever believes on him, may not perish, but obtain eternal life. (aiōnios g166)
17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.
For God has sent his Son into the world, not to condemn the world, but that the world may be saved by him.
18 Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba.
He who believes on him shall not be condemned; he who believes not, is already condemned, because he has not believed on the name of the only begotten Son of God.
19 Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne.
Now this is the ground of condemnation; that light has come into the world, and men have preferred the darkness to the light, because their deeds were evil.
20 Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu.
For whosoever does evil, hates the light, and shuns it, lest his deeds should be detected.
21 Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah.
But he who obeys the truth, comes to the light, that it may be manifest that his actions are agreeable to God.
22 Bayan wannan, Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan Yahudiya, inda ya ɗan jima da su, ya kuma yi baftisma.
After this, Jesus went, with his disciples, into the territory of Judea, where he remained with them, and immersed.
23 To, Yohanna ma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salim, saboda akwai ruwa da yawa a can, mutane kuwa suka yi ta zuwa don a yi musu baftisma.
John also was immersing in Enon, near Salim, because there was much water there; and people came thither, and were immersed.
24 (Wannan kuwa kafin a sa Yohanna a kurkuku.)
For John was not yet cast into prison.
25 Sai gardama ta tashi tsakanin waɗansu almajiran Yohanna da wani mutumin Yahuda a kan zancen al’adar tsarkakewa.
Now John's disciples had a dispute with a Jew, about purification.
26 Sai suka zo wurin Yohanna suka ce masa, “Rabbi, wancan mutumin da yake tare da kai a ƙetaren Urdun, wannan da ka ba da shaida a kansa sosai nan, yana baftisma, kuma kowa yana zuwa wurinsa.”
Then they went to John, and said to him, Rabbi, he who was with you near the Jordan, of whom you gave so great a character; he, too, immerses, and the people flock to him.
27 Ga wannan zancen Yohanna ya amsa ya ce, “Mutum yakan karɓi kawai abin da aka ba shi ne daga sama.
John answered, A man can have no power but what he derives from heaven.
28 Ku kanku za ku shaida cewa na ce, ‘Ba ni ne Kiristi ba, sai dai an aiko ni ne in sha gabansa.’
You yourselves are witness for me, that I said, I am not the Messiah; but am sent before him.
29 Ango ne mai amarya. Abokin da yake masa hidima yakan jira ya kuma saurara masa, yakan kuma cika da farin ciki sa’ad da ya ji muryar ango. Wannan farin cikin kuwa nawa ne, ya kuma cika a yanzu.
The bridegroom is he who has the bride; but the friend of the bridegroom, who assists him, rejoices to hear the bridegroom's voice: this, my joy, therefore, is complete.
30 Dole ne yă yi ta ƙaruwa, ni kuma in yi ta raguwa.
He must increase, while I decrease.
31 “Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa; wannan da ya zo daga ƙasa na ƙasa ne, yana kuma magana kamar wanda ya zo daga ƙasa ne. Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa.
He who comes from above, is above all. He who is from the earth is earthly, and speaks as being from the earth. He who comes from heaven, is above all.
32 Yana ba da shaidar abin da ya gani da kuma ya ji, duk da haka ba wanda ya yarda da shaidarsa.
What he testifies, is what he has seen and heard; yet his testimony is not received.
33 Mutumin da ya yarda da ita ya tabbatar da cewa Allah mai gaskiya ne.
He who receives his testimony, vouches the veracity of God.
34 Gama wannan da Allah ya aiko yakan faɗi kalmomin Allah ne, gama Allah yana ba da Ruhu babu iyaka.
for he whom God has commissioned, relates God's own words; for to him God gives not the Spirit by measure.
35 Uban yana ƙaunar Ɗan ya kuma danƙa kome a hannuwansa.
The Father loves the Son, and has subjected all things to him.
36 Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa.” (aiōnios g166)
He who believes on the Son, has life eternal; he who rejects the Son, shall not see life: but the vengeance of God awaits him. (aiōnios g166)

< Yohanna 3 >