< Yohanna 21 >

1 Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya. Ga yadda ya faru.
在这之后,耶稣在提比里亚海边再次向门徒显现。他显现的经过是这样的:
2 Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili,’ya’yan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare.
当时彼得、“双生子”多马、加利利的迦拿人拿但业、西庇太的两个儿子,和另外两个门徒聚在一起。
3 Sai Siman Bitrus ya ce musu, “Za ni kamun kifi,” suka ce, “Za mu tafi tare da kai.” Saboda haka suka fita suka shiga jirgin ruwa, amma a daren nan ba su kama kome ba.
彼得对他们说:“我要打鱼去。”他们说:“我们也跟你一起去。”于是他们出去上了船,可是那一夜他们并没有打到什么。
4 Da sassafe, sai ga Yesu tsaye a gaci, amma almajiran ba su gane cewa Yesu ne ba.
黎明时分,耶稣站在岸边,门徒却不知道他就是耶稣。
5 Sai ya ce musu, “Abokai, kuna da kifi kuwa?” Suka amsa suka ce, “A’a.”
耶稣对他们说:“我的朋友们,打到鱼没有?”他们回答:“没有。”
6 Ya ce musu, “Ku jefa abin kamun kifinku dama da jirgin ruwan, za ku samu.” Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo abin kamun kifin saboda yawan kifi.
耶稣说:“把网撒在船的右侧就可以打到鱼。”于是他们把网撒下去,但却拉不动,因为鱼太多。
7 Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan.
耶稣所爱的那名门徒对彼得说:“是主!”彼得一听见是主,就立刻穿上衣服(因为他当时没有穿衣服),纵身跳进海里。
8 Sauran almajiran kuwa suka bi shi cikin jirgin ruwan, janye da abin kamun kifin cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, wajen yadi ɗari ne.
其他的门徒因为离岸不远(约有一百公尺),于是就跟着来到小船上,把那网鱼拖过来。
9 Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma’yan burodi.
他们上了岸,就看见那里有一堆篝火,上面正在烹饪鱼,还有一些饼。
10 Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.”
耶稣对他们说:“把你们刚才打的鱼拿几条来。”
11 Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo abin kamun kifin gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan abin kamun kifin bai tsintsinke ba.
彼得上船把网拉到岸上,那网装满了大鱼,共有一百五十三条。鱼虽然这么多,网却没有破。
12 Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Ba wani daga cikin almajiran da ya yi karambanin tambayarsa, “Wane ne kai?” Sun san cewa Ubangiji ne.
耶稣对他们说:“来吃早饭吧。”门徒中没有一个人敢问他:“你是谁?”因为知道他是主。
13 Yesu ya zo, ya ɗauki burodin ya ba su, haka kuma kifin.
耶稣走过来,把饼递给他们,又把鱼递给他们。
14 Wannan fa shi ne sau na uku da Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa bayan an tashe shi daga matattu.
这是耶稣死而复生后,第三次向门徒显现。
15 Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?” Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Ciyar da’ya’yan tumakina.”
他们吃了早饭,耶稣问西门(彼得):“约翰的儿子西门,你爱我比这些更深吗?” 他回答说:“是的,主啊,你知道我爱你。”
16 Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?” Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Lura da tumakina.”
耶稣对他说:“照顾好我的羊羔。”耶稣第二次又问他:“约翰的儿子西门,你爱我吗?”他回答:“主啊,是的,你知道我爱你。”
17 Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?” Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.” Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina.
耶稣说:“照顾好我的绵羊。”耶稣第三次问他:“约翰的儿子西门,你爱我吗?”彼得因为耶稣第三次问他“你爱我吗?”就有些难过。于是对耶稣说:“主啊,你是无所不知的,你知道我爱你。”耶稣说:“照顾好我的绵羊。
18 Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.”
告诉你实话,当你年轻的时候,你会打扮好去任何地方,但当你变老,就要伸出手来,让别人给你穿上衣服,带你到你不愿意去的地方。”
19 Yesu ya faɗi wannan ne, don yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yă ɗaukaka Allah. Sa’an nan ya ce masa, “Bi ni!”
耶稣说这话,是在解释他死亡的方式如何让上帝获得荣耀。然后他对彼得说:“跟我来吧。”
20 Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu sa’ad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”)
彼得转过身来,看见耶稣所爱的那名门徒跟着他们,他在最后的晚餐时曾侧身问耶稣:“主啊,出卖你的是谁?。”
21 Da Bitrus ya gan shi sai ya ce, “Ubangiji, wannan fa?”
彼得看见他,就问耶稣:“主啊,他会怎么样呢?”
22 Yesu ya amsa ya ce, “Idan na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai bi ni.”
耶稣回答他:“如果我让他活到我到来之时,跟你有什么关系呢?你只管跟从我吧!”
23 Saboda wannan, jita-jita ta bazu a cikin’yan’uwa cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma fa Yesu bai ce ba zai mutu ba; shi dai ya ce, “In na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki?”
这句话传到其他门徒那里,说那位门徒不会死。其实耶稣并没有对他说他不会死,只是说:“如果我让他活到我到来之时,跟你有什么关系呢?”
24 Wannan shi ne almajirin da ya ba da shaida a kan waɗannan abubuwa ya kuma rubuta su. Mun san cewa shaidarsa gaskiya ce.
这位门徒确认发生过这件事,并且将其写了下来。我们知道他的见证是真实的。
25 Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za tă sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.
耶稣还做过许多其他的事情,如果全部写下来,我怀疑整个世界能否容纳所有要写的书。

< Yohanna 21 >