< Yohanna 20 >

1 Da sassafe a ranar farko ta mako, tun da sauran duhu, Maryamu Magdalin ta tafi kabarin ta kuwa tarar an kawar da dutsen daga bakin kabarin.
And early on the first day of the week, while it was yet dark, Mary Magdalene came to the tomb, and saw that the stone had been taken away from the tomb.
2 Sai ta zo da gudu wajen Siman Bitrus da ɗayan almajirin, wanda Yesu yake ƙauna, ta ce, “Sun ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuma san inda suka sa shi ba!”
Then she ran and came to Simon Peter, and to the other disciple whom Jesus loved, and said to them: They have taken away the Lord out of the tomb, and we know not where they have laid him.
3 Sai Bitrus da almajirin nan suka nufi kabarin.
Then Peter and the other disciple went out, and came to the tomb.
4 Dukansu biyu suna gudu, amma ɗayan almajirin ya tsere wa Bitrus ya kuma fara kai kabarin.
And the two ran together; and the other disciple outran Peter, and came first to the tomb;
5 Ya sunkuya ya duba ciki ya ga ƙyallayen lilin ne kwance a can amma bai shiga ba.
and he stooped down and saw the linen cloths lying, but he did not go in.
6 Sa’an nan Siman Bitrus, wanda yake bayansa, ya iso ya kuwa wuce cikin kabarin. Ya ga ƙyallayen lilin kwance a can,
Then came Simon Peter, following him; and he went into the tomb, and saw the linen cloths lying,
7 haka ma zanen binnewar da aka naɗe kan Yesu da shi. Zanen a naɗe yake shi kaɗai, a keɓe da lilin ɗin.
and the handkerchief that had been on his head, not lying with the linen cloths, but folded in a place by itself.
8 A ƙarshe sai almajirin nan, wanda ya kai kabarin da farko, shi ma ya shiga. Ya gani ya kuma gaskata.
Then, therefore, the other disciple, who came first to the tomb, went in, and saw, and believed.
9 (Har yanzu ba su fahimci Nassin nan da ya ce lalle ne Yesu yă tashi daga matattu ba.)
For, as yet, they did not know the scripture, that he must rise from the dead.
10 Sai almajiran suka koma zuwa inda suke zama.
Then the disciples went away again by themselves.
11 Maryamu kuwa ta tsaya a bakin kabarin daga waje tana kuka. Da tana cikin kuka, sai ta sunkuya ta leƙa cikin kabarin,
But Mary stood without near the tomb, weeping; and as she wept, she stooped down and looked into the tomb,
12 sai ta ga waɗansu mala’iku biyu saye da fararen tufafi, zaune a inda dā gawar Yesu take, ɗaya wajen kai ɗayan kuma wajen ƙafafu.
and saw two angels in white raiment, sitting, the one at the head, and the other at the foot, where the body of Jesus had lain.
13 Suka tambaye ta cewa, “Mace, don me kike kuka?” Ta ce, “Sun ɗauke Ubangijina, ban kuma san inda suka ajiye shi ba.”
And they said to her: Woman, why do you weep? She said to them: They have taken away my Lord, and I know not where they have laid him.
14 Da ta faɗin haka, sai ta juya ta ga Yesu tsaye, sai dai ba tă gane cewa Yesu ne ba.
Having said this, she turned back, and saw Jesus standing, and knew not that it was Jesus.
15 Sai ya ce, “Mace, don me kike kuka? Wa kike nema?” Ta yi tsammani shi ne mai aikin lambun, sai ta ce, “Ranka yă daɗe, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka ajiye shi, in je in ɗauke shi.”
Jesus said to her: Woman, why do you weep? Whom do you seek? Supposing that it was the gardener, she said to him: Sir, if you have taken him hence, tell me where you have laid him, and I will take him away.
16 Yesu ya ce mata, “Maryamu.” Sai ta juya wajensa ta ɗaga murya ta ce da Arameyanci, “Rabboni!” (Wanda yake nufin “Malam”).
Jesus said to her: Mary. She turned, and said to him: Rabboni; which is, translated, Teacher.
17 Yesu ya ce, “Kada ki riƙe ni, gama ban riga na koma wajen Uba tukuna ba. A maimako, ki tafi wajen’yan’uwana ki gaya musu, ‘Ina komawa wajen Ubana da Ubanku, wajen Allahna da kuma Allahnku.’”
Jesus said to her: Touch me not, for I have not yet ascended to my Father: but go to my brethren, and say to them, I ascend to my Father and your Father, and to my God and your God.
18 Sai Maryamu Magdalin ta wajen almajiran da labari cewa, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma gaya musu cewa ya faɗa mata waɗannan abubuwa.
Mary Magdalen came and told the disciples that she had seen the Lord, and that he had said these things to her.
19 Da Yamman ranar farko ta mako, sa’ad da almajiran suna tare, ƙofofi kuma suna a kulle saboda tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!”
Then, on that day, the first day of the week, when it was evening, and the doors of the house in which the disciples were assembled had been closed for fear of the Jews, Jesus came and stood in the midst, and said to them: Peace be to you.
20 Bayan ya faɗa haka, sai ya nuna musu hannuwansa da gefensa. Sai almajiran suka yi farin ciki ƙwarai da suka ga Ubangiji.
And having said this, he showed them his hands and his side. Then the disciples rejoiced, when they saw the Lord.
21 Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama tă kasance tare da ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma ina aikan ku.”
Then Jesus said to them again: Peace be to you. As my Father has sent me, so I send you.
22 Da wannan sai ya hura musu numfashinsa ya ce, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki.
And when he had said this, he breathed on them, and said to them: Receive the Holy Spirit.
23 Duk wanda kuka gafarta wa zunubansa, an gafarta masa ke nan. Duk wanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta masa ba ke nan.”
Whosever sins you forgive, they are forgiven them: whosever sins you retain, they are retained.
24 Toma kuwa (wanda ake kira Didaimus), ɗaya daga cikin Sha Biyun, ba ya tare da almajiran sa’ad da Yesu ya zo.
But Thomas, one of the twelve, who is called Didymus, was not with them when Jesus came.
25 Saboda haka sauran almajiran suka ce masa, “Ai, mun ga Ubangiji!” Amma ya ce musu, “Ina, ai, sai na ga ramin ƙusa a hannuwansa na sa yatsata a inda ƙusoshi suka kasance, na kuma sa hannuna a gefensa, in ba haka ba, ba zan gaskata ba.”
Then the other disciples said to him: We have seen the Lord. But he said to them: Unless I see in his hands the print of the nails, and put my finger in the print of the nails, and put my hand into his side, I will not believe.
26 Bayan mako guda, har wa yau almajiransa suna cikin gidan, Toma kuwa yana tare da su. Ko da yake ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!”
And after eight days, again his disciples were within, and Thomas was with them. Then Jesus came, though the doors had been closed, and stood in the midst, and said: Peace be to you.
27 Sa’an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsarka nan; dubi hannuwana. Miƙa hannunka ka sa a gefena. Ka daina shakka ka gaskata.”
Then he said to Thomas: Reach hither your finger, and behold my hands; and reach hither your hand, and put it into my side; and be not faithless, but believing.
28 Toma ya ce masa, “Ya Ubangijina da Allahna!”
And Thomas answered and said to him: My Lord and my God.
29 Sai Yesu ya ce masa, “Wato ka gaskata saboda ka gan ni ne, masu albarka ne waɗanda ba su gan ni ba, amma suka gaskata.”
Jesus said to him: Because you have seen me you have believed: blessed are they who, though they have not seen, yet have believed.
30 Yesu ya yi waɗansu abubuwan banmamaki da yawa a gaban almajiransa da ba a rubuta a wannan littafi ba.
Many other signs truly did Jesus in the presence of his disciples, which are not written in this book;
31 An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.
but these are written, that you may believe that Jesus is the Christ, the Son of God, and that by believing you may have life through his name.

< Yohanna 20 >